Martin Jacques: Yanayin Yaduwar COVID-19 A India Ya Zama Wani Babban Bala’i

- Advertisement -

Martin Jacques: Yanayin Yaduwar COVID-19 A India Ya Zama Wani Babban Bala’i

Daga CRI Hausa

Shaihun malami dan kasar Birtaniya Martin Jacques, ya bayyana yanayin yaduwar cutar COVID-19 a kasar India da wani mummunan bala’i, wanda ya dakile aniyar kasar ta zama tamkar kasar Sin a fannin shawo kan annobar.

Cikin wasu sakwannin Tiwita 2 da masanin ya wallafa a ranar three ga watan nan, ya ce wajibi ne firaministan India Narendra Modi, ya dauki alhakin yanayin da kasar ta fada ciki. A cewar sa, akwai rashin sauke nauyi, da nuna rashin kwarewa da rashin sani a bangaren mahukuntan kasar. Malamin ya kara da cewa, ga alama India ba ta shiryawa tunkarar cutar yadda ya kamata ba.

Ya ce matakan da gwamnatin firaminista Modi ta dauka sport da tunkarar wannan annoba, solar fi na tsohon shugaban Amurka Trump, da shugaban Brazil Jair Bolsonaro rauni. Kuma India za ta dandani mummunan tasirin wannan cuta cikin dogon lokaci.

Mr. Jacques, ya jinjinawa kasar Sin bisa kyawawan matakai da ta aiwatar, a fannin yaki da wannan annoba, yana mai cewa, tsohon shugaban Amurka Donald Trump, da shugaban Brazil Jair Bolsonaro, da firaministan Birtaniya Boris Johnson, da na India Narendra Modi, na sahun gaba cikin shugabannin duniya da suka gaza matuka, wajen daukar sahihan matakan dakile COVID-19 a kasashen su.
A daya sakon na Tiwita kuwa, Martin Jacques ya ce, shekara guda da ta gabata, wasu kasashen yamma solar rika furta kalamai marasa ma’ana kan kasar Sin, inda suka rika zargin kasar sport da yaduwar wannan annoba, amma sai ga ta Sin din ta yi rawar gani, wajen shawo kan annobar, sama da yadda abun yake a kasashe da dama. (Mai fassarawa: Saminu daga CRI Hausa)

- Advertisement -