Matar Gwamnan Neja Ce Ta Yi Min Kyautar Da Ba Zan Taba Mantawa Ba –Allyn Waka

- Advertisement -

Matar Gwamnan Neja Ce Ta Yi Min Kyautar Da Ba Zan Taba Mantawa Ba –Allyn Waka

Hassana Aliyu Birgi, matashiyar ‘yar siyasa ce kuma mawakiya a bangarorin rayuwa da dama. A wannan zantawarta da wakilinmu Muhammad Awwal Umar, ta tabo batutuwa da dama da ya shafi rayuwarta.

Da farko zan so ki bayyana wa mai karatu matsayin ki.

Assalamun’alaikum warahmatullahi! Da farko, sunana Hassana Aliyu, amma a yanzu an fi sani na da Bintu Allyn waka. An haife ni wani kauye mai suna Birgi cikin karamar hukumar Bosso a jihar Neja. Na yi karatun addini da na boko dai dai gwargwado.

Yanzu ina matsayin ‘yar siyasa kuma mawakiya ina kuma ina zaune da al’umma lafiya babu tsangwama, a takaice wannan shine kadan daga cikin labarina.

Shin tauraruwar ta taba yin aure, in kuma ta taba wani matsayi auren yake ciki yanzu.

Gaskiya ban taba yin aure ba, amma ina da niyya idan lokaci ya yi insha Allahu. Kasancewar aure ko yaushe lokacin sa yake jira, idan lokacin ya yi sai an yi. Idan lokacin sa bai yi ba komai yunkurinka sai ka jira. Sannan kuma dama karshen dukkan burin mace musulma shine ta yi aure.

Ga ki, mawakiya kuma ga ki ‘yar siyasa ya abin yake.

Gaskiya ne, gani mawakiya kuma yar siyasa. Wannan ba wani abu ba ne da za’a ce ya zama hadin gambiza ba, duk da kasancewar waka da siyasa mabanbanta ne ta wata fuskar. Amma ta wani bangaren abubuwa ne da suke kan turba daya, kasancewar dukkanninsu abubuwa ne da ake yi domin hidimtawa al’umma da su. Mawaki, koyaushe yana kokarin kawo wa al’umma da yake cikinta wani sako wanda yana kokarin hidimtawa al’ummar ne. Hakan nan dan siyasa na zahiri shima yana yi ne domin hidima ga al’ummarsa. Dan haka ka zama mawaki kuma dan siyasa ka hada hidima biyu ga al’umma rka ke nan.

Kuma ba kaina aka fara samun mawaki dan siyasa ba. A wasu Jihohi a kasar nan an samu mawaki ya yi takara kuma yaci zabe yanzu haka yana majalisar tarayya yana wakiltar al’ummarsa. Sanna an samu da yawan mawaka suna samun “appointment ” a gwamnati, yanzu suna rike da muƙamai.

Ni kaina Alhamdulillah, ina alfahari da mutanena kasancewar ina mawakiya kuma ‘yar siyasa “group” su kace ni suke so su baiwa amanar kansu. Jama’a suka tsayar dani, Alhamdulillah na yi takara, wallahi babu tsangwama, saboda ‘yan takara tara suka fito, idan ka hada da ni, goma ke nan, amma suka zabe ni, ni ce na zo ta biyu, ai sai godiya ga Allah subhanahu wata’alah.

Kin dade da fara wakoki kuma solar samu karbuwa a wajen jama’a, shin wasu irin wakoki ki ka fi mayar da hankalin ki akan su.

Wakar siyasa ita ce na fi yawan yi, sai kuma bangaren yabon Annabi Muhammad (S.A.W) ina rubutawa na baiwa dalibai su rera maza da mata. Kuma nima wani lokaci sai na shiga studio na rera.

A cikin birnin zuciyata na fi son yabon Annabi Muhammad (S A.W). Amma a fili na fi nuna son wakar fadakarwa, sakamakon kalubale da mu ke fuskanta a kasata Nijeriya, wanan shi ne.

