Jinin Mujaddadin Musulunci Sheikh Bello Yabo Sokoto yayi zazzafan raddi ma wani Gwamna wanda ya sa aka rufe makarantun koyon Qur’ani a jiharsa
Kuma Sheikh Bello Yabo yayi raddi ga wawayen Musulmin da suke ganin cewa Daliban da suke koyon Qur’ani aka kamasu ai makarantar Darika ne, Bello Yabo yace wannan ba matsala bace ta kungiya ko Darika, Musulunci ake yaka.
Sheikh Bello Yabo yayi fata-fata da Gwamnan, kuma yayi roko ga jama’ar Musulmi su fara yiwa Gwamnan bakar addu’ah daga yanzu har zuwa shekarar 2023 in yaso ya kama kowa ya daure idan ya isa
Sheikh Bello Yabo yace yayi bakin ciki da ba’a yiwa Gwamna canjin gurin aiki, da yaso a yiwa Gwamnan canji zuwa Sokoto ya gani ko zai iya cin mutuncin Musulunci a kyaleshi a Sokoto kamar yadda yake yi a jihar sa
Sheikh Bello Yabo yace duk wanda yake fada da Qur’ani Yaa Allah Ka shaida ba ma sonsa kowayeshi, kuma mun kulla fada da shi har abada, bama bukatar tubansa, hakika ran maza ya baci.
Ku shiga wannan hyperlink domin Downloading Audion wannan karatu.
Allah Ka tsare mana Sheikh Bello Yabo Sokoto Amin.
432 total views, 3 views today