Matawalle Ya Nemi Agaji Da Addu’ar Al’umma Don Kawo Karshen Ta’addanci A Zamfara

0
119

Matawalle Ya Nemi Agaji Da Addu’ar Al’umma Don Kawo Karshen Ta’addanci A Zamfara

Gwamna Bello Matawalle na Zamfara ya yi kira ga mazauna jihar da su fara addu’o’i na mako guda don neman taimakon Allah don kawo karshen ‘yan bindiga, ta’addanci da sauran laifuka a jihar.

Wata sanarwa dauke da sa hannun sakataren labarai na gwamnan, Jamilu Iliyasu, wacce aka baiwa manema labarai a Gusau ranar Lahadi ta ce gwamnan ya yi wannan rokon ne lokacin da sarakuna 17 na jihar suka zo yi masa ta’aziyya kan rasuwar Shugaban PDP na jihar, Alhaji Ibrahim Mallaha.

Sanarwar ta ce gwamnan ya lura cewa “gwamnatinsa na yin iya bakin kokarin ta don kawo karshen matsalar ‘yan fashi da makami, sace-sacen mutane da sauran ayyukan ta’addanci a cikin jihar ta hanyar amfani da ice da sanda.

“Ya ce akwai bukatar dagewa da addu’o’i domin neman karfin kudurar Allah.”
Gwamnan ya bayyana cewa a matsayinsu na sarakunan gargajiya wadanda suka fi kusanci da jama’a, ya kamata sarakuna su marawa gwamnati baya ta hanyar hadin gwiwa da nufin tabbatar da tsaro a jihar.

Don haka, ya umarci sarakunan da su hada kan Limamai da sauran Malaman Addinin Musulunci da su dukufa wajen gudanar da addu’o’i na musamman a masallatai da sauran wuraran tarurrukan wa’azi don kawo karshen matsalar, kuma ya gode musu kan wannan ta’aziyya.

Da yake jagorantar takwarorinsa, Shugaban Majalisar Sarakunan jihar, wanda kuma shi ne Sarkin Anka, Alhaji Attahiru Ahmed, ya ce photo voltaic je gidan Gwamnatin ne don yi musu ta’aziyya ga Gwamnati da jama’ar jihar kan rasuwar Alhaji Ibrahim Mallaha, da kuma dattijo, Sen. Yushau Anka, wanda duk photo voltaic rasu ne a makon da ya gabata.
Sarkin ya ce marigayi Ibrahim Mallaha ya yi rayuwa mai sauki wacce ta dace sauran ‘yan siyasa su yi koyi da ita, sannan ya yi addu’ar Allah Madaukakin Sarki ya gafarta masa dukkan kurakuransa kuma ya ba iyalansa karfin jure rashinsa.

Sauran wadanda suka halarci gidan gwamnatin don yi musu ta’aziyyar photo voltaic hada da Malaman Addinin Musulunci na Jihar Zamfara a karkashin inuwar Majalisar Ulama ta Jihar Zamfara karkashin jagorancin Shugabanta, Malam Abubakar Aliyu, da kuma Kungiyar Kwadago ta reshen jihar (NLC), karkashin jagorancin Shugabanta, Kwamared Bashir Mafara.

What's On Your Mind?