Matsayin ki na matashiya wasu shawarwari za ki baiwa matasa ‘yan uwan ki kan halin rayuwa, musamman dogaro da kai da neman abin yi.

Matasa! Magana akan matasa na da matukar mahimmanci. A cikin rukunonin na zamantakewar al’umma, rukunin matasa shi ne yanki mafi tasiri. Ana cewa idan kana son fahimtar goben kowace al’umma to ka kalli yanayin rukunin matasanta. Matasa sune kashin bayan zamantakewar al’umma, sune suke kawo cigaba a cikin al’ummansu. Idan solar zama managarta za’a samu nagartacciyar al’umma idan solar baci kuma al’ummar ta ɓaci.

Dan haka na ke kiran wannan rukunin matasan al’ummar tamu da mu tashi mu fahimci mune kashin bayan matsalar zamantakewarmu. Mu farka mu kawo sauyi cikin al’ummarmu.

Matasa ya kamata mu fara neman koyon halin kwarai wanda zai saka mu zaman mutanen kirki kuma na kwarai shi ne farko ma kafin ilimin boko. Ya zama muna da dabarar zamantakewa da sanin hakkokan mu da hakkookan sauran al’ummar da muke zama cikinta.

Sannan akwai bukatuwar mu zama masu neman aikataccen ilimi wanda zamu iya aiki da shi da kan mu ba sai mun jira gwamnati ba. Ilimi kuma ya hada da na addini ga dukkannin addinin da ka ke bi.

Sannan akwai matuƙar bukatuwar matasa su zama masu dogaro da kan su. Matashi ya rike wata sana’a komai kankarta ta fi masa zaman jira ya yi banbabanci yana karbar umarni daga wasu mutanen wanda idan aka yi rashin sa’a sai ya fada mugun hannun da za’a dinga anfani da shi wajen aikata miyagun aiki. Mafi sharrin mutum shine wanda al’ummar da take zaune da shi ba ta fita daga sharrin mugun aikinsa ba.

Lokacin da ki ka fara samun karbuwa a fagen waka, sai kuma ki ka tsunduma a harkokin siyasa har da tsayawa takarar kansula. Ya abin yake.

To da waka da siyasa dukka huldodi ne na mu’amala da al’umma, kuma tun lokaci mai tsawo suna da alaka da junansu. Akwai waka a cikin siyasa tun jamhuriyya ta farko inda mawakan ke tallata kudurorin ‘yan siyasar, haka ‘yar shigowar wannan zamanin an ci gaba da amfani da waka wajen tallata dan takara da manufofinsa, ka ga akwai makusanciyar alaka tsakanin siyasa da waka, idan kana cikin ɗaya waka ko siyasa za ka iya fahimtar yadda za ka kara bayar da gudunmawa a daya bangaren na waka ko siyasar.

Sakamakon haka lokacin da na fara karki a waka sai na kara fahimtar akwai rawar da zan iya takawa a siyasa. Wannan shine ya jawo hankalina na shiga siyasa ka’in-da-na’in har ta kaini ga tsayawa takara.

Wani bambamci ki ka gani tsakanin dandalin siyasa da harkar waka.

To duk da dai yadda na nuna a baya cewa waka da siyasa akwai inda suke da alaka, amma kuma akwai inda suke da bambanci.

Waƙa ta fi jibantuwa da kebewar tunani, tana bayar da damar ka kebance tunanin ka wajen wane sako ya kamata ka aikawa al’umma. Kana da damar sai ka kammala aikin ka a tsana ke sannan ka fito da shi zuwa ga al’umma. Waka kana iya zama “impartial” ba tare da ka shiga wata kungiya ba, kuma za ka cigaba da harkokin ka yadda ya kamata, amma ga siyasa abun ba haka yake ba. Sport da siyasa lamari ne da yake tu’ammali da al’umma ko dare ko rana.

A siyasa baka da lokacin kan ka sosai, ko yaushe kana cikin karbar uzurorin al’ummar ka babu dare babu rana. Siyasa bai yiwu wa sai da jama’a, za ka nemo wasu, wasu kuma za su neme ka. Idan kana da jama’a a siyasa za’a nema ka, idan kana son jama’a a siyasa dole ne ka nemo su. A kasin mawaki, shi mawaki mai jama’a ne a fili da badini, kashi casa’in na mawaka neman su ake yi.

