Shagulgulan ‘Yancin Kai: Manyan Al’amurra Fiye Da 60 Game Da Nijeriya

0
49

Samun ‘yancin kan Nijeriya a ranar 1 ga watan Oktoba na shekarar 1960 ya kasance wani babban lamari na daya da za a fara kirgawa recreation da tarihin daidaituwar kasar a matsaya kasa mai cin gashin kanta, saboda bankwanan da ta yi da kangin ‘yan mulkin mallaka. Nijeriya ta samu ‘yancin kanta ne daga kasar Ingila, a inda Sir. Abubakar Tafawa Balewa, ya jagoranci gwamnatin hadin gwiwa ta farko a matsayin Firaminista, shi kuma Nnamdi Azikwe yana matsayin shugaban kasa.

Abu na biyu shi ne mika wa kasar ragamar tafiyar da harkokin tattalin arzikinta da Ingila ta yi a shekarar 1963, wanda ya alamta samun cikakken ‘yancin kai a kan dukkanin lamurranta.

A tsakanin 1962 zuwa 63, an gudanar da kidayar jama’a wanda ta tayar da jijiyoyin wuya  matuka a tsakanin sassa da kabilun kasar. A ranar 15 ga watan Janairu na shekarar 1966 kuma aka kashe Firaminista Sir Abubakar Tafawa Balewa, da Firmiyar Arewa Sir Ahmadu Sardaunan Sakkwato a wani juyin mulki da sojoji suka yi bisa jagorancin Chukwuma Kaduna Nzeogwu da Emmanuel Ifeajuna. Akalla manyan kasa 22 ne aka kashe a juyin mulkin.

A watan Yuli na shekarar 1966 ne kuma aka kashe shugaban mulkin soji, Johnson Aguiyi-Ironsi, a wani juyin mulkin na daukar fansa a karkashin jagorancin Laftana Kanar Yakubu Gowon.

A shekarar 1967, jihohin kudancin kasar nan guda uku photo voltaic shelanta ficewarsu daga tarayyar Nijeriya, abin da ya haifar da yakin basasan da aka zubar da jinni mai tarin yawa.

Sai dai a shekarar 1970, shugabannin Biyafara bisa jagorancin Odumegwu Ojukwu suka mika wuya, dukkanin yankunan na biyafara kuma suka sake komowa cikin tarayyar Nijeriya.

Manyan Al’amurra Fiye Da 60 Game Da Nijeriya

A shekarar 1975 Sojoji photo voltaic hambarar da gwamnatin Janar Gowon, Gowon ya sami nasarar tserewa zuwa kasar Ingila, a inda Murtala Ramat Mohammed, ya maye gurbinsa sa a matsayin shugaban gwamnatin mulkin Soja, wanda kuma tun daga hawansa ne ya fara kokarin mayar da hedikwatar kasar nan zuwa babban birnin tarayya Abuja.

A shekarar 1976 ne aka kashe Murtala Muhammad, a wani juyin mulkin da bai yi nasara ba, a inda kuma mataimakinsa, Laftana Janar Olusegun Obasanjo, yam aye makwafinsa a matsayin shugaban gwamnatin mulkin Soja, wanda kuma shi ne ya taimaka wajen kaddamar da tsarin mulkin shugaban kasa samfurin na kassar Amurka.

A shekarar 1979, an gudanar da babban zaben kasar nan a jamhuriya ta biyu wanda ya yi sanadiyar zuwan Shugaba Shehu Shagari a matsayin shugaban gwamnatin farar hula mai cikakken iko.

A shekarar 1983 ne gwamnatin kasar nan ta wancan lokacin ta kori ‘yan kasashen waje, yawanci ‘yan kasar Ghana daga cikin kasar nan, gwamnatin ta bayar da hujjar cewa bakin photo voltaic yi kakagida photo voltaic kuma tsawaita zamansu a nan kasar, sannan duk photo voltaic kwace wasu ayyukan da ‘yan Nijeriya ne ya kamata a ce suna gudanar da su. Duk da kasashen ketare masu yawa photo voltaic yi suka a kan wannan abin da gwamnatin kasar nan ta yi a wancan lokacin na korar bakin wajen, amma dai ‘yan kasa photo voltaic yi murna da hakan.

