Matasan Arewa: Gaba Kura Baya Siyaki (II)

0
86

Abin takaici sport da haka shi ne ba iyaye ba ne suke kago wadannan, matasan ne da kansu suke ganin photo voltaic fi iyayensu wayewar kai, domin kuwa haka nan suke karantawa a mujallu da jaridu ko su kalla a fina-finai sport da wanda wasu jinsi ke yi? Tun da kuwa haka ne mai zai sa ba za su yunkura ba su kawar da wadannan munanan dabi’un da ke cutar da su, suna yi ma rayuwarsu tarnaki? Shi ke nan don matashi na so a ce ya dace da dabi’un zamani wadanda suka sha-ban-ban da al’adunsa sai ya kuntatawa kansa kafin ya yi aure, idan ba haka ba zai tabbata a matsayin tuzuru? Irin haka ne kuma ke sa ‘yan mata yin kwantai a dara, da wuya ake samun mai tayawa. Lallai da sake sport da wannan al’amari, domin su wadanda ake kwaikwayon dabi’unsu arzikinsu ba daya ba ne da namu, yanayin rayuwarsu ta bambanta da irin tamu, sa’annan kuma ba abin da zai sa su kwaikwayi irin namu dabi’un komai saukinsu da kuma fin dacewarsu. An dai ce wanda ya ce a yi musanya, ya raina nasa.

Wasu na cewa tsananin rashin aikin yi ne ko wata kwakkwarar sana’a ce ke kai matasan kasar nan shaye-shayen miyagun kwayoyi. E, ana iya cewa haka, amma a bisa gaskiya wannan ba shi ne babban dalilin da ke haddasa haka ba. Da farko dai wannan wata al’ada ce da matasanmu suka koya daga Turawa, kuma ko da wannan mummunar dabi’ar ta yi kamari a can kasashen Amerika da nahiyar Turai sai su Turawan suka dukufa ka’in da na’in don magance ta, ganin yadda take sabarta ‘ya’yansu, wadanda idan ba a yi hankali ba za su ta shi ba su da wata mamora ga kasarsu, ko su karan kansu. Shi ya sa dokar sayarwa ko shan miyagun kwayoyi a kasashen ketare ta fi kowacce tasiri, kuma Turawa ba su wasa da ita domin sukan tsallaka har cikin kasashen da ake samar da wadannan miyagun kwayoyin su hukunta masu aikewa da kwayar kasarsu, ana bata masu ‘ya’ya.

Duk da cewa a can kasashen ne ake yin kwayoyin da matasanmu ke hadiya a nan cikin gida,  amma an fi mu’amala da su a kasashe masu tasowa, inda Turawan ke bari da gangar ana haka don photo voltaic san cewa gwamnatocinmu ba za su matsa wajen hana shigowa da su ba, hakan kuma zai sa matasan kasashen Turai su samu aikin yi a masana’antun yin kwayoyin da za su yi ta habaka, namu kuma na ta sha, suna lalacewa, babu kuma abin kirkin da za su iya tabukawa, hatta gonakin kakaninsu ma ba su iya nomawa.

Matasan Arewa: Gaba Kura Baya Siyaki (II)

Ai idan har an samu nasarar hana shan miyagun kwayoyi, to me kuma dillalansu  da masu daure masu gindi a nan cikin gida za su yi? Shi ya sa a wasu kasashe masu tasowa, ciki har da na nahiyar Afrika ake fuskantar matsalolin juyin mulki, domin kuwa duk gwamnatin da ta nemi karyawa dillalan miyagun kwayoyi a kasashen tsinke tsire a idanu, ko toshe masu hanyoyin tatse arzikin kasarta, yanzu-yanzunnan za a wancakalar da ita. To idan kuwa haka ne ya kamata matasanmu su yi wa kawunansu kiyamul-laili, su guji shan miyagun kwayoyi don su tsira da mutuncinsu, su kuma yi ban-kwana da talauci.

