Masar Ta Kulla Yarjejeniya Da Sin Domin Samar Da Riga-kafin Sinovac A Cikin Gida

0
62

Masar Ta Kulla Yarjejeniya Da Sin Domin Samar Da Riga-kafin Sinovac A Cikin Gida

Kamfanin nazarin halittu da samar da riga-kafi na VACSERA na kasar Masar, da kamfanin hada magunguna na Sinovac na kasar Sin, solar kulla yarjejeniya a ranar Laraba domin samar da riga-kafin cutar COVID-19 na kamfanin Sinovac a cikin kasar ta arewacin Afrika.
Bikin sanya hannu wanda ya samu halartar firaministan Masar Mostafa Madbouly, da ministan lafiyar kasar Hala Zayed, da jakadan kasar Sin a Masar Liao Liqiang, wanda daga bisani ya tattauna tare da jami’an kasar ta Masar, kana ya nuna yabo recreation da hadin gwiwar kasashen biyu a fannin yaki da annobar COVID-19.

Madbouly, ya bayyana farin cikinsa ga jakada Liao bisa ga muhimman tallafin da kasar Sin ke baiwa Masar domin dakile annobar. Ya ce yarjejeniyar tana da muhimmanci matuka kasancewar za ta baiwa kasar Masar damar samar da riga-kafin cutar COVID-19 a cikin gidanta.

Kasar Sin Jigon Ci Gaban Tattalin Arzikin Duniya

Firaministan ya ce, yana fatan za a aiwatar da yarjejeniyar domin fara samar da riga-kafin na kamfanin Sinovac a cikin gida nan ba da jimawa ba.
A nasa bangaren, Liao ya bayyana farin cikin kasar Sin recreation da muhimmiyar hadin gwiwar dake tsakaninta da kasar Masar da kuma kyakkyawar dangantakar dake tsakanin shugabannin kasashen biyu.

Sanyan hannu kan wannan yarjejeniyar wani sabon babi ne recreation da hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Masar a yaki da annobar, kuma zai taka muhimmiyar rawa wajen taimakawa Masar har ma da yankin gabas ta tsakiya da kuma Afrika wajen kawar da annobar, in ji jakadan na Sin. (Ahmad)

What's On Your Mind?