Matakan Da Ake Dauka Kan Masu Lalata Da Dalibai A Jami’o’i

0
84

Matakan Da Ake Dauka Kan Masu Lalata Da Dalibai A Jami’o’i

Daga Muhammad M. Awwal,

Mai karatu barkanmu da sake saduwa a wannan fili namu, wanda kullum muke bayyana cewa manufar wannan fili shi ne hango wasu abubuwa masu hadari ko masu amfani a rayuwar mu ta yau da kullum, wadanda idan aka bi su, ko aka kiyaye za a samu amfani.

A makonnin da suka gaba muna yin bayani ne recreation da yadda wasu marasa kishin zuci, kuma marasa kishin al’ummarsu suke bata ’ya’yan jama’a, musamman a manyan makarantun kasar nan, inda wannan abu ya fi kamari da Jami’o’i da sauran makarantun gaba da Sakandare.

In dai ana biye da mu muka magana kan batun nan ne na badala, ko kuma lalata da ’yan mata daga Malamansu a wadannan manyan makarantu da muke magana a kai, wanda kuma a baya mun yi bayanin cewa batun har ya kai gaban Majalisar Dattawa don sanya doka mai karfi a kan haka.

A irin wannan rubutu nawa ne wani mai karatunmu ya kira ni a waya, duk da dai na fi son a rubuto mani sakon kar-ta kwana ne, wato tedt. Domin ya fi mana sauki, kuma wani lokaci za a iya kira a lokacin da ba za mu iya amsa wayar ba, don haka ne ya fi kamata a aiko da Tedt din.

Wannan Malami mai suna Malam Hasan Kargon Kunci daga jihar Kano, ya kira ne ta lamba 0703 044 3374, ya yi bayanai masu ratsa jiki recreation da wannan annoba da muke magana a kai, inda ya ce matsala ce da ke damun duk wani mai kishin iyalinsa da kuma al’ummarsa.

Malam Hasan Kargon Kunci ya ce irin wadannan abubuwa, abubuwa ne da ya wajaba duk wani mai yi wa kasar nan fatan alhairi ya kyamace shi ya kuma yi iya abin da zai iya yi don maganin abin.

Yana mai cewa su kansu irin wadannan Malamai yana da muhimmanci su fahimci cewa akwai fa ranar sakamako, ranar da za a tambayi kowa abin da ya aikata. Malamin ya ce haka su ma matan da suke bayar da kansu don su samu abin duniya, to su sani cewa komai na duniya mai karewa ne, lahira ce matabbata.

Ba a kan Malamai da daliban Malam Hasan ya tsaya ba, ya kuma yi korafin cewa su ma wasu iyayen ba sa taimakawa, domin ba sa jawo ’ya’yansu a jiki ta yadda za su nuna masu irin hadarin da ke tattare da wadannan abubuwa. Ya ce domin sai iyaye solar rinka zama da ’ya’yansu suna sanin matsalolinsu ne za iya ba su shawara.

Ya ce, amma abin takaici mu a al’ummar mu, su babu ruwansu da haka, sai ka ga magidanci bai damu da harkar ’ya’yansu mata ba, babu abin da ke hada su da su, wata kila sai gaisuwa da secure, daga shi ne babu wani abu.

Mutum ba zai zauna da ’yarsa ya ji me ke damunta ba, me aka yi mata, me za a yi mata? Idan har uba bai samu irin wannan damar ba, to da haka yaran ke fadawa cikin wani mawiyacin hali, su iyayen ba su ma sani ba. Sai a ce za a bar wa iyaye mata, alhali su kuma hidindimun cikin gida ya ishe su.

Malam Hasan ya kuma jawo hankalin irin wadannan Malamai don su san da cewa da su ne ake koyi, don haka wajibinsu su nuna kyakkyawar dabi’a. Su kuma iyaye su kasance suna kusantar ’ya’yansu don jin matsalolinsu.

Saboda haka irin wannan abu a har kullum muna fadin cewa abu ne da bai dace ba, kuma wajibi ne a yake shi ta duk inda za a iya. Muna godiya da wannan tsokaci na Malam Hasan, muna kuma maraba da kowa da kowa. Domin kamar yadda na kan ce, wanann fili yana da mara da masu karin haske.

Idan muka ci gaba da bayaninmu kuwa, wani abu mai faranta rai shi ne, bayan matakan kora da aka dauka a wasu jami’o’in kasar nan, kamar yadda na kawo bayani a baya, a shekaran jiya ma Kwalejin kimiyya da fahasa ta Kaduna Polytechnic ita ta bi sahun daukar irin wannan hukunci kan irin wadannan miyagun Malamai.

Kwalejin ta sallami wani Tsohon Shugaban sashen ne wanda aka samu da laifin yi wa dalibai mata barazanar lalata. Kamar dai yadda jami’in hulda da jama’a na Kwalejin ya bayyana a wata takatdar manema labarai da ya fitar.

Sanarwar ta ce sakamakon koke da wata daliba ta kai gaban Hukumar Kwalejin, ya sa kwamitin ladabtarwar ya gayyaci Malamin don amsa tambayoyi, wanda kuma sakamakon zaman ya tabbatar da cewa ya aikata laifin, ba tare da bata lokaci ba Hukumar gudanawar Kwalejin ta bayar da umurnin a sallame shi daga aiki.

Irin wannan mataki ne mu ke magana a kai, musamman na ita dalibar, haka shi ma na Hukumar Kwalejin, wanda har ma wasu ke ganin bai kamata ana barin abin a haka ba, kamata ya yi a rinka hadawa har da kai su gaban kuliya don yi masu hukuncin da ba za su sake maimaita irin wannan abu ba.

To amma ko ma dai mene ne, muna matukar jinjina ga shugaban Kwalejin, Farfesa Idris Bugaje bisa wannan hukuncin da suka dauka, wanda kuma ana jin zai iya zama darasi ga bata gari irinsu.

What's On Your Mind?