Matsalolin Arewa Su Ka Sa Na Fara Rubutu – Meena Abba

0
139

Assalamu Alaikum. Barkan mu da sake kasancewa da ku a filin ku na FASIHAI. Shafi  da ke zakulo muku shahararrun marubuta da mawakan hausa, tare da wakiliyar MOBILIZED9JA A YAU ,SADIYA SIDI SAID, wacce aka fi sani da SIDIYA.

Bakuwar mu ta mako itace AMINA ABBA UMAR wacce kuka fi sani da MEENA ABBA a duniyar marubuta. MEENA ABBA daya ce daga cikin fitattun marubutan mu na yanar gizo. Itace wacce ta nishadantar da Ku a cikin littafin Ku mai farin jini wato Afrah. Ga yadda tattaunawar ta kasance.

Meena Abba, masu karatu za su jin dan takaitaccen tarihinki?

Da farko dai sunana Amina Abba Umar wacce ku ka fi sani da Meena Abba. Ni haifaffiyar Jahar Katsina ce, a karamar hukumar dutsanma. Na yi firamare na a dutsanma, na yi sakandire a sandamu.  Daga nan na wuce karatuna na gaba a nicely being ‘know-how kankia’ , a bangaren ‘neighborhood nicely being edtension workers(chew)’. Bayan na kammala na yi aure a garin dutsanma. Inada yarinya daya. Wannan shine takaitaccen tarihina.

Ta ya aka yi ki ka tsinci kanki a harkar rubutu?

Lura da wasu matsaloli da muke fama dasu a arewacin najeriya, wannan shi ya jawo hankalina na fara rubutu, saboda a koda yaushe nakan zauna na yi tunanin ta inane yakamata in bada gudummuwa ta wurin gyara matsalolin da muke fama dasu, ganin yadda mutane su ka raja’okay wurin karatun littafin hausa, hakan ne ya bani damar fara rubutu, domin nasan sakona zai isa duk inda bana tunani, kuma ta hanyar rubutun da zanyi nasan insha Allahu za’a fadakar da mutane ta hanyar nishadantarwa, amma zasu gyara matsalolin da muke fama dasu. Wannan shine dalilin daya ja hankalina na fara rubutu.

A dunkule mai ki ka fahimta recreation da rubutun Hausa?

Rubutun hausa wata hanya ce da zaka iya isar da duk wani sakon da ka ke son isarma al’umma. Sannan hanyace ta fadakarwa, nishadantarwa, da kuma wa’azanatarwa cikin sauki.

Tsawon wani lokaci ki ka dauka kina rubutu a yanar gizo, sannan daga fara rubutun ki zuwa yanzu littafi nawa ki ka rubutu?

Matsalolin Arewa Su Ka Sa Na Fara Rubutu – Meena Abba

Ban wani dauki lokaci da farawa ba. Na fara rubutu ne a shekara ta dubu biyu da goma takwas. Littafai biyu na rubuta, saboda kafin in fara rubutu sai na yi dogon nazari da bincike ta yadda sakon da nakeson isarwa ya tafi yadda yakamata da kuma yadda wanda nake yi dansu za su fahimci inda na dosa.  Hakan yasa bana yawan yin rubutu.

Ko za ki iya gayawa masu karatu sunan littafanki?

Afrah, da kuma 2. Reshe ya juye da mujiya.

Wanne ne bakandamiyarki a ciki?

Gaskiya kowanne ina son shi, sai dai wanda aka fi sani na da shi shine littafin Afrah.

Da wani salo ki ka yi amfani wurin rubuta littafin Afrah, sannan a dunkule wani sako littafin ke dauke da shi?

Na yi amfani da salon da zai jawo hankalin mutane, wanda idan suka fara karanta littafin ba za su so su daina karanta shi ba har sai photo voltaic ga karshenshi. Salon kamar, nishadi, soyayya, barkwanci, tausayi, da dai sauransu, ta hakane na yi amfani da wannan damar na saka wasu matsaloli da suke damun al’umma dan isar da sakon cikin aminci. Littafin Afrah yana dauke da sakonni da dama a ciki, kadan daga cikinsu akwai; yadda da kaddara, yadda da zabin Allah, kaucewa daga aikin zina, da kuma dana sani, karfafa zumunci da dai sauran su.

Bidiyo: Maza A Dajin Sambisa – Yamu Baba X Zainab Sambisa Karya Ta Kare (Official Video 2020)

Ko akwai wani kalubale da ki ka fuskanta yayin rubuta littafin Afrah?

Kalubalen dana samu gaskiya bai wuce na mutane da suke kira na, kowa yana fadan irin yadda yake son littafin ya tafi, ko ya kasance, bayan ni kuma na riga na tsara labarina tun kafin na fara rubutun shi, dan saboda wannan dalilin ne har sai da na tsaida rubutun da niyyar bazan karasa ba, saboda nace kowacce ta karasa shi ta yadda take so. Daga karshe kuma aka rika kira na ana bani hakuri  daga nan ne na cigaba. Wannan shine kawai kalubalen dana samu.

Ta fannin kalubalen rubutu mai yafi ci miki tuwo a okay’warya, sannan masu karatu za su so jin irin nasarorin da ki ka samu a harkar rubutu?

