Matsalar Tsaro: Za A Ci Gaba Da Addu’o’i A Masarautun Jihar Neja Takwas

- Advertisement -

Matsalar Tsaro: Za A Ci Gaba Da Addu’o’i A Masarautun Jihar Neja Takwas

Daga Muhammad Awwal Umar, Minna

An tabbatar da cewar a wannan satin za a cigaba da yin addu’o’in musamman a dukkanin masarautu takwas na jihar Neja dan neman Allah ya kawo karshen matsalar tsaron da jihar ke fuskanta, ko a satin da ya gabata malaman addini, manyan jami’an gwamnati, gwamna Abubakar Sani Bello da mataimakinsa, sarakunan gargajiya na daga cikin wadanda suka jagoranci fara addu’o’in a babban masallacin juma’ar Minna.

Addu’ar ta musamman wanda babban limamin masallacin juma’ar Minna, Mallam Ibrahim Isah Fari ya jagoranta an yi saukar Al-kur’ani mai tsalki da nufin Allah ya kawo wa jihar Neja da kasar karshen matsalar tsaron da ta ke fuskanta.

Da yake zantawa da manema labaru bayan kammala addu’o’in, gwamna Abubakar Sani Bello yace akwai bukatar a fuskanci Allah da magiya da roko a jiha da tarayya duk da cewar ba zasu bar kowace irin kafa da za ta kasa samar da zaman lafiya, dan haka idan muka yi kokarin mu kuma muka roki Allah za mu ga karshen matsalar rashin tsaro a jihar nan cikin gaggawa.

Gwamnan yace mun fara ganin alamun cigaban da aka samu na daidaituwar lamurra a wasu yankunan, inda ya kara da cewar addu’o’in zasu cigaba koda bayan azumin Ramadan ne.

” Muna karfafa guiwar kowa, duk wani ruwa da tsaki, kowa ya goyi bayan gwamnatin jiha da ta tarayya da addu’o’i, ina da yakinin cewar komai zai kawo karshe da yardar Allah”.

Babban daraktan kula da harkokin addinai kuma sakataren kungiyar Limamai, Mallam Umar Farouk Abdallah, yace matsalar tsaro a jihar nan yana bukatar komawa ga Allah dan samun mafita, gaba dayan mu ya kamata mu hadu dan samun rahamar Allah.

Ya jaddada cewar akwai bukatar al’ummar jihar da su kiyaye ayyukansu daidai da koyarwar addini, ya nemi ‘yan ta’adda da su tuba da miyagun ayyukan da suke yi, su ajiye makamansu, kuma su dawo ga Allah, inda ya kara da cewar ayyukansu baya kan karantarwar addinin musulunci.

- Advertisement -