Mata Sha’irai Ba Su Da Wani Burin Da Ya Wuce Raya Sunnar Manzon Allah (S A W) – Maimuna Ibrahim

- Advertisement -

Mata Sha’irai Ba Su Da Wani Burin Da Ya Wuce Raya Sunnar Manzon Allah (S A W) – Maimuna Ibrahim

Daga Saddek Muhammad.

A wannan lokaci an samu shigowar Mata cikin harkar bege wanda aka fi sani da yabon Manzon Allah, wanda a ke ganin kusan matan ma su fi mazan yawa.

Maimuna Ibrahim Ismai’l tana daya daga cikin Sha’irai mata da suke cikin harkar a yanzu, kuma ta yi wakoki da dama na yabon Manzon Allah S A W, don haka ne wakilin mu ya nemi jin ta bakin ta dangane da tarihin rayuwar ta, da kuma harkar bege da Matsalolin da su ke cikin harkar, don haka sai ku biyo mu ku ji yadda tattaunawar ta mu ta kasance.
Da farko za mu so ki gabatar da kan ki ga masu karatun mu.

Ummi Burdatu. To da farko ni dai suna na Maimuna Ibrahim Ismail Amma dai an fi sani na da sunan Ummi Burdatu, kuma an haife ni a Darki ta karamar Hukumar Wudil da ke jihar Kano. A shekarar 1998 aka haife ni, sai dai mun dawo garin Kano a 2004 na yi makarantar Firamare ta Kabiru Kiru da ke unguwar Sharada na yi karamar Sakandare Salanta Sharada Na yi babbar Sakandare ta G G S S Jaen Sabon Gida.

A yanzu kuma ina Aminu Kano School ina shekara ta biyu. Kuma a bangaren karatun Arabia, na yi Islamiyyu a kalla guda uku in da na yi saukar Alkur’ani tare da hadda kuma na sauke wasu littattafai.
To ko ya ya aka yi kika samu kan ki a cikin harkar yabon Manzon Allah S A W?
Gaskiya na samu kaina a harkar yabon Manzon Allah S A W tun ba ni da wayo. Saboda na kasance ma’abociyar son waka tun ina yarinya, har a kan ba ni labarin cewa ko aikena aka yi ina dawowa da waka a ke gane na dawo ita ce sallama ta, to inda na fara kasida a wata Makaranta ce da na taba yi Hidayatus Sufya in da na fara da yin amshi to da Mauludi ya zo sai aka ba ni na yi da bai haka dai ana ta tafiya na fara rubuta baiti biyar zuwa sama har na zo Darikun Huda na yi kasida mai baiti 15 a nan Malamai suka zauna suka duba aka kira ni aka tambaye ni ko za a bar ni a gida na je Studio na ce ban sani ba, Amma ina tsoro, saboda gidan mu ‘yan Izala ne kafin wannan wannan ma a kwai makarantar da na yi wadda a nan ma ina yin wakar da baki sai Malamin mu ya nemi mu je da sauran Dalibai ya yi kasida za mu hau aka Hana ni a gida, to a wannan makaranta Darikal Huda nan ne na yi nasara na fara shiga Studio a shekarar 2017, wannan shi ne tarihin fara yabon Manzon Allah S A W a waje na.

Ita harkar Yabon a yanzu wasu suna rubutawa da kan su su rera, wasu kuma ana rubuta musu a rera sai su hau Karin ke a wanne matsayi kike?
E gaskiya akwai kasidu na ni na rubuta na rera kamar guda biyar, akwai wadanda rubuta mini aka yi kamar biyar su ma, sannan rubutattun da nake da su cikakku wanda na gama aiki kawai au ke jira Allah ya hore a kalla solar kai guda takwas, sai wadanda ba a kai ga kammala su ba su ka suna da yawa.

To wacce kasida ce kika yi ta farko da ta fito da ke?
Kasida ta farko ita ce Labbaika Annabin Allah, Barka da zuwa Ma’iki na. ‘Yan Dariku Huda muna son ka wa sa a daika karbi rokona. Na yi wannan kasidar ne a 2017, don haka zuwa yanzu ina da kasidu bugaggu solar kai guda goma, amma dai ban yi Album ba sai nan gaba.

Ko me ya fi burge ki a cikin harkar yabon Manzon Allah S A W?
Abin da ya fi burge ni shi ne yadda mu’amala ta ta ke kasancewa da mutane, ka kusanci kowa ba kyara ba kyama Sha’irai manya da kanana a hadu cikin shaukin hirar Ma’aiki da yadda a ke taron wayar da kan Sha’irai abin yana burgeni.
Ko akwai wasu matsaloli a cikin harkar yabo da ku ke yi?
Gaskiya akwai matsaloli jingim ya mace in tana harkar yabon Manzon Allah S A W ya shafi j zuwa Studio, dole to kuma har yau kai bai gama wayewa da zuwa Studio in ya mace ta je sai a rinka yi mata wani irin kallo na daban, sannan yawan fitar Sha’irai mata Majalisi ko wani taro, ka fita yau ka fita gobe ko a sati ka fita sau uku shi ma ‘yan unguwar ku suna yi maka wani irin kallo mai kama da ina take zuwa, sannan har yanzu ba a fiya yarda’ ya’ya mata suna da zurfin ilimin da za su fadi wata kalmar ga shugaba ba, sai a ga in dai ba rubutawa aka yi aka ba su ba, to ba za su iya ba to ba haka ba ne.

Amma ana ganin ku mata masu Yabon Annabi, auren ku yana da wahala.
A a babu wani wahala, ai mata masu Yabo ba su da wani buri da ya wuce habbaka sunnar Shugaba S A W. Farin cikin sa fa mu ke nema, gaskiya wannan tunanin bai yi daidai ba duk wanda ya ke yi to ya daina. Mata nawa ne suka fara suna ‘Yammata kuma suka ci gaba da yi bayan solar yi aure? Kuma ko ba su ci gaba ba suna zama su raya sunna tun da dama mai sunnar su ke so su dkbi’ antu da shi me ya rage, ai mu burin mu bai wuce yardar Allah da samun matsayi cikin fadar shugaba ba.

A yanzu wanne buri ki ke da shi a fagen yabon Manzon Allah?
Burkina na ga an sai ta hanya a yabo an gyara Kura kurai, musamman na furucin kalma.domun akwai furucin da bai kamata a yi wa Manzo da sugar furucin ba, akwai kalmomin da ba su cananta ba a saka su a sahun ba kamar kalma mai harshen Damo ba a saka ta a bege, tana bada ma’ana biyu kai mai yabo har zuciyar ka mai kyau ka dauka shi mai sauraro sai ya dauke ta a marar kyau, ka ga wannan tana hada jayayya. Allah ya shiga lamarin mu.

To daga karshe wanne kira ki ke da shi ko shawara?
A karshe ina son na yi amfani da wannan damar na Kara godewa Allah tare yiwa kungiyoyi na addu’a, Budatul Madihi fi Madahin Nabiy S A W. Wacce ta ke rajin kare janubin shugaba S A W. tare da tsaftace kalamai a yabon Annabi wanda ko yaushe shi ne aikin ta shi ta sa a gaba Allah ya ci gaba da yi wa shugabanni jagora, sai kuma Sha’iran Annabi ta jihar Kano Group WhatsApp wacce take fufutukar hada kan Sha’irai tare da wayar da kai a cikin yabo don ganin an gudu tare an tsira tare. Allah ya ci gaba da masu jagorancin ta Amen.
To Madalla mun gode.
Nima nagode.

- Advertisement -