Masarautar Daura Ta Soke Hawan Karamar Sallah Saboda Tsaro

- Advertisement -

Masarautar Daura Ta Soke Hawan Karamar Sallah Saboda Tsaro

Daga Mahdi M. Muhammad, Abuja

 

Mai martaba Sarkin Daura, Dakta Umar Faruk Umar, ya bayyana cewa, ba za a gudanar da hawan bikin Sallah a masarautar ba a yayin bikin karamar Sallah mai zuwa dangane da kalubalen tsaro.

 

Ya kuma ba da umarnin cewa ba bu wani hakimi da zai ziyarce shi a ranar Sallah.

 

Wannan ya na kunshe ne a cikin wata takarda mai dauke da kwanan wata 6 ga Mayu, 2021, wanda aka gabatar wa hakiman masarautar tare da sa hannun Danejin Daura, Alhaji Abdulmimini Sahihu, wanda kuma menema labarai suka samu a ranar Lahadi.

 

Sanarwar ta ce, “Sarkin ya umarce ni da in sanar da ku cewa, saboda rashin tsaro a kasar, sace-sacen mutane don neman kudin fansa da sauran barazana ga zaman lafiyar kasa, ba bu hawan Sallah da aka saba ba za ta gudanar da wannan karamar sallar.”

 

“Maimakon haka, za a fi mayar da hankali ne kan yin addu’o’i na musamman a ranar Sallah da zarar an idar da Sallar Idi,” in ji sanarwar.

 

Sanarwar ta kara da cewa, sarkin ya umarci hakiman yankin da su gudanar da Sallar Idi tare da mutane a yankinsu tare da yin addu’o’i na musamman don dorewar zaman lafiya a kasar nan da nan bayan Sallar Idi.

 

“Ana wannan sanarwar ne don sanar da dukkan limamai su yi wa Shugaba Muhammadu Buhari (Bayajida II) da sauran shugabanni addu’ar kariya daga dukkan sharrin makiya masu kin son ci gaban kasar nan, da kwanciyar hankalin ta da kuma kasancewar ta daya,” in ji sanarwar.

- Advertisement -