Matsalar Tsaro: Muna Neman Taimakon Kasashen Waje – Buhari

0
186

Matsalar Tsaro: Muna Neman Taimakon Kasashen Waje – Buhari

Muhammadu Buhari ya roki kasashen duniya da su tallafa wa Nijeriya wajen magance matsalolin tsaro da ke ci gaba da ta’azzara a kasar don dakile barnar da ake yi.

Shugaba Buhari ya yi wannan rokon ne a wata ganawa ta sirri da Sakataren Harkokin Waje na kasar Amurka, Mista Anthony Blinken.

Shugaban ya bukaci Amurka da ta sake yin la’akari da kafa hedikwatar AFRICOM daga Stuttgart, Jamus, zuwa Afirka, mafi kusa da wuraren yaki a Nijeriya.

Shugaba Buhari ya ce, AFRICOM, wacce ke kawance da kasashe don magance barazanar da ke tsakanin kasashen duniya, kamata ya yi a maida su Afirka don karfafa kokarin da ake yi na duba yanayin tsaro, da yiwuwar hakan ya shafi wasu kasashen.

“Matsalolin tsaro a Nijeriya solar kasance masu matukar damun mu,  kuma suna da tasiri sosai ta yadda ake fuskantar matsin lamba mara kyau a yankin Sahel, Afirka ta Tsakiya da Yammacin Afirka, da kuma Yankin Tafkin Chadi. Idan aka daidaita lamarin na yanzu, Nijeriya da jami’an na tsaronta za su ci gaba da jajircewa wajen ganin an dakile matsalolin da kuma magance musabbabinsu,” in ji Buhari.

Ya ci gaba da cewa, “ba za a iya wuce gona da iri ba wajen tallafa wa muhimman abokan hulda kamar Amurka saboda sakamakon rashin tsaro zai shafi dukkan kasashe,  saboda haka ya zama tilas a samu hadin kai da hadin gwiwar dukkan kasashe don shawo kan wadannan matsalolin.”

“Dangane da wannan kuma, ya kamata a yi la’akari da yadda ake samun kalubalen tsaro a Yammaci da Afirka ta tsakiya, Tekun Gini, yankin Tafkin Chadi da Sahel, wanda ya nauyaya Afirka, ya nuna bukatar Amurka ta sake yin la’akari da sake kafa hedikwatar AFRICOM daga Stuttgart, Jamus zuwa Afirka da kuma kusa da wuraren yaki,” in ji shi a cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Femi Adesina ya fitar.

Shugaban ya ce, Nijeriya za ta inganta hadin gwiwa ta kowane fanni, tare da abokai da manyan abokan hulda, don yin aiki tare don inganta tsaro ga kowa, wanda ya kasance mafi muhimmancin yanayin shawo kan matsalolin da ake fuskanta.

Bugu da kari, Shugaba Buhari ya taya Blinken murnar nadin da Shugaba Joe Biden ya yi masa, ya kuma yaba wa Amurka kan shawarar da ta yanke na dakatar da dokar hana shigo da bakin haure da aka fi sani da ‘Muslim ban’, sake komawa cikin hukumar lafiya ta duniya (WHO) da yarjejeniyar Paris kan Canjin Yanayi.

“Nijeriya ta ba da muhimmanci ga alakarta da Amurka,” in ji Shugaba Buhari.

Ya kara da cewa, “Bari in bayyana wannan dangane da nuna godiya ga Shugaba Joe Biden recreation da marabarsa da kuma yanke shawarar soke takunkumin bakin haure da aka sani da ‘Muslim ban’ kan tafiye-tafiye da biza ga ‘yan kasar, wanda galibinsu daga kasashen Musulmi da kasashen Afirka suke, ciki har da Nijeriya.”

Shugaba Buhari ya bayyana cewa, Nijeriya na nan daram a kan kudurinta na tallafawa kokarin duniya kamar yadda yake a yarjejeniyar Paris kan Canjin Yanayi, wacce ke neman takaita dumamar yanayi da rage gurbataccen hayaki.

Sakataren na Amurka, wanda ya ce ya yi farin ciki da sanya Nijeriya a cikin ziyararsa ta farko a Afirka, ya ce, Nijeriya da Amurka suna da abubuwa dayawa recreation da batutuwan da suka shafi kasashen biyu.

Ya kara da cewa, zai yi farin cikin ginawa a kan tubalin da aka aza tsakanin kasashen biyu sama da shekaru 60 da suka gabata, yana mai bayyana cewa, sassan tattaunawar da Nijeriya za su hada da yadda za mu gina tattalin arzikinmu bayan annobar Korona, tsaro ga al’umma, da kuma matsalolin yanayi.

