Masarautar Gaya Ta Nada Sa’idu Madaki Sarkin Yakinta

0
24

Masautar Gaya da ke jihar Kano ta nada Alhaji Sa’idu Madaki Muhamnadi Gaya a matsayin sabon Sarkin Yakin Gaya.

Yayin da yak e tattaunawa da wakilinmu, sabon Sarkin yakin, ya bayyana cewa tun kafin a yi masarautar Gaya suke tare da Sarkin Gaya, Mai martaba Dokta Ibrahim Abdulkadir a matsayin da da uba.

Masarautar Gaya Ta Nada Sa’idu Madaki Sarkin Yakinta

Ya ce, yanzu da Allah ya kawo masarauta ta sami daukaka ya ga cancantarsa ya daga darajarsa daga Dagaci ya yi masa Hakimi, sannan kuma yanzu ya yi masa Sarkin yakin Gaya.

Gwamnati za tayi zama na musamman a kan maganar komawa aji bayan kamarin COVID-19

Daga nan ya yi nuni da cewa Sarkin Gaya a kullum maganarsa ta nasinace duk abin da zai fada yana danganta shi da kaddarar Ubangiji, don haka duk wani abu da ya so da shi ba ya tantama akansa, ba ya kuma shakku akan irin kaunar Sarki ke da shi na son ci gaban Gaya.

Sarkin Yakin na Gaya ya ce Allah ne ya dubi irin kaunar da Sarki ke wa masarautar Gaya ya ba shi wannan sarauta mai daraja ta daya a jihar Kano, sannan kuma ya zabo su a cikin dubban jama’a su taimaka masa wajen cika burinsa na taimaka wa al’ummar Gaya.

Ya ce, duk Wanda Sarki ya baiwa matsayin a fadarsa cancanta ce ta sa ya dauko shi ya ba shi, duk wanda ya baiwa za ka ga yana bada gudumuwa ga son ci gaban al’umma dama a rayuwarsa.

Alhaji Sa’idu Madaki Gaya ya ce a baya matsayin Sarkin yakin kamar Kwamandan yaki ne, amma yanzu tunda ba a yaki, zai zama aikinsa a masarautar Gaya shi ne kokarin gina ci gaban al’umma ta fannin kare martaba da muhibbar masarautar, duk Inda a ka ga abin da zai iya bata sunanta ko abin da zai kawo mata ci gaban shi ne abin da za a yi.

Sarkin Yakin na Gaya Alhaji Sa’idu Madaki Muhammad Gaya ya yi kira ga al’ummar Gaya su ba da hadin kai, domin hakan ne zai ba su ci gaban zaman lafiya da bunkasar tattalin arziki.

What's On Your Mind?