Dangane da irin wannan al’amarin ne matasanmu suka tsinci kansu cikin wani halin da bai dace da al’adun iyayensu ba, bai kuma zo bai daya ba ba da na wadanda suke kwaikwaya, domin kuwa idan da za su kusanci Yahudu da Nasaran da suke bi ido rufe, kyarar su za yi, su kuma sa a kore su, a kuma zuba ruwa a wuraren da suka kasance domin wai wari da karnin da jikinsu ke yi za su sa wadancan Turawan haraswa. To wajibi ne sai matasanmu photo voltaic guji jallabiyya da shakwara da jamfa, har ma da kaftani da kufta da hula kubiyo ko kube da tagiya, photo voltaic koma suna sa wani irin wando wai shi tiri-kwata da wata jaket kamar ta alkalin kyankyasai, sa’annan su kakaba wata hular ulu irin ta yaro goyayye, mai randagin kai? Tilas ne su dinga kwama wasu gilasai kaman heliman ‘yan safiyo, ko kuma su kwaga wasu takalma, kan-kura, irin na Sauna Jack kafin a ce kansu ya waye? Da wane dalili ne matasanmu ke yin shiga irin ta bakaken fata, marasa galihu na nahiyar Amerika ta Arewa, wadanda fafaren fatar can suka tsana, har suna kiransu Negroes don tsabar walakanci? To shi ne kuma matasanmu ke sha’awar a kira su  da wancan suna na Negroe, da aka takaita  zuwa Niga, don ya yi irin shigarsa? Wai shin suna sane da cewa talauci ne ke hana wadancan nigogin shiga mai kyau, irin ta Turawar da ke kyamar su? Shi ne matasanmu ke kukewa yin kwalliya da kayan sanyi a cikin uban zafin wannan kasar? Kaico! Allah wadan batar basirar da ta ke addabar matasanmu wadanda ke zamantowa jimagu, su ba dabbobi ba, ba kuma tsuntsaye ba, watau photo voltaic  yi shiga irin na farar fata, photo voltaic kuma bambanta da bakaken fatar da suke cikinsu..

Matsalolin Arewa Su Ka Sa Na Fara Rubutu – Meena Abba

Tuni dai matasan kasar nan, musamman na Arewa, suka yi ilmin karbi-a-jika, amma photo voltaic kasa gane haka. Photo voltaic kasa fahimtar yadda takwarorinsu na sauran sassan kasar nan suke. Ana iya cewa wadancan matasan photo voltaic san ciwon kansu, ko kuma iyayensu ba su bari su wofantar da kansu a banza. Sa’ilin da matasan yankin Kudanci ke kasancewa tare da iyayensu, bayan tashinsu daga makaranta, suna koyon sana’o’in da suka gada, na Arewa kuwa sai  zaman banza da aikin wofi. Ba su da wani abin yi sai bin mafarauta, suna sanya warwaron robobi a hannayensu, suna shafa tozalin kifil a idanunsu, su yi ta yawo da karnuka lungu-lungu, sako-sako wai su kauraye. Haka nan za su tabbata tutur cikin mawuyacin halin wahalar da zuciyarsu da jikinsu, ba su amfani kansu da komai ba, iyayensu kuma ba su cin gajiyarsu.

Daga cikin matasan da ba su da karfin halin  yawon farauta akwai masu zaman gida, ba aikin fari balle na baki, ba su kuma taimakon iyayensu balle malamansu, ba ruwansu da na gaba da su, haka nan ma makwabcinsu bai isa ya sanya ko ya hana su ba. Muddin dai ba matasan Arewa photo voltaic yi watsi da wadannan dabi’un ne ba, su ka rungumi sana’o’in da suke ganin photo voltaic fi karfin yi don tsabar girman kai da takama da asali, har  suka bari ‘yan Kudu, suka hauro kasar su, suka mamaye su, ba to ba shakka  zai yi wuya a kai ga magance matsalolin da ke yi masu tarnaki, yana hana su sakata, su wala a kasar haihuwarsu. Haka nan ma dukkan kokarin da ake yi don inganta al’adu da dabi’u da kuma tsarkake addinin al’umma zai ci tura. Ya dai rage wa ga jama’an Arewar ce gaba daya, ba ga matasa ba kadai, domin kuwa a yanzu su na cikin wani mawuyacin hali na gaba kura, baya siyaki.

What's On Your Mind?