 

Atiku

Tsohon mataimakin shugaban Nijeriya, Alhaji Atilu Abubakar ya koka matuka gaya da yadda gwamnatin Nijeriya ke tafiyar da lamuran da suka shafi harkokin ‘yan bindiga da na masu garkuwa da mutane.
Abubakar ya bayyana haka ne a sa’ilin da yake maida martani kan sace wasu daliban jami’ar gwamnatin tarayya da ke Makurdi a ranar Lahadi da daddare.
Wasu daliban jami’ar solar bayyana cewar an yi garkuwa da abokan karatunsu ne da bindiga. Biyu daga cikin daliban suna karatu ne a tsangayar koyar da ilimin lantarki da na ilimin kimiyya.
Hukumomin makarantar da jami’an tsaro na ‘yan sanda dukkaninsu solar tabbatar da lamarin harin da aka kai.
A wani sakon da ya wallafa a shafinsa na Tuwita jiya Talata, tsohon mataimakin shugaban kasar wanda kuma ya sha kaye a zaben shugaban kasa na 2019,  ya bayyana cewa garkuwa da dalibai “Dole ne a dakile shi kada ya zama wani sabon al’amari a garemu,”
“Lokaci yayi da a matsayinmu na ‘yan kasa za mu fuskanci zahiri muna da matakan gagagwa a hannunmu. Wani bala’in dole ne a dakile shi tun kafin ya zo ya zama kaka-ni-ka-yi,” ya bayyana.
“Dole ne mu daina biye wa irin wannan aikin ta’addanci tare da sako-sako wajen magance matsalar. Abun ya isa haka kawai. Dole ne a samu kariya na rayuka da dukiyar dalibamu,”
“Idan an gaza hakan kuwa, to za a iya rasa aminci kan wannan sashin, hakan zai iya kara yawan daliban da basu zuwa makaranta a fadin kasar nan wanda kuma tunin ma mun zama shalkwatar kasar da yara suka fi yawa wadanda basu zuwa makaranta, idan hakan ta ci gaba da faruwa za a kara samun wadanda za su kaurace wa makarantu.
“Wannan ne ya sanya a baya na ce rashin hukunci na iya bada kofa. Lokacin da ‘yan ta’adda suka hau kan ta’addancinsu, hukunci sai ya biyo baya, wannan zai sanya suke jin shakka aikata danyen aikinsu, amma a daidai gabar da ake sako-sako da hukunta su, zai basu dama su cigaba da aikata ba daidai ba.”
Atiku ya nemi hukumomi a dukkanin matakai da suke daukan matakan da suka dace kan masu garkuwa da mutane da daukan bindiga ba bisa ka’ida ba, yana mai cewa ta hakan ne za a samu raguwar wannan matsalar.
Ya ce, ‘yan ta’adda sannu a hankali suna kara fadada ta’addancinsu wanda kasar nan kuma na kara fadawa cikin firgici da damuwa a kowani lokaci, sai ya nemi hakan ya dace ya sauya kawai.
Ya nemi a sanya dokar ta badi kan ilimi kuma a dukkanin makarantun kasar nan a jibge jami’an tsaro domin bada kariya.

 

Buba Galadima

A sakamakon cigaba da kai farmaki na hare-hare da ake cigaba da samu a sassan kasar nan, Buba Galadima, wani tsohon masoyin shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya bukaci gwamnatin tarayya da ta nemo sojojin haya daga kasashen waje domin su taimaka wa dakarun sojin kasar nan wajen yakar ‘yan ta’adda.
A ya yi wannan kiran ne a lokacin da ke jawabi ta cikin shirin gidan talabijin din Channels a wani shiri mai suna Dawn Each day na ranar Talata.
Galadima, wanda ya nuna tabbas a zahirance yake Nijeriya ta kasance cikin rauni na tunkarar matsalolin tsaro kuma akwai gazawa a cikin sha’anin sojin kasar nan.
Ya ce Nijeriya ta tafka asara, “Domin ta rasa kyakkyawar daman a neman tallafin kasashen waje,” bisa kin halartar jana’izar marigayi shugaban Chadi Idriss Deby.
“Saboda akwai shugabanin kasashen duniya da dama a wajen ciki har da na Faransa don haka wata cikakkiyar dama ce da shugaban kasa ke da shi wajen zuwa domin tattauna batutuwan da suka shafi tsaro da yadda za a inganta sha’anin tsaro a nahiyar Afrika.
“Kamar yadda muka sani ne, Shugaban Chadi ya kasance jarumi a wannan yankin. Ya na da sojojin da aka girke a Mali, Burkina Faso, da jamhuriyar Nijar da aka baiwa aikin wanzar da zaman lafiya.
“Don haka mun rasa wannan damar kuma saboda kwanaki biyu da suka wuce, hukumar soji ta Chadi ta bayyana cewar ba za ta taba tattaunawa da ‘yan bindiga ba, wannan yana nuni da cewa Chadi za ta iya fadawa yakin basasa da kuma yiyuwar bazuwar kananan makamai a Nijeriya.
“Muna da dakarun soji; amma basu da wadatattun kayan aiki na dakile matsalar tsaro a kudu maso gabas, arewa maso gabas, kudu maso tsakiya.”
“Hazakar sojojinmu ta yi karanci kuma muna bukatar bunkasa musu wannan kuzarin nasu.”
“Kunnuwar yaki a Chadi zai sanya kananan makamai su iya bazuwa a Nijeriya kuma sojojinmu basu da nagartar da za su iya tunkarar matsalar nan. Don haka muna bukatar a nemo sojojin haya da za su taimaka wa sojojinmu wajen magance matsalolin tsaro,” ya bayyana.

What's On Your Mind?