Mata Da Rikon ‘Ya’yan Kishiya: Abinda Ka Shuka Shi Za Ka Girba

- Advertisement -

Mata Da Rikon ‘Ya’yan Kishiya: Abinda Ka Shuka Shi Za Ka Girba

Daga Sameerah Bello Shinco Gusau

“Dan kishiya rikon mai hakuri”, “kishiyar uwa ba uwa ba ce”, “Dan wani da uwar wani….”.Irin wadannan kirari daban-daban da Hausawa ke yi suke nu na irin alakar da ke tsakanin dan kishiya da kuma matar uba. Watakila wadannan kirarin suna cikin abubuwan da suke dasa kiyayya tsakanin bangarorin biyu, in da a lokuta da dama ba sa ganin amfanin juna. Hakan ya sa cin zarafin ‘ya’yan miji, ko kuma raina matar uban suka kasance wasu abubuwa da suka yi fice a yankunan da dama a kasar nan da ma Afirka baki daya, musamman a nan kasar Hausa.
Bincike ya nuna cewa mata da dama na kishi da ‘ya’yan mijinsu, kuma suna dora musu tsana da kiyayya harda cin zarafi. Shin hakan nada nasaba da irin zaman da suka yi da Mahaifiyar yaran ne ko kuma akwai wasu dalilai dabam? A dayan bangaren, ana samun ‘ya’yan miji da dama da ba sa ganin kishiyar Mahaifiyarsu da gashi. Wannan rubutun an yi sa ne bayan nazari da kuma la’akari da yawan afkuwar irin wanan matsalolin a al’umma.
Shin Su Waye ‘Ya’yan Kishiya?
I dan aka ce dan kishiya ana nufin dan miji wanda wata matar ta haifa, ko tana a gidan, ko kuma sakinta aka yi, ko kuma mutuwa ta rabata da ‘ya’yan ta. Da yawan mata ba su iya rike amanar da Allah ya basu ta ‘ya’yan abokan zaman su, in da zaka ji labarai kala-kala da ake samu na mata masu gallazawa ‘ya’yan kishiyoyin su.
Kadan Daga Irin Musgunawa Da Ake Yi Wa ‘Ya’yan Miji
A na samun matan da ke dukan ‘ya’yan miji ko basu musu laifin komai ba, wani lokacin har su ji musu rauni ko su sumar dasu. I dan abu yazo da Karin kwana ma sai ka ji labari marar dadi.
Ana samun matan da ke yiwa ‘ya’yan kishiyar su horo da ruwan sanyi ko ruwan zafi, ko wuta ko barkono, ko kuma yanka su da reza ko wani abu mai kaifi.
Akwai matar da take horon yaran da yunwa, ta hanyar hana su abinci ko kuma basu wanda ba zai wadace su ba.
Wasu matan kuma kullum sai solar samu laifin da za su cewa mijinsu yaran solar musu, dan kawai su hana su walwala da mahaifinsu.
Akan dorawa yara aiki mai yawa ko wanda yafi karfinsu, dan hana su zuwa makaranta ko samun walwala.
Akwai matan da basu kula da lafiyar ‘ya’yan kishiya ko da ba su da lafiya tana kallonsu suna kwance taki kai su asibiti, kuma taki sanar da Mahaifinsu.
Wasu matan dayawa ma kokarin kashe’ ya’yan kishiyoyin su suke yi, ta hanyoyi daban-daban kamar su guba da sauran su.
Wasu ma tallah suke dorawa yaran kawai dan su kashe musu rayuwa, su hana su neman ilimi.
Alamomin Yaran Da Ke Shan Wahala A Gun Kishiyar Uwa
Ana yawan tsangwamar su koda kuwa a gaban abokansu ne, ko saurayi idan budurwa ce.
Yaran basa son zama a gidan su, kullum suna makwabta; idan har ana barin su fita waje kenan. Idan ba sa fita waje zaka gansu koda yaushe a takure wuri daya, solar yi shiru ko suna ta fama da aiki.
kusan koda yaushe zaka gansu ba sutura mai kyau, ko kuma rashin tsabta.
Akwai muguwar mace da take kula da yaro a zahiri amma a boye kuwa gallaza masa take ba tare da an gane ba, irinsu zaka ga yaran na shakkarsu ko abu za su karba a hanun su.
Zaka samu yaran da tsananin tsoran matar uban su, ko sunanta aka kira jikinsu zai fara kakkarwa.
Zaka samu yaran da matukar son wani abu na ‘yan uwa ya tashi; kamar biki ko suna da zai sa suje su yi kwana biyu a wani gun dan suhuta.
A kan samu yaran solar saba da aikin wahala har solar kware a kan su.
Za ka ga wasu suna yawace-yawace a unguwa ba wanda ya damu, ko kuma yawon tallah.