Abunda yafi ciman tuwo a kwarya shine, ta yadda masu karatu ba za su rika tsayawa su na jiran mai rubutu ya rubuta abunda yayi niyyar rubutawa ba, saboda a duk lokacin daka dauko rubutunka, akwai inda ka ke son ka direshi, amma masu karatu sai su nemi sai photo voltaic sauya maka tsari harka ji wasu su na cewa idan ba ayi yadda suke so ba zasu daina karatun. Alhamdulillah na samu nasarori da dama, amma babbar nasarar da na ji dadinta itace sakona yakai inda nake son yakai kuma yayi ma wasu amfani, dan na samu kira daga wata baiwar Allah da har yanzu muke zumunci. Cikin rubutun nawa tace min abun ya faru da ita, dan akwai wasu abubuwan a cikin littafin take ganin kamar da ita nake, kuma a cikin littafin ta samu mafita, da shawarwarin da tayi amfani da su. Wannan itace babbar nasarar dana samu kuma nake alfahari da ita kasancewar dama na fara rubutun ne dan magance wasu matsalolin dake damun mu.

Wa ni ko wata ne ya baki shawarar fara rubutu a yanar gizo ko kuwa kin fara ne dan ra’ayin kanki?

A gaskiya babu wanda ya taba bani shawarar nazo nayi rubutu, saboda shi rubutu ba abu bane da wani zai zo yace ka fara rubutu, dan kila ba lallai ka iyayi ba saboda abune wanda yake bukatar nazari, bincike, da kuma sha’awar yin sa, dan haka ra’ayina ne nason fadakarwa, da aikawa da sako. shine abunda yasa ni fara rubutu.

Kin taba wallafa littafi?

A’a ban taba ba, amma littafin afrah mutane da dama photo voltaic bani shawara akan na wallafashi, sai dai hakan bai samu ba sai nan gaba insha Allahu.

Me Meena Abba ta fi so ta bangaren abinci da abun sha, da kuma nau’in sutura?

Ina son doya duk yadda aka sarrafata, ina son ta kamar sakwara, faten doya, da soyayyiya. A bangaren abun sha ina son kunun aya. Sutura kuma ina son atamfa.

Kasancewar an samu ci gaba a duniyar rubutu na wanzuwar kungiyoyi masu zaman kan su, shin ko akwai wata kungiyar da ki ke ciki? Idan akwai masu karatu za su jin manufar wannan kangiya a takaice?

Tabbas ina cikin kungiya mai suna ‘intelligent writers affiliation’. Wannan kungiya an bude ta ne dan hadin kan masu rubutu na yanar gizo. Manufar bude wannan kungiya shine, za’a rika tace littafan wannan marubuta na cikinta, ta hakane za’a rage yaduwar littafan batsa da wasu daga cikin marubuta suke yi, dan duk wanda aka kama da irin wannan rubutu mai bata tarbiyar yaranmu, ko kannenmu, to tabbas kungiya zata hukunta shi. Sannan akwai gyare-gyare na rubutu da ake yi ma marubutan, sannan akwai shawarwari da ake bayarwa na ganin rubutun kowa yana tafiya akan tsari, tare da tura littafi dan ganin sakon ya isa inda ake so. Wannan shine kadan daga cikin manufofin kungiyar.

Wani shawara za ki baiwa masu karatu har ma da marubuta ‘yan uwanki?

Shawarata ga masu karatu shine, su daure su rika nutsuwa su na yin karatun yadda yakamata, kuma su saka fahimta su ga shin wai wannan littafi me yake dauke da shi, bawai su rika daukar abunda bazai amfanar dasu ba, kamar kyawun ‘yan littafi da ake sakawa, wata ta koma daga gefe tace ita dole sai mai irin kyan mijin nobel zata aura duk takori samarinta, wannan ba daidai bane, muna saka musu wannan siffofinne dan su ji dadin karanta labarin, amma ba wai dan shine darasin dake cikin shi ba. Ina kara bama masu karatu shawarar su dubi girman Allah su daina karanta littafin batsa saboda muddin su ka daina karantawa, suka daina sharhi to su ma masu rubutarwa za su daina, kasancewar da bazar masu karatun muke taka rawa. Su kuma masu rubutu shawarata a gare su dan Allah su rika sanin abunda suke rubutawa kada mun fito da niyyar gyara tarbiya mu rika lalatatawa, ka yi rubutu wanda ko a gaban iyayenka ba za kayi shakkar a karantashi ba.

Wacece tauraruwar ki cikin marubutan yanar gizo da kuma mawallafa?

Duka yan kungiyar ‘intelligent writers’ sune taurarina. Ina matukar alfahari da su. A masu wallafa littafi kuma babu.

Ko ki na da albishir din da za ki yi wa masoyanki?

Albishir din da zan yi ma masoyana shi ne Ina cikin koshin lafiya da kwanciyar hankali, saboda ina ganin korafin su na rashin ji na da ba su yi da sauri, sannan ina masu albishir din littafina da zai zo masu mai suna ‘Ramin Mugunta’, duk da ba ni kadaice mai rubuta shi ba.

Mene ne burin ki nan gaba recreation da rubutunki?

Burina shi ne in fara wallafa littattafaina dan sakon da na ke son isarwa ya kai har wurin wanda ba su da wayar hannu dan su ma su amfana da abinda na ke rubutawa.

Meena Abba, MOBILIZED9JA A YAU na yi mi ki fatar alkhairi.

Godiya na ke yi marar adadi. Allah ya kara daukaka.

What's On Your Mind?