Martanin ‘Yan Majalisun APC Ga ‘Yan Adawa: Tura Ta Kai Bango A Kan Buhari

- Advertisement -

Martanin ‘Yan Majalisun APC Ga ‘Yan Adawa: Tura Ta Kai Bango A Kan Buhari

Daga Khalid Idris Doya, Sunday Isuwa

Mambobin Majalisar Tarayya wadanda ‘ya’yan jam’iyyar APC ne solar bayyana cewa a halin yanzu tura ta kai bango a kan barazanar da takwarorinsu na jam’iyyar adawa ke yi wa Shugaban kasa Muhammadu Buhari, don haka ya dace su kwan da sanin cewa har yanzu dai Buharin ne ke da ragamar kasar nan a hannunsa.

Mambobin majalisar da suka kasance ‘ya’yan jam’iyyar adawa ne a ranar Talata suka bayyana cewar suna nan suna kan tattara irin ababen da Buhari ya yi na kama-karya kuma za su dauki kwararan matakan da suka dace a lokacin da ya kamata bisa bin doka da oda wanda kuma tuni wai solar fara tattaunawa da sauran abokansu na jam’iyya mai mulki.
Sai dai kuma mambobin APC a majalisar solar soki takwarorinsu na ‘yan adawa, suna masu cewa lamarin nan fa ya fara wuce gona da iri.

“Bayanin da mambobin PDP a majalisa suka yi ya wuce gona da iri bisa la’akari da kyakkyawar alakar aiki da ke tsakanin mambobin majalisa,” a cewar jagoran majalisa kuma shugaban kungiyar mambobin APC a majalisar dattawa, Yahaya Abubakar Abdullahi.

Da ya ke bayani bayan ganawar da suka yi a majalisar, Sanata Yahaya Abubakar ya bayyana cewar har zuwa yanzu dai Muhammadu Buhari shi ne ke jan ragamar gwamnatin kasar nan.

“A kowace demoradiyya, sukar lamarin da ya shafi kasa ba abu da ake lamunta ba.

“Duk da haka, a daidai lokacin da muke mutunta irin wannan ‘yancin; mun damu da bayanin da marasa rinjaye a majalisar nan suka fitar da ke cike da siyasa wanda ake tsammanin sune za su kasance masu kishi da son cigaban kasa,”Abdullahi ya fadi.

“Bugu da kari, batun rashin ganin shugabanmu da zargin rashin tabuka abun a zo a gani ga shugaban kasarmu babu gaskiya a ciki kuma tsantsan siyasa ce kawai. Shugaban kasa da shugabanin tsaro solar himmatu babu dare ko rana wajen ganin solar shawo kan matsalar tsaro a sassan kasar nan baki daya.

“Sannan, shugaban kasa a kowani lokaci yana magana da ‘yan Nijeriya musamman a duk lokacin da wani lamari na tsaro ya wakana, kuma yana bada tabbacin kokarinsu na ganin matsalar tsaro ta zama tarihi a kasar nan.

“Muna son mu tabbatar wa ‘yan Nijeriya shugaban Muhammadu Buhari har yanzu shine ke jan ragamar gwamnati kuma yana kokarin sauke nauyukan da suke kansa bisa dacewa da kishin kasar nan. abu ne a zahirance kuma a bayyane, gwamnatin tarayya a karkashin PDP ta gaza ta kuma ki daukan matakan da suka dace na shawo kan matsalolin tsaro a fadin kasar nan, amma lokacin da shugaban kasa a karkashin mulkin APC solar tashi tsaye wajen ganin an shawo kan matsalar tare da gyara duk wani kofar barna da gwamnatocin baya suka bari, gwamnatocin baya sune suka assasa matsalolin tsaron nan, amma muna tabbatarwa Buhari da gwamnatinsa na kokarin kawo karshen matsalar,” suka tabbatar.

- Advertisement -