Me Ke Kawo Hakan?
Rashin bincike daga mazan: da yawa basa sanin halin da yaran ke ciki, basu jan su a jiki, kuma basu damu dasu ba. Wannan na bawa matan damar mayar da yaran kamar bayi.
Rashin imani da tausayi: wasu matan tsabar rashin imani da tausayi ke saka su musgunawa yaran.
Kishin banzaHassada: da yawa kishin uwar yaran ko hassada saboda wata baiwa da yaran suke da, ko kuma irin son da Mahaifinsu ke musu shi ke saka su musgunawa yaran.
Matsalar yaran: Wasu yaran kuwa za ka samu basa jin magana, ko da mace tana iya kokarinta wajen kyautata masu sai solar saka an zage ta an ce dan ba ita bace ta haife su; irin haka sai ya saka ta fita harkar yaran ta barsu suna shan wuya.
Wasu mazan tsoron matan nasu ke saka matan abinda suka ga dama, tun da miji baya iya tsawata musu.
Bokaye: wasu matan wurin bin bokaye ake basu umurnin musgunawa yaran duk don son abun duniya.
Sharhi
Zargin cuzgunawa ‘ya’yan kishiyoyi dai ba bakon abu ba ne a Arewacin Najeriya. Galibi bakin kishi kan kare ne a kan yaran da basu ji ba basu gani ba; su tsinci kansu saboda kiyayyar kishiyoyin Mahaifiyarsu cikin tashin hankali da tsangwama, hadi da musgunawa. Halin da wasu kishiyoyi ke jefa ‘ya’yan mijinsu abun bakin ciki ne, domin za ka iske uban ma an mallake shi ba ya iya tabuka komai ko cewa uffan.
Ka ga Namiji ya tara mata marasa imani ko wacce yaran da ta haifa ta sani don haka ayi ta cin zalin juna, Idan ka yi magana a ce yaro ya gaggara don kawai an ga mahaifiyarsa ba ta gidan. Jahilci da kuma yadda duniya ta koma; kowa nasa ya sani ko tsakanin ‘yan uwa ciki daya babu soyayya sai kiyayya suna cikin dalilan faruwar hakan .Sai dai kuma wasu na ganin su ma yaran ba sa girmama matan mazajensu, abin da ke sa wasu zuciya ta debe su su aikata mummunan aiki a kansu.
Ina Mafita?
Mata ba su fiya la’akari da ce wa wannan dan mijinsu ne ba, abin da suke mayar da hankali a kai wannan yaron ko yarinya ‘yar kishiya ce. Sai dai duk wacce ke cutar da yara, akwai rashin tarbiya da imani ko matsalar kwakwalwa a tattare da ita. Daidaita kishi ko samar da mafita abu ne mai wahala, saboda masu imanin kadan ne duba da irin zamanin da ake ciki, duk da hakan akwai bukatar fadakarwa, nasihohi tare da ilimantarwa ko da ba za su dauka ba.
Ya ke ‘yar uwa, ki sani tsagwaran zalunci ne cutar dan da koda kece kika haife sa, ballantana wanda ba kece kika haife sa ba. Ki sani Allah (SWT) sai ya tambaye ki akan amanar da aka baki takula dashi. Idan kika mutu kina zaluntarsa bai yafe miki ba, tofa ba makawa sai kinje wuta; saboda Allah baya yafe hakkin wani. kuma ki sani tun a nan duniya sai kin ga sakayya domin shi dai ba zai ji kan kiba idan ya girma.Watakila ma Allah ya yi masa sakayya a kan ‘ya’yanki kema kifita ki auri wani wata tazo ta gallazawa naki ‘ya’yan.
Sannan kuma, sau tari irin wadannan yaran Allah yana basu nasibi a rayuwa; sai kiga solar girma Ubangiji ya albarkace su.Watakila ma lokacin ke kin zama abar tausayi kina neman taimako. Dan haka ‘yar uwa ki sani shi da amana ne Allah ya baki riko, zai kuma tambaye ki a kan amanar. Ku kuma iyaye maza, a matsayinku na uba, wajibi ne ku kare yancin ‘ya’yan ku, ku basu kariya da kula, dan kuma sai Ubangiji ya tambaye ku a kan amanar da ya baku.
Sannan gwamnati akwai bukatar ta sa ido ta bijiro da hanyoyi takaita irin wadannan mugayen halaye da ke cutar da yara. Akwai bukatar fadakarwa da ilimantarwa tun daga iyaye kafin aurar da yarinya. Sannan akwai bukatar sa ido kan yanayin zamantakewa a gidaje.

 

 

 

- Advertisement -