Masifar ‘Yan Bindiga A Zamfara: Mun Cire Rai Da Yin Noma A Bana – Sarkin Noma Hassan  

0
118

Masifar ‘Yan Bindiga A Zamfara: Mun Cire Rai Da Yin Noma A Bana – Sarkin Noma Hassan  

Daga Abubakar Abba

Sarkin noman jihar Zamfara Alhaji Hassan kwazo ya bayyana cewa a bana solar cire rai da yin noma, sana’ar da suka gada iyaye da kakanni da ke rufe masu asiri tare da iyalansu, inda ya kara da cewa za a shafe shekaru goma kafin noma ya dawo daidai a jihar saboda.
Ya kara da cewa, noman gaske da aka sani a Zamfara ya gagara saboda hare-haren ƴan bindiga, inda ya kara da cewa, ba a yi noman da aka saba ba kusan shekara biyar zuwa shida.
A cewarsa, noma ya ja baya a Zamfara domin masu noma buhu 500 zuwa 1,000 gonakin solar gagare su zuwa, inda ya bayyana cewa, kafin noman ya dawo kila za a kai shekara 10 saboda duk manoman da suke noman na gaske solar watse.
Bugu da kari, Hukumomi da jami’an tsaron solar sha ikirarin cewa suna kokarin ganin an shawo kan matsalar da magance ta baki daya.
Har yanzu ana kai hare-hare da garkuwa da mutane duk da ikirarin gwamnatin Zamfara na yin sulhu da ‘ƴan fashi. Haka kuma manomi idan ya samu wurin shuka da abin da zai shuka babu abin da yake bukata fiye da tsaro da kwanciyar hankali.
Har ila yau, wani masani a fannin aikin noma Shua’aibu Yakubu ya bayyana cewa, a yayin da kakar diminar ke kara kunno kai, rahotannin solar bayyana cewa, manoma a kasar nan, musaman a arewacin kasar na ci gaba da shiga cikin firgici saboda yawan kai hare-haren ‘yan bingiga
Ya bayyana hakan ne a hirarsa da manema labarai a Abuja, inda ya kara da cewa, noma wajibi ne musamman ga mutanen karkara domin samun abinci da kuma samun kudaden shiga.
A cewarsa, harkar noma ta shiga wani mawuyacin hali sakamakon hare-haren ‘yan bindiga baya ga kalubale da annobar korona ta haddasa.
Ya koka da cewa, lamarin ya fi kamari musamman Zamfara da Katsina da yankin Birnin Gwari a Kaduna, inda hakan ya janyo dubban manoma suka yi watsi da sana’ar don tsira da rayukansu.
Masanin ya ci gaba da cewa, manoman solar warwatsu zuwa wasu manyan birane domin samun mafaka, duk da wasu solar koma kauyukansu saboda sulhun da gwamnati ta ce ta yi da ‘yan fashin daji da suka addabe su.
A cewarsa, akwai wadanda suka hakura da manyan gonakinsu a kauye kuma suke fargabar komawa gida, matakin da ke kara haifar da barazanar karancin abinci.
A wani rahoton da ta fitar a makon da ya gabata, hukumar samar da abinci ta duniya, WFP ta ce yunwa za ta tsananta tsakanin watan Yuni zuwa Agusta na wannan shekarar 2021.
A cewar rahoton, fiye da mutum miliyan 31 a yankin yammacin Afirka za su fuskanci barazanar yunwa sakamakon tsadar kayan abinci da kuma rikici da matsaloli na tsaro, inda rahoton ya yi nuni da cewa, lokaci ne da abinci zai yi wahala kafin zuwa lokacin girbi.
Har ila yau, rahoton ya bayyana cewa, rashin tabbatar da tsaro da kwanciyar hankali musamman a jihohin arewa maso yammacin Nijeriya ya sa har yanzu manoman da suka yi gudun hijira ba su koma ga gonakinsu ba, matakin da ya rage yawan abincin da ake samarwa a Nijeriya.
A cewar wani manomi Isah Musa da ya yi gudun hijira daga kauyen Jangeme zuwa garin Gusau a jihar Zamfara, inda ya ce kafin ya yi gudun hijira yana noma sosai wanda yake ci da iyalinsa har ya kai kasuwa ya sayar amma yanzu ba ya da halin yin noman, yana mai cewa, “barayi suka addabe mu muka gudu, yanzu ba wani aikin da nake sai leburanci.”

What's On Your Mind?