A tsakanin watan Agusta da Satumba na shekarar 1983 ne aka sake zaban Shugaba Shagari a karo na biyu a matsayin shugaban kasan nan mai cikakken iko, duk da kokawan da jam’iyyun hamayya suka yi da cewa an tafka magudi a cikin zaben.

Sai dai a cikin watan Disamba na shekarar 1983, Manjo Janar Muhammadu Buhari (shugaba mai ci a yanzu) ya kwaci mulki daga hannun gwamnatin ta farar hula, a cikin wani juyin mulkin da ba a zubar da jini a cikinsa ba. Wani muhimmin abu da ‘Yan Nijeriya ba za su taba mantawa da shi ba a zamanin mulkin soja na Buhari shi ne yaki da rashin da’a, da fatattakar ‘yan siyasa da aka zarga da cin hanci da rashawa.

A watan Agusta na shekarar 1985 kuma sai Janar Ibrahim Badamasi Babangida, ya katse wa gwamnatin mulkin Soja ta Buhari hanzari, inda ya kifar da ita a wani juyin mulkin da ba a zubar da jini a cikinsa ba, wanda kuma daga lokacin ne kai tsaye ya fara shirin mayar da mulki a hannun farar hula.

A watan Yuni na shekarar 1993, Sojoji a karkashin gwamnatin mulkin soja ta Babangida photo voltaic soke zaben da aka gudanar a lokacin da sakamakon zaben na farko ya fara nuna alamun cewa Marigayi Cif Moshood Abiola ne yake kan gaba wajen lashe zaben.

Mabambantan Ra’ayoyin Wasu ‘Yan Nijeriya Kan Jawabin Shugaba Buhari

A watan Agusta na shekarar 1993 ne mulki ya koma a hannun gwamnatin rikon kwarya a karkashin Cif Earnest Shonekan.

A watan Nuwamba na shekarar 1993 din ne Janar Sani Abacha ya kwace mulki daga hannun gwamnatin ta rikon kwarya.

A watan Yuni na shekarar 1994 ne gwamnatin Abacha ta kama Abiola, a bayan da ya shelanta kansa a matsayin shugaban kasa.

A shekarar 1995 – Ken Saro-Wiwa, wani marubuci kuma mai rajin kare muhallin da aikin hakar danyan mai yake lalatawa a yankinsu na Ogoni, aka zartar masa da hukuncin kisa a wata shari’ar gaggawa da aka yi masa. Wanda a sakamakon hakan ne kungiyar kasashen Turai suka kakaba wa kasar nan wasu takunkumi har ya zuwa shekarar 1998, hakanan su ma kungiyoyin kasashen renon Ingila suka kori Nijeriya daga cikin kungiyar har ya zuwa shekarar ta 1998.

Shugaban gwamnatin ta mulkin Soja a wancan lokacin, Janar Abacha ya mutu a watan Yuli na shekarar 1998, a inda kuma Manjo Janar Abdussalami Abubakar, ya maye makwafinsa a matsayin shugaban gwamnatin mulkin Soja.

A watan Yuli na shekarar ta 1998 ne Cif Abiola ya mutu a lokacin da yake tsare a gidan Yari.

An gabatar da manyan zabukan kasa a shekarar 1999, wanda ya kai ga rantsar da Olusegun Obasanjo, a matsayin shugaban gwamnatin farar hula.

A shekarar 2000 ce wasu Jihohin Arewa suka rungumi tsarin shari’ar Musulunci, wanda hakan ya tayar da jijiyar wuya musamman daga al’ummar Kiristoci wanda hakan ya kai ga samun wasu ‘yan rigingimun da daruruwan mutane suka mutu a cikinsa a tsakanin Musulami da Kiristoci.

A shekarar 2001 ne aka sami rikicin kabilancin a Jihar Benuwe da ke gabas ta tsakiyar kasar nan wanda ya raba dubban mutane da gidajen su.

A watan Oktoba na wannan shekarar, aka tura Sojoji domin su lafar da rikicin, a inda su Sojojin suka kashe sama da mutane 200 wadanda basa rike da makami a hannun su, wanda ake jin sojojin photo voltaic yi hakan ne a matsayin martani a bisa sacewa da kuma kashe wasu jami’an Sojojin guda 19.

