Masu Taba Mutuncin Annabi (SAW) Sun Shiga Uku

- Advertisement -


Jiya labari na gaskiya mai dadin ji ya karade duniya musamman duniyar Musulunci sakamakon wani bawan Allah da ya takarkare ya zabga wa shugaban Kasar Faransa Emmanuel Macron mari mai zafi a kuncinsa.
Na kalli video yadda aka mari kwarton bayahude Emmanuel Macron sai da ya fadi har kasa, mari ne irin wanda idan an zabga wa mutum sai ya ga wuta a idonsa

Kamar yadda BBC suka hada rahoton:-

Wani mutum ya gaura wa shugaban Faransa Emmanuel Macron mari a lokacin ziyarar da yake yi a kudu maso gabashin kasar.

A wani bidiyo da ya karade shafukan sada zumunta, an ga Mr Macron yana tafiya zuwa wajen wani shinge lokacin balaguron da ya yi zuwa Tain-l’Hermitage da ke wajen birnin Valence

Mutumin ya wanke Mr Macron da mari a fuska ne kafin jami’ai su yi hanzarin kai masa dauki, daga nan ne aka janye shugaban

Kafofin watsa labaran Faransa sun ce an kama mutum biyu bayan gaura wa shugaban kasar mari -BBC

Babu kaskancin da ya wuce wannan, har ma yafi daraja ace an harbeshi da bindiga ne ya mutu madadin ace yana shugaban kasa aka wankeshi da mari sai da ya fadi har kasa

Musulmin duniya muna kin Emmanuel Macron ne ba don komai ba sai don yana bayyana kiyayyarsa ga addinin Musulunci, tare da nuna goyon bayansa ga masu zagi da cin zarafin shugaban mu Annabi Muhammad (SAW)

Allah Ka karawa Annabi daraja.

- Advertisement -