Masu hakar Mai da Gas sun yi asarar Naira Biliyan 320

0
60

Masu Dakon Mai Da Gas Na Shirin Tafka Asarar Naira Biliyan 320

Kungiyar masu kawo mai da gas a Nijeriya (NOGASA), sun bukaci kungiyar kwadugo (NLC) da kungiyar ‘yan kasuwa (TUC) da su janye aniyarsu ta gudanar da zanga- zanga a kan sabon kasrin farashin mai, yin hana zai sa su tafka asarar naira biliyan 320. A cikin bayanin da kungiyar suka fitar a Abuja, sun bayyana cewa, duk wani ragi na farashi da aka samu a yanzu sai sa su tafka asara mai yawan gaske.

Sun ce, “ragin farashin mai za sa sun tafka asara mai yawan gaske wacce ta kai ta sama da naira biliyan 320, bayan sun gama sayan mai daga hannun gwamnati a kan sabon farashi, kawai sai dai a tilasta musu rage farashin wanda suka saya a kan yadda kasuwa ta kaya.”

Masu Dakon Mai Da Gas Na Shirin Tafka Asarar Naira Biliyan 320

A cewarsu, rage farashin da aka yi a cikin watan Maris sakamakon cutar Korona, ya janyo musu cikas wajen harkokin kasuwancinsu a bangaren wurin sarin man. NOGASA mafi yawancin harkokin kasuwancinsu sun bushe saboda rage farashin mai a baya. kungiyar sun bayyana cewa, gwamnati ba ta tuntubarsu kafin ta rage farashin man. Sun kara da cewe, idan suka tafka asara lokacin da aka rage farashin man, gwamnati bayar musu da kudaden da suka tafka asara.
NOGASA sun ce, “gwamnati ba ta taba dawo mana da kudaden da muka yi asara, wannan ne ya talastawa wasu kamfanoni rufe harkokin kasuwancinsu da kuma korar ma’aikatansu daga aiki.

“Sakamakon irin durkushewar tattalin arziki da aka samu a Nijeriya, muna rokon kungiyoyin kwadugo da na ‘yan kasuwa da su duba bukatunmu wajen daukan mataki a kan karin kudin mai da na wutar lantarki wanda gwamnati ta yi.

“Mun tabbatar da cewa, daukan wannan mataki zai haddasa matsaloli mai yawa ga ma’aikata da kuma harkokin kasuwanci da yake bukatan magance matsalolin da ya fuskanta a baya.”

NOGASA sun damu matuka idan aka dauki wannan mataki wanda hakan zai kawo matsaloli ga harkokin kasuwanci da ma’aikata da kuma tattalin arzikin Nijeriya gaba daya. Sun kara da cewa, lallai farashin mai shi ke kawo nakasu ga harkokin kasuwancin mai, tun lokacin da cutar Korona ta barke muke fuskantar matsaloli a cikin harkokin kasuwanmu na karin haraji da kuma na farashin mai. A cewarsu, kasuwancin mai ya hade da matsaloli masu yawan lokacin cutar Korona, inda yake kokarin farfadowa. Sun ce, akwai bukatar a yaba wa kungiyar NOGASA wajen rige ma’aikatansu lokacin dokar hana zirga- zirga wanda har ta kai suka kara masu albashi duk da matsalolin tattalin arziki da aka cikin a wancen lokaci. Sun ce, a tuna irin jajircewar da kungiyar NOGASA suka yi lokacin dokar hana zirga- zirga wajen samar da man fetur a ko’ina a fadin kasar nan.

Karanta Har ila yau: Dauwamammen Zaman Lafiya A Xinjiang Ya Rusa Yunkurin Wasu ‘Yan Siyasar Amurka Na Amfani Da Batun Jihar Don Hana Ci Gaban Kasar Sin

“Mun tabbatar da cewa, kowani mambar kunyiyarmu sun tsare rayuwarsa da na ma’aikatanmu a lokacin wadannan watanni masu matukar wahala.

“Ba mu damu da rage farashin mai ba, amma muna kallon asarar da za mu iya tafkawa ne.
“Yana da kyau gwamnati ta bayar kasuwa ta kayyade farashin mai a Nijeriya. Bai kamata gwamnati ta dunga saka farashi ba musamman ma a wurin saro man.

“Gwamnati tana siyasantar da kasuwancin mai wajen saka farashi.
“Masu kawo mai sun zuba kudadensu ne domin su sami riba, amma suna shiga cikin mammunan yanayi a bangaren wajen tafka asara ga kuadaden da suka zuba jari.

“Mun yadda da maganan kungiyar kwadugo na cewa, ya kamata gwamnati ta gyara matatun mai kasar nan, ta kuma bar ‘yan kasuwa masu zaman kansu su gudanar da harkokin kasuwancin tace mai a Nijeriya, domin a samu gasa a cikin fannin man.

“Wannan shi zai samar da ayyukan yi ga ma’aikata da kuma saukaka farashin man. A duk lokacin da aka samu hanyoyi da yawa na tace mai, to za a samu dai-daituwar farashi sannan masu amfani da man za su amfana da lamarin da kuma samun tattalin arziki.”

What's On Your Mind?