A watan Oktoba na shekarar 2001, Shugaban kasan Nijeriya, Olusegun Obasanjo da na kasar Afrika ta kudu Mbeki, da shugaban kasan Algeriya, Bouteflika suka kaddamar da shirin hadin gwiwar nan na bunkasa Nahiyar Afrika (NEPAD), a bisa manufar bunkasa nahiyar da inganta tsarin shugabanninta gami da kokarin kawo karshen fadace-fadacen da ake yi a wasu sassan nahiyar ta Afrika, har da janyo ra’ayin masu zuba jari zuwa nahiyar da kuma dauke shingen nan na kasuwanci da ke a tsakanin kasashen nahiyar ta Afrika.

A shekarar watan Fabrairu na shekarar 2002 ne aka sami wani rikicin kabilanci a Legas, a inda aka kashe akalla mutane 200 a tsakanin Yarbawa da al’ummar Musulmi mafiya yawa Hausawa daga Arewacin kasar.

A watan Nuwamba na shekarar 2002 ne sama da mutane 200 suka rasa rayukansu cikin kwanaki hudu a wani tashin hankalin da ya faro a sanadiyar bikin zaben Sarauniyar kyau ta Duniya da aka shirya gabatarwa a garin Kaduna, a watan Disamba na wannan shekarar, wanda hakan ya sanya aka mayar da gasar zuwa kasar Ingila.

A ranar 12 ga watan Afrilu ne na shekarar 2003 aka gudanar da zaben farko na ‘yan majalisu tun bayan fitowa daga karkashin mulkin Soja a shekarar 1999, an samu jinkiri matuka a wajen fara zaben, an kuma koka da tafka magudin zabe a akwatunan zaben, wanda a karshe Jam’iyyar da Obasanjo ke yi wa takara ta PDP ta sami rinjaye a zaben na ‘yan majalisun na tarayya.

A ranar 19 ga watan Afrilu na shekarar ta 2003 aka sake zaban Olusegun Obasanjo a matsayin shugaban kasa, a inda ya sami kuri’a sama da kashe 60 cikin 100 a zaben wanda jam’iyyun hamayya suka nuna rashin amincewarsu da zaben, haka nan masu sanya ido a kan zaben daga kasashen Turai duk photo voltaic shaida tafka magudi a cikin zaben.

A watan Yuli na shekarar ta 2003 ne aka janye yajin aikin da ma’aikata suka shafe kwanaki Tara suna yi a bayan da gwamnati ta amince da ta rage farashin litar man fetur da ta yi wa kari ba da jimawa ba a lokacin.

A watan Agusta na shekarar ta 2003 kuma, rikicin kabilanci a garin Warri da ke yankin Neja Delta ya yi sanadiyyar mutuwar kimanin mutane 100 da jikkata akalla mutane 1,000.

A watan Satumba na shekarar 2003, Nijeriya ta kaddamar da tauraron dan adam dinta na farko a sararin samaniya wanda wani makamin roket na kasar Rasha ya harba shi.

A Janairun 2004, Majalisar Dinkin Duniya ta shiga tsakanin wajen kaddamar da tattaunawa a tsakanin Nijeriya da kasar Kamaru a kan yankin kan iyakar nan da ake yin jayayya a kansa na Bakassi. A inda dukkanin kasahen biyu suka amince da su sanya jami’an tsaro na hadin gwiwa a tsakanin su domin kula da yankin.

A watan Mayu na shekarar ta 2004 ne aka kafa dokar ta-baci a tsakiyar Jihar Filato, a bayan da aka kashe al’umma galibi Musulmi sama da 200 a garin Yalwan Shendam, a wani farmaki da ‘yan tsageran da ake zargin Kiristoci  ne suka kai masu da sunan mayar da martani a kan harin da matasan Musulmai suka kaddamar a kan mutanensu a Kano.

A watan Agusta zuwa Satumba na shekarar 2004 ne aka sami wani kazamin rikici a tsakanin kungiyoyin da ba sa ga maciji da juna a garin Fatakwal, wanda ya yi tsanin da sai da aka tura dakarun Soji domin su lafar da shi. Kungiyoyin kare hakkin dan adam na Amnesty Worldwide photo voltaic ce an kashe akalla mutane 500 a rikicin, amma hukumomin gwamnati photo voltaic ce mutane 20 ne kacal aka kashe a rikicin.

