Masarautar Katsina Ta Dakatar Da Hakimin Kankara

0
125

Masarautar Katsina Ta Dakatar Da Hakimin Kankara

Masarautar Katsina sanar da dakatar da Sarkin Fawwa, Hakimin Kankara, Alhaji Yusuf Lawal, saboda zargin da ake masa na hulda da ‘yan fashi da suka addabi jihar.

Al’ummar yankin Kankara ne suka kai kukansu ga jami’an tsaro bisa wannan zargi da suke yi, domin samun mafita daga wannan barazana.

Bisa wannan ne masarautar  Katsina ta kafa kwamitin musamman domin gudanar da bincike a kan zarge-zargen da ake yi wa hakimin na Fawwa Alhaji Abubakar Yusuf.

Daga cikin zarge-zargen da ake masa akwai, hada baki da ‘yan sa kai wajen aikata wasu abubuwa da ba a fito fili an bayyana ba.

Alhaji Mamman Iso, Sarkin Yakin Katsina, kuma sakataren masarautar Katsina, ya shaida wa majiyarmu cewa, babu kanshin gaskiya a zargin da wasu ke yi na cewa ana yi wa hakimin bi ta da kulli ne.

Ya ce, idan kwamitin da aka kafa ya gama bincike zai gabatar da rahotonsa wanda za a aika wa gwamnati, sannan idan har an gano cewa bai aikata laifin komai ba za a bayar da umarnin mayar da shi kan kujerarsa.

 

What's On Your Mind?