Matata muguwace ta na fallamin Mari tai ta Zagina – Magidanci ya gayawa Kotu

0
151

Matata muguwace ta na fallamin Mari tai ta Zagina - Magidanci ya gayawa Kotu

Wani magidanci ya kaiwa kotu kara inda yake neman ta raba aurensa da matarsa da suka shafe shekaru 7 suna tare.
Ya bayyana wa kotun Ille Tuntun dakw Ibadan cewa matar takan rika marinsa hadda zagi.

Mutumin ne suna, Gbade Olaniyi ya bayyana cewa, Matarsa, Bunmi Olaniyi muguwace inda yace ya gaji da zama da ita.

Kamar Yadda Hutudole ta rawaito cewa Itama matar ta bayyana cewa ta amince a rana aurensu, inda tace shima yana dukanta ka kuma cin amana gashi baya kula da ita.

Tace tabbas ta faffalawa mijin nata mari har sau biyu bayan da ta ganshi da wata ma kwabciyarsu suna rike hannu.

Tace kuma bayan da ta je gida haihuwa, ta dawo ta tarar wata mata na dafa masa abinci, inda tace a nan ma solar yi fada ta mammareshi.

Mai shari’a, Olasunkanmi Agbaje ya daga karar har sau biyu amma daga baya, Mijin ya ce ya janye karar saboda cocinsu ta Shiga maganar, kamar yanda Tribune ta ruwaito.

What's On Your Mind?