A watan Yuli ne na shekarar 2005, Klub din masu kudin nan na kasar Faransa ya amince da ya yafe wa da Nijeriya kashi biyu bisa uku na bashin dalar Amurka biliyan 30 da yake bin kasar nan.

A watan Janairu ne ‘yan tsagera a yankin Neja Delta suka kai wa bututun mai da sauran kadarorin kamfanin mai na kasa hari, suka kuma sace wasu ma’aikatan man ‘yan kasashen waje, ‘Yan tsageran photo voltaic nemi da a ba su karin iko ne a kan arzikin danyan man da ake hakowa daga yankin na su.

A watan Fabrairu na shekarar 2006 har ila yau, wani rikicin addini ya lakume rayukan sama da mutane 100 a wasu garuruwan Musulmai na Arewacin kasar nan da kuma garin Onitsha, da ke kudancin kasar nan.

A watan Afrilu na shekarar 2006 a sakamkon samun kudaden mai, Nijeriya ta zama kasar Afrika ta farko da ta iya biyan dukkanin basukan da Kulab din masu kudin nan na kasar Faransa yake binta.

A watan Mayu na shekarar 2006, Majalisar Dattawa ta ki amincewa da canje-canjen nan da aka so kawo wa a cikin tsarin mulkin kasar nan, wanda zai iya bai wa Shugaban kasa na lokacin Olusegun Obasanjo damar tazarce a karo na uku a shekarar 2007.

Badakalar Bakassi

A watan Agusta na shekarar 2006, Nijeriya ta hannata yankin nan na Bakassi da ake rikici a kansa ga makwabciyarta kasar Kamaru, a karkashin wani shiri na kotun Duniya.

A watan Oktoba na shekarar 2006 kuma shugaban majalisar al’ummar Musulmi, Sultan Muhammadu Maccido ya rasa ransa a wani hatsarin Jirgin sama wanda shi ne annnoba ta uku mafi tsanani da kasar nan ta fuskanta a hadarin Jiragen sama a cikin shekara guda.

A watan Afrilu na shekarar 2007 kuma aka shelanta Umaru Musa ‘Yar’aduwa, na Jam’iyyar PDP a matsayin wanda ya lashe zaben Shugaban kasa na wannan shekarar.

A watan Satumba na shekarar 2007, kungiyoyin tsagerun nan na yankin Neja Delta (MEND), suka yi barazanar kawo karshen dakatar da bude wuta a yankin nasu, suka kuma yi alkawarin kaddamar da wasu sabbin hare-haren a kan dukkanin kadarorin mai a yankin da kuma sace ma’aikatan man yan kasashen waje.

A watan Nuwamba na shekarar 2007 din ne wasu da ake kyautata zaton tsagerun ne suka kashe wasu Sojojin kasar Kamaru guda 21 a yankin na Bakassi.

A wannan shekarar ce, Majalisar Dattawan Nijeriya ta yi fatali da yarjejeniyar da aka cimma na hannanta yankin na Bakassi ga kasar Kamaru.

A watan Janairu na shekarar 2008 albarka ta karu, inda aka siyar da gangar danyan mai a kan dalar Amurka100 a karon farko, a lokacin da rikici a yawancin kasashen da suke fitar da danyan man yake ta kara habaka, kamar kasashen Nijeriya da Algeriya, wanda hakan ya sanya farashin danyan man ya haura sama.

A watan Fabrairu 2008, kotun sauraron kararrakin zabe ta tabattar da sahihancin zaben Umaru ‘Yar’aduwa a matsayin shugaban kasa a sakamakon kalubalantar zaben nashi da abokanan hamayyarsa karkashin shugaba mai ci Muhammadu Buhari suka yi da neman a soke zaben a kan hujjar an tafka magudi a zaben da suke zargin an yi.

A watan Afrilu na shekarar 2008 ne aka tuhumi wasu tsoffin Ministocin lafiya  biyu da kuma diyar Shugaban kasa Olusegun Obasanjo, tare da wasu manyan jami’an lafiya 12 da laifin yin almunbazarranci da dukiyar al’umma da yawanta ta kai jimillar Naira miliyan 470.

