Martani PDP A Kan Jawabin Shugaba Buhari

0
61

A martanin da ta mayar, Jam’iyyar (PDP) ta bayyana ikirarin tattalin arziki a cikin jawabin cikar shekarar Nijeriya 60 da samun ‘yancin kai da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gabatar a matsayin wata ” Babbar bulala ce ” da ya yi amfani da ita a hankulan‘ yan Nijeriya.

Buhari ya gabatar da jawabinsa a ranar bikin cikar Nijeriya shekaru 60 da samun ‘yancin kai a ranar Alhamis, inda ya ambaci kasar Saudiyya a matsayin daya daga cikin kasashen da farashin mai ya fi tsada sama da na Nijeriya.

Amma da yake mayar da martani, PDP a cikin wata sanarwa daga Sakataren Yada Labaranta na Kasa, Kola Ologbondiyan ya ce yunkurin Shugaba Buhari na ba da hujjar karin kudin mai da aka yi kwanan nan a Najeriya ta hanyar kwatanta shi da Naira 168 kan kowace lita a Saudiyya, ya kasance wani al’amari mai ban tsoro.

Jam’iyyar ta ce mafi karancin albashi a Saudi Arabia shi ne Naira 305,113 wato (Riyal 3000), wanda ya ninka sau goma akan Naira 30,000 mafi karancin albashinmu wanda akasari ba a aiwatar da shi” a Nijeriya.

Martani PDP A Kan Jawabin Shugaba Buhari

“Shin Mai Girma Shugaban Kasa bai san cewa, a matsakaita, mutumin da ke aiki a Saudiyya yana samun kusan 4,230SAR (Naira 430, 267) zuwa Riyal 16,700 daidai da (Naira 1,698,693) a kowane wata?

“Jam’iyyarmu na tuhumar Mai Girma Shugaban Kasa da ya duba littattafansa ko yaushe kafin yin irin wannan kwatankwacen, hatta farashin a Misira inda yawan kudin da ake samu a kowane wata ya kai Naira 222, 841 daidai da (9,200 EGP) a kan Naira 30,000 na matsakaicin albashinmu.

“Idan muka kwatanta farashinmu da wasu kasashe kamar su Ghana, Chadi da Nijar inda karfin saye da sayarwar ‘yan kasa ya fi haka, shin Shugaban kasa yana la’akari da kudin hayar gida, ilimi, kiwon lafiya da kuma matsakaicin dogaro da mai don rayuwa ta yau da kullum ta hanyar kyautatawa talakawa ‘yan kasa kamar yadda ake samu a Nijeriya?

“Idan maganganun da basu dace kamar yadda suka bayyana a cikin jawabin shugaban kasa ba, ya zamto kai tsaye kalaman nasa suna nuni ne kan yadda ake tsara manufofi a cikin gwamnatinsa, to bai kamata mutum ya yi mamakin dalilin da ya sa tattalin arzikinmu yake cikin rudani ba.

Resumption: Lecturers of Ojukwu Varsity Resume Duties Amid ASUU Strike

“Hakika, ya zama dole a bayyana cewa idan da gwamnatin Buhari ta nemi kwarewa da gaskiya don ci gaba da shirye-shiryen da gwamnatocin da suka gabata suka tsara a karkashin jam’iyyarmu don rayar da matatunmu da kuma samar da kashin bayan ci gaban yankinmu mai fa’ida, ta yadda farashin mai ba zai zama kari fiye da Naira 100 a kowace lita ba, ban da ribar da aka samu daga danyen mai.

“Don haka PDP ta bukaci Mai girma Shugaban kasa da ya samar da daidaito da kuma samar da abubuwa ta hanyar ba da damar tattaunawa mai fa’ida da zata samar da farashi mai sauki na man fetur da sauran kayayyaki masu mahimmanci a kasarmu.

“Jam’iyyar mu kuma ta nuna cewa Shugaba Buhari yana caccakar takensa na ” Larger Collectively’ lokacin da gwamnatin da yake jagoranta, ke gudanar da nuna bangaranci, rashin bin doka da oda, cin zarafin dan’adam, cin hanci da rashawa, rashin hakuri da siyasa, danniya da hana fadin albarkacin baki da kuma cin zarafi ga sabanin murya.

“Bugu da kari, ya kamata Shugaban kasa ya dukufa kan sake gina tattalin arzikinmu ta hanyar kawo karshen bashin da yake yi da kuma mai da hankali kan karfinmu na samar da abubuwan additional rayuwa maimakon kuka da rashin iyawarsa kan gazawarsa,” in ji PDP.

What's On Your Mind?