Hassana ganin gwagwarmayar da ki ka gani a tafiyar siyasa ko kina da kudurin ja baya dan tsayawa akan turba daya.

Ko kadan! Bani da tunanin janyewa daga siyasa, ka sani cewa siyasa kusan al’ummata ce suka sdnya ni a ciki, a garin mu da farko an dauko ni ne na zama ina wakiltar kauyenmu a siyasance, maigarin mu da dattawan garinmu ne suka yanke hukuncin su zabeni, su turani a matsayin wakiliyarsu a siyasan ce. Ka ga kuwa babu yadda za’a yi na karaya na tafi na ce musu na gaza. Dole ne na yi iyakar raina domin cika wakilcin iyaye na da sauran al’ummar garina. Kuma kwarin guiwa ma na ke kara samu akan na sake jajircewa akan turbar da na ke son na kasance mai fadakarwa a bangaren waka kuma ina da niyyar sake tsayawa takarar neman wani mukamin a siyasan ce, in Allah ya yarda. Wannan shine! Siyasa ba juya baya sai lokacin da Allah ya kuma ya kaddara ikon sa.

A kowani lokaci ana kira ga mata da su shiga harkokin siyasa, wanda ke kin jaraba. Shin kina ganin wannan kiranyen da gaske ne na cewar ana son tafiya da ku a harkokin mulki.

Gaskiya ne, amma ba’a inganta tafiya da mata a siyasan ce ba, sabanin yadda ake nunawa mutane a fili. Yanzu idan namiji ya fito takara za ka ga an tsaya masa tsayin daka don ganin ya yi nasara, wanda ba’a yiwa mata hakan. Idan mace ta fito takara sai a bar ta da mata ‘yan uwanta ba za’a tallafa mata da komai ba, sai dai ma ace kada ku yarda mace ta mulke ku. Idan ana son jama’a mata ake nema, idan ana son masu fada da cikawa mata ne. Sau da dama za ka ji dan siyasa yana cewa ya fi son ya baiwa mace amanar kuri’arsa. Saboda ya san tana da amana ba kamar wasu mazan ba. Da hakan na ke jan hankalin gwamnati da ta zamo mai fada da cikawa ba maganar baki ba.

A baiwa mata amana a gani, domin ” Rana bata karya”.

Ina so na ja hankalin mata masu ra’ayi irin nawa kada su karaya gyara muke so mu kawo a cikin al’umma, mu kara zage dantse dan ganin an daina anfani da mu wajen neman kuri’a. Mu zamo da mu ake damawa don hakan ne zai ba mu damar cika alkawarin da muke yiwa masu ba mu amanar kuru’unsu, Allah yasa mu dace.

Ana zargin da yawan matasa mata musamman ‘yan siyasa da cewar ba cancanta ko dacewar dan takara ke kai ku ga marawa dan siyasa ba, illa inda za ku rika samun abin biyan bukatun yau da kullun, shi yasa ba ku cika rike mutuncin ku ba.

To gaskiya ba zan iya cewa ba haka ba ne. Ana iya samun wasu da suka dauki siyasar ta wannan fuskar wanda ba haka ya kamata ya zama ba. Wannan kuma ba zai kebanta ga mata kawai ba, har da mazan ana iya samun wannan halayyar.

A bangaren maza ma abin ya yiwa ‘yan siyasa maza kanta a zuciya ba mata ba, mu mata an san mu da amana da rike alkawari, abinda na sani shi ne, ai shuwagabannin mu na siyasa maza ne. Mafi rinjayen ranshin cancanta yana cikin mazaje ‘yan siyasa don sune suke yin alkawari idan hakon su ya cin ma ruwa sai su manta da mafarin su, shiy a muke kira ga al’umma su baiwa masu amana dama don cigaban kasar mu.

