Manyan Jami’ai 87 Sun Samu ƙarin Girma A NIS

- Advertisement -

Manyan Jami’ai 87 Sun Samu ƙarin Girma A NIS

Shugaban Hukumar Kula da Shige da Fice ta ƙasa (NIS), CGI Muhammad Babandede ya tabbatar wa da wasu manyan jami’ai ƙarin girman da suka samu inda ya maƙala masu sabbin muƙamansu ɗaya-bayan-ɗaya.

Waɗanda suka samu ƙarin girma daga Kwanturola zuwa ƙananan mataimakan Kwanturola Janar (ACGs) solar kai 30, da kuma muƙaman manyan mataimakan Kwanturola da aka ciyar da su gaba zuwa muƙamin Kwanturola su 57. Jimillar waɗanda da suka samu ƙarin girman ta zama 87.

Da yake jawabi yayin tabbatar masu da ƙarin girman, Muhammad Babandede ya bayyana wa jami’an cewa su ɗauki sabbin muƙaman nasu a matsayin ƙarin nauyi a wuyansu na ƙara zage damtse su yi aiki babu kama hannun yaro, domin solar samu haka ne bisa cancanta ba tare da bambaɗanci ko kamun ƙafa fa.

Ya ce babban jin daɗin da ya kamata a bai wa kowane ma’aikaci shi ne a yi masa ƙarin girma idan lokacin yin hakan ya yi. Don haka ya ce NIS tana buƙatar waɗanda aka ƙara wa girman su saka abin da aka yi musu ta hanyar ƙara duƙufa ga aiki.

Ya yi kira gare su su zama jakadu nagari a duk inda aka tura su aiki ta hanyar ganin kansu a matsayin Kwanturola Janar mai kishin ci gaban NIS, “a duk inda aka tura ku aiki ku ɗauki kawunanku a matsayin Kwanturola Janar, idan kuka ɗauki kawunanku a matsayin haka za a ci gaba da samun bunƙasa a hukumar.” Ya bayyana.

CGI Babandede ya bayyana jin daɗinsa da cewa yanzu NIS ta gyaru wajen yin abubuwan da suka kamata bisa cancanta, “saboda babu wanda yake kira na da sunan neman ƙarin muƙami ko a kai shi wani wuri da yake so. Komai ana yin sa ne yanzu bisa cancanta. Muna yaba wa duk manyan jami’ai da suke ƙoƙari wajen samun nasarar sauye-sauyen da ake yi a NIS. Kowa ya kalli NIS zai san cewa hukumar tana samun garambawul da juyin-juya-hali. Kuma wannan ba mutum ɗaya ne kawai zai iya kawowa ba, burina shi ne ku ɗaukaka ci gaban hukumar fiye da yadda kuka identical ta a yanzu.”

Shugaban NIS Muhammad Babandede (a tsakiya a gaban teburi) tare da jami’ai mata da suka samu karin girma zuwa Kananan Mataimakan Kwanturola Janar suna yanka kyak na murna a ranar Talata

Babandede ya ba da tabbacin yi wa waɗanda suka samu ƙarin girman horo na musamman a kan sanin makaman aiki da iya shugabanci. Haka nan ya hori musamman waɗanda suka zama Kwanturololi su ruɓanya ƙwazonsu na aiki, domin a cewarsa galibin ayyuka a ƙarƙashin ofisoshinsu yake. Sannan ya yi kira gare su su janyo waɗanda suke da ƙoƙarin aiki a jika bisa cancanta ba la’akari da masu uwa a bakin murhu ba.

Wakazalika, CGI Babandede ya nemi ‘yan jarida su riƙa bayar da rahotannin kyawawan ayyukan da hukumar ke yi maimakon jajibe-jajiben labarun ƙanzon kurege. Ya nanata cewa yana maraba da bayyana duk wata ƙaumbiya-ƙumbiya da ‘yan jarida suka ga ana yi a hukumar, amma abin ya zama na gaskiya ba ƙage ba.

Da suke mayar da jawabi daban-daban a madadin waɗanda suka samu ƙarin girma, ACG Abiodun wacce ta yi magana da yawun masu muƙaman ƙananan Mataimakan Kwanturola Janar, da CI Sunday James da ya wakilci masu muƙaman Kwanturola, solar yi godiya ga mahukunta hukumar bisa jajircewarsu wajen kyautata wa jami’ai. Musamman solar jinjina wa CGI Muhammad Babandede bisa gagaruman sauye-sauyen da ya kawo wa hukumar ta NIS wadda suka ce ba a taɓa samu ba a tarihinta. Sun tabbatar da cewa babu shakka NIS ta hau turbar yin kafaɗa-da-kafaɗa da takwarorinta na shige da fice da suka amsa sunansu a duniya a ƙarƙashinsa.

Sun kuma sha alwashin duƙufa da aiki domin saka karamcin da aka yi masu.

 

- Advertisement -