Matsayin Mata A Musulunci

- Advertisement -

Matsayin Mata A Musulunci

Daga Khadijah Ahmad,

Bismihi Ta’ala:

Allah ya halicci halittunSa a doron kasa a jinsi biyu ne wato ‘namiji da mace’. Wannan ka’ida ce da Allah ya so ya wanzar da halittu ta hanyarta, kuma wannan ka’idar ba ta canza ba a halittar dan Adam. An halicci mace ne daga abinda aka halicci namiji,kuma daidai suke a halitta,babu fifiko a tsakanin su sai na tsoron Allah.

Kafin zuwan musulunci, mata solar tsinci kansu a mawuyacin hali. A wasu al’ummun an musguna musu ne an tauye musu hakkokinsu an maidasu wani abu dake tsakanin mutum da dabba, wato su mata ba a daukesu mutane ba. Hakan yasa suka fuskanci nau’uka na zalunci da tauye hakkoki kamar killacesu a gida tamkar fursunoni, maidasu ababen mallakar mazawandaharta kaiga ana gadonsu, wadannan abububuwan a bayyane suke a al’ummu kamar tsohuwar daular Indiya,Jahilyyar larabawa da sauransu.Wani nau’in zalunci kuma da mata suka fuskanta shine an maishesu hoto da ake amfanidasudon cimma wata manufa, anan ana basu wasu mukamai na zahiri misali sarauniya ta wani gari a zahiri,amma a badini ba itace ba wasu ne ke amfana da kasantuwarta sarauniyar. Wannan amfanuwar da ake da mata ta kaima har aka maida su ababen bauta,kamar yadda ya faru a Misra da Indiya.

Musulunci da ya zo sai ya baiwa mata matsayinsu na mutum daidai da namiji wato ya daidaitasu a dan Adamtaka ba tare da nuna fifiko ba. Sannan ya kwato musu hakkokinsu da aka tauye masu ya kuma toshe hanyar da wasu zasu yi amfani da su don cimma manufofinsu ta hanyar ɗaga darajarsu da kuma takaita mu’amalolinsu ta hanyar sanya musu hijabi, wanda shi wannan hijabin Katanga ne daga munannan abubuwa ga mata ta kowane janibi na rayuwarsu. Sannan musulunci ya baiwa mata hakkoki daidai da namijikamar; hakkin neman ilimi zuwa makurar da zasu iya, hakkin mallaka da kuma sarrafa abinda suka mallaka bisa ka’ida’ hakkin gado( su gada kuma a gajesu), hakkin zaɓi da sauran hakkoki.

Musulunci baitsaya nan ba, saida yayi duba zuwa ga yanayin halittar mata sannan ya basu aiki daidai da halittarsu, saboda tsantsar adalci irin na addinin musulunci baice tunda ya daidaita mace da namiji a Dan Adamtaka,to dole ya zama aikinsu iri daya da na maza ba, ya duba bambanci na halitta na jiki da halaye dake tsakanin mace da namiji sai ya basu ayyuka mabambanta kamar yadda Allah ya fadi a littafin Shi Mai tsarki ‘Wa ma khalakaz zakara wal unsa , Inna sa’ayakum la shatta’. Mafi muhimmancin ayyukan mata a cikin gida suke, inda suke taka rawa a matsayinsu na ‘Ya ya, Matan aure da kuma Uwa.

A dukkan wadannan rawar da suke takawa, musulunci ya dora musu wani nauyi da zasu sauke wanda sauke wannan nauyin shine mafi muhimmancin aikin mata sai kuma wani aikin da ke bi mishi na al’umma; mata suna da damar su shiga cikin al’umma su bada gudummawa wurin ci gabantar da al’umma ta hanyar koyarwa,kula da lafiya da sauransu.

Musulunci ya daukaka darajar mata ta hanyar damka musu amanar dan Adamtaka, daga mata ne kowane mutum ke samuwa, sune makarantar farko ga kowane dan Adam. Sune asasi na ci gaba da cibayan kowace al’umma. Sakamakon wannan babban nauyi da aka dora musu ne yasa aka karfafa kyautatamusu,indaa wurare mabambanta Manzon Allah (S) da sauran A’imma (AS) sukai nuni ga kyautatama mata tsawon rayuwarsu,kumaaka kwadaitar dasu matan irin falalar dake tattare da nauyin nasu misali Inda Manzon Allah (S) Yake cewa “ Jahadin mace shine kyakkyawan zamantakewarta da mijinta” da sauran wuraren da aka nuna dimbin ladar dake tattare da zama uwa.

Sannan musulunci bai bar mata haka nan ba saida ya samar musu da ababen kwaikwayo, matayen da sukai rayuwa a lokuta mabmbanta suka cimma kamala suka zarce mazaje. Allah ya bamu misali na Mata muminai a cikin Suratul Tahrim aya ta sha daya zuwa sha biyu inda aka ambaci Matar Fir’auna da Maryam mahaifiyar Annabi Isa (AS) a matsayin misali na muminai bayan kawo matar Annabi Nuh da Annabi Lud (AS) a matsayin misali na wadanda suka butulce. Mata solar taka rawa a musulunci tsawon tarihi inda suke taka rawarsu harma su kara da na maza misali irinsu Sayyida Khadijah(AS) wacce ta kasance bangon jingina ga Manzon Allah (S) saboda gudummawar da ta bayar ma addini ya kaiga Manzon Allah (S) Yace “ Addini ya kafu ne da dukiyar Khadijah da takobin Ali.” Da sauran mata da suka taka muhimman rawa wurin ci gabantar da addini tun daga daga farko har zuwa yau.

A karshe zan kare da kira ga iyaye dasu kula da ilimi da tarbiyya na ‘ya ‘yansu mata su tabbatar da cewa basu fi muhimmatar da ilimin ‘ya ‘yansu maza akan mata ba sannan su yi kokari wurin ganin solar kyautata rayuwarsu ta hanyar sama musu dukkan ababen da suke bukata na rayuwa daidai da karfinsu. Sannan mu kuma Mata muyi amfani da wannan dama da gata da addininmu ya bamu wurin neman kusanci da Allah tare da zama sanyin ido ga Iyayenmu ko yaushe ya zama hankoranmu shine cigabantar da al’ummarmu ta kowane janibi da muke da iko tare da kula da kasantuwarmu ginshikin al’umma don haka dole mu zamo na gari don samar da al’umma ta gari, tare datakatsantsan domin kuwa makiyanmu makiya addininmu tuni solar gano cewa mune tushen cigaba da cibaya don haka suka karkato da makaman yakinsu don farmakarmu ta hanyar maishe mu gurbatattu wanda hakan zai samar da al’umma gurbatacciya

Allah ya tsaremu da tsarewarsa ya sanya mu daga cikin Mata masu biyayya gare Shi wadanda Manzon Allah da Sayyida Zahra zasu yi alfari dasu, wadanda kuma zasu zama mataimaka ga Sahibul Asr Wazzaman(AJF) ta hanyar tarbiyyantar da al’umma su zama na gari.

- Advertisement -