Sai dai ana kallon fifikon illar ne ga mata wala Allah domin ana ganin cewa su mata iyayen al’umma ne. Mata sune ka renon kowace al’umma ta duniya domin haka ake kaffa kaffa da yadda suke gudanar da al’amuran su. Ko ya ya suka samu tasgaro sai ka ji ya yi zafi. Wannan yasa ake ganin laifinsu yana fitowa fili.

Maganar gaskiya, wakilai mata a siyasa bai kamata su fifita dan abin hannun da suke samu ba akan nagartar dan takara. Ya kamata su zama wakilai na hakika wajen tantance nagartar dan takara da fahimtar kudirin sa na ciyar da al’umarsu gaba, da ya ke da shi fiye da mai da hankali ga dan hasafin da zai ba su wanda ba isar su, dan ba yanke talauci zai yi ba. Amma ni a nawa bangaren ba yabon kai ba inda za ka samu wadanda mu ke mu’amalar siyasa da su za su fada ma ka wace ce ni akan akidar siyasa, ba sai na bayyana ba.

Sannan a yanzu muna kan kokarin kaddamar da wani yunkuri na canjawa mata akidar siyasa su zamo nagartattu domin akwai alamun siyasar za ta dawo hannun su.

Wane kuduri ki ke da shi nan gaba a rayuwa.

kudirina na farko shine cigaba da karatu. Na biyu, ina da wudirin sa ke tsawa takarar neman wani abu a siyasan ce. Sauran ina da kudirin idan muna cikin masu rai da lafiya na ziyarci dakin Allah, garin Annabi Muhammad (S.A.E). Sauran tsakanina ne da Allah. Allah ya sa mu dace.

Wanne shawarar za ki baiwa ‘yan uwanki matasa musamman mata.

Shawarata ga matasa mata mu zamo masu abin yi, shi ne sana’a ko a cikin gidanki za ki yi sana’a. Domin sana’a maganin wulakanci ne, sana’a maganin talauci ne, talauci yana tsoron mai dogaro da kan shi. Maza da mata mu kama sana’a, mu baiwa mara da kunya. Allah ya bamu abinyi a rayuwa wanda zai amfanemu duniya da kiyama.

Zuwa yaushe ki ke fatar barin sana’ar waka.

Gaskiya Allah shi ne masani, ban sani ba ko zuwa wane lokaci zan daina, komai tsari ne daga Allah.

Kina jin yaruka kusan uku, Gbagyi, Nupe da Hausa dukkansu kina yin waka da su.

Eh, yarukan da ni ke ji solar fi uku, amma mu bar su a ukun. Nupe ba koyo na yi ba, Yare na ne. Ina yin waka da Nupe kuma ina yi da Hausa insha Allah.

Adadin wakokin da farawa zuwa yanzu za ki iya ba mu jimillarsu.

Gaskiya ba zan iya fadar adadin su daidai ba. Amma zan kiyas ta, za su kai kamar dari biyu da ‘yan kai insha Allah.

Wace waka ki ka yi da ki ka fi sonta kuma me ye dalilin.

Ina son dukkan wakokina amma na fi son wata wakar mai taken RAYUWA. Gaskiya dalilina shi ne wakar fadakarwa ce sosai, wa’azantarwa ce kuma nishadantar wa. Sai wakar cinnaka wadda ba ta bar kowa ba. Nagode.

Wace waka tafi ba ki wahala.

To wakar sammatsi gare ta. Akwai wakar da za ka ci mata buri amma sai ka je yinta sai ta murde maka. Wadda ka ke ganin za ta baka wahala sai kuma sai aka iske ka yi ta cikin kwanciyar hankali.

Wace kyauta aka taba yi maki da ba za ki iya mantawa ba.

Gaskiya matar gwamnan Neja Dakta Amina Abubakar Sani Bello ita ce ta yi min kyautar da ba zan taba mantawa da ita ba.

Wani abu ki ka fi so a rayuwa, kuma wani kike kinsa a rayuwar ki.

Abinda na fi so a rayuwa ta shi ne gaskiya. Sannan abinda ba na so shi ne karya.

 

- Advertisement -