Matsalar Rashin Tsaro A Nijeriya Abin Kunya Ne – Dahiru Bauchi

- Advertisement -

Matsalar Rashin Tsaro A Nijeriya Abin Kunya Ne – Dahiru Bauchi

Daga Abubakar Abba, Kaduna

 

Khadimula Faidah Sheikh Dakta   Dahiru  Usman Bauchi ya koka da cewa, lamarin rashin tsarro na kara tabarbarewa a kasar nan, inda ya yi nuni da cewa babu abin da ya canza kan lamarin.

Shehun Malamin, ya yi wannan koke a lokacin rufe Tafisirin Alkur’aninsa na bana a Masallancin Juma’a na Tudun Wada Kaduna, ba kamar yadda aka saba a filin sukuwa na Murtala Muhammad Skuare Kaduna ba.

A cewar Dakta   Dahiru, “ Mun yi magana, mun sake magana, kuma ba za mu gaji ba, domin babu abin da ya canja”.

Shehin Isalaman ya ci gaba da cewa, abin da ya sa ake kafa gwamnati saboda ta kare rayukan mutane da kuma dukiyoyinsu daga barin wasu azzalmumai masu halakar da mutane.

“ Bai kamata gwamnati ta bari ana kashe mutane ba, wajbi ne gwmnati ta tsare gabobin al’ummarta da jininsu da kuma dukiyoyinsu,” in ji shi.

Ya bayyana cewa, bai kamata gwamnati ta bari ana kashe mutane ana kone dukiyoyinsu ba  kuma dole ne ta tsare mutuncinsu, ta kare mutuncinsu wannan shi ne amfanin gwamnati.

“Abu na farko dai shi ne, gwamnati ta kiyaye ran ‘yan kasarta, domin abin takaici ne yadda ‘yan bindiga suke sace mutane sai an biya kudin fansa kafin a sako su ko kuma a je a kone musu gidajensu kuma duk gwamnati tana gani ake yin wannan, babu wanda ya fita ido babu kuma wanda ya fita kuune.

Kazalika Shehin ya koka da cewa, “ Wannan abubuwa da kullum muke yin kuka a samar da tsaro a kasa, amma an yi shiru an zuba ido, wannan kunya ne kuma abin tir”.

Ya yi wa kasa addua’a da fatan Allah ya kawo karashen matsalolin da ake ci agaba da fuskanta, a karshe ya kuma yi wa manema labarai addu’ar fatan alheri saboda muhinmiyar rawar da suke takawa wajen bayar da sahihan rahotannin da za su taimaka wajen samun zaman lafiyar kasar nan.

- Advertisement -