Masanin Nijeriya: JKS Na Da Tarihin Tsawon Shekaru 100

0
83

Masanin Nijeriya: JKS Na Da Tarihin Tsawon Shekaru 100

Daga CRI Hausa

An bayyana JKS a matsayin wadda ta jagoranci jama’ar kasar zuwa ga samun manyan nasarori a sassa daban daban.
Dakta Agaba Halidu na kwalejin nazarin ilmin siyasa da huldar kasa da kasa ta jami’ar Abujan Nijeriya ne ya bayyana haka, cikin wani sharhi da ya rubuta a Jaridar Blueprint ta Nijeriya, dangane da cika shekaru 100 da kafuwar jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin.

A cewar sharhin, cikin shekaru 100 da suka gabata, JKS ta kafa wata hanyar gurguzu mai halin musamman na kasar Sin, ta kuma gabatar wa kasashen duniya dabarunta a fannonin kara azama kan samun zaman lafiya da ci gaba da tafiyar da harkokin kasa da kasa, lamarin da ya shaida nagartacciyar kwarewar JKS wajen bada jagoranci da kuma fifikon da kasar Sin take da shi a fannin tsare-tsare.
Sharhin ya kara da cewa, a watan Yulin shekarar 1921, JKS ta kafu a birnin Shanghai da ke gabashin kasar Sin. Inda zuwa shekarar 1949, yawan ‘yan jam’iyyar ya karu zuwa miliyan four da dubu 500, a lokacin da jamhuriyar jama’ar kasar Sin ta kafu. Sa’an nan a shekarar 2019, yawan ‘yan jam’iyyar ya wuce miliyan 91.91 a duk fadin kasar, adadin da ya kai 6.6% bisa jimilar al’ummar kasar Sin. Ya ce JKS ta jagoranci raya tattalin arzikin kasar Sin da sauyawar salon zamantakewar al’ummar kasar. Kuma a karkashin shugabancinta ne al’ummar Sin suka samu manyan nasarori.

Har ila yau, JKS tana nacewa wajen bin hanyar gurguzu mai halin musamman na kasar Sin, lamarin da ya taimaka wa kasar zama ta biyu a duniya ta fuskar tattalin arziki, kana ta kasance kasuwar sayayya ta farko a duniya.

Ban da haka kuma, a karkashin jagorancin JKS ne aka fitar da daukacin al’ummar Sin daga kangin talauci, lamarin da ya kasance wani abin al’ajabi ga duniya. Baya haka kuma, JKS tana tsayawa tsayin daka kan bude kofa ga kasashen waje, da bin manufar cudanyar sassa daban daban, da gabatar da shawarar “Ziri daya da hanya daya”, a kokarin samun kyakkyawar makoma ga dukkan bil Adama. (Tasallah Yuan)

What's On Your Mind?