A shekarar ce aka rage yawan danyan man da ake kakowa da rabinsa a sakamakon zanga-zanga da hare-haren da ake kai wa a kan bututun man wanda ‘yan tsagera suke ta faman yi. Matsalolin da aka fuskanta a Nijeriya a lokacin ya sanya farashin man ya daidaita a kasuwannin Duniya.

A watan Agusta na shekarar 2008, a sakamakon yarjejeniyar da aka kulla a watan maris na wannan shekarar, a karshe dai Nijeriya ta hannata yankin na Bakassi ga kasar ta Kamaru.

Faduwar farashin danyan mai

A watan Oktoba na shekarar 2008, gwamnati ta shelanta rage yawan kasafin kudinta a sakamakon faduwar farashin danyan man fetur.

A watan Nuwamba 2008, ne aka kashe akalla mutane 200 a wani fadan da ya barke a tsakanin Muslmai da Kiristoci a garin Jos.

A watan Yuli na shekarar 2009, daruruwan mutane photo voltaic rasa rayukansu a sakamakon wani mummunan harin da ‘yan kungiyar Boko Haram suka fara kaddamarwa. Jami’an tsaro photo voltaic sami nasarar kashe shugaban kungiyar tasu a lokacin da suka farmaki babban sansaninsu.

A shekarar ce kuma gwamnati ta saki jagoran ‘yan tsageran nan na MEND, Henry Okah, bayan da ya karbi tayin da gwamnati ta yi masa na yafiya.

A watan Nuwamba na shekarar 2009, Shugaban kasa Umar ‘Yar’aduwa ya yi tafiya zuwa kasar Saudiyya domin neman magani. Tsawon zaman da ya yi a can din ne ya haifar da rikicin tsarin mulki wanda har wasu suka rika yin kiransa da ya sauka daga mulkin kasa.

A watan Janairu na shekarar 2010, an kashe akalla mutane 149 a wani fadan da ya sake barkewa a tsakanin Musulmai da Kiristoci a garin Jos.

A watan Mayu na shekarar 2010, kuma Allah ya yi wa Shugaban Kasa Umar ‘Yar’aduwa rasuwa, bayan doguwar jinyar da ya yi, inda kuma mataimkainsa wanda a lokacin yake a matsayin mukaddashin Shugaban kasa, Goodluck Jonathan ya maye makwafinsa.

A watan Oktoba na shekarar 2010, Nijeriya ta yi bukin ranar samun ‘yancin kai na musamman tare da wani mummunan tashin bama-bamai a kusa da wajen da ake yin bukin a Abuja.

A watan Maris na shekarar 2011, Goodluck Jonathan ya sake lashe zaben shugaban kasa.

A watan Agusta na shekarar 2011 ne aka sami wani harin kunar bakin wake a ofishin Majalisar Dinkin Duniya da ke Abuja, wanda ake kyautata zaton ‘yan kungiyar Boko Haram ne suka kai.

A watan Mayun 2013 kuma, Gwamnatin tarayya ta shelanta kafa dokar ta baci a Jihohin arewa maso gabas uku na Borno, Yobe da Adamawa.

A watan Afrilu na shekarar 2014, ‘yan kungiyar Boko Haram photo voltaic sace sama da ‘yan mata 200 daga wata makarantar Sakandare ta ‘yan mata da ke Chibok a Jihar Borno.

A watan Agusta na shekarar 2014, ‘yan kungiyar ta Boko Haram suka shelanta kafa kasarsu yankin Arewa maso gabashin kasar nan, shelar da gwamnati ta musanta da cewa batatta ce.

A watan Fabrairu na shekarar 2015 ne dakarun Sojin Nijeriya suka sake kama garin Gwoza, wanda a baya yake a hannun ‘yan kungiyar ta Boko Haram, wanda kuma suka rika a matsayin babbar hedikwatarsu.

A watan Maris na shekarar 2015 ne a karon farko, shugaba Buhari da ke bangaren adawa ya ci zaben shugaban kasa a inda ya zama shugaba na farko da ya sami nasara a kan shugaban da yake a kan kujerar mulki a tarihin Nijeriya.

A ranar 16 ga watan Maris na shekarar 2016 Karamin Minista a ma’aikatar kwadago da samar da ayyukan yi James Ocholi ya rasa ransa a wani mummunan hadarin mota a kan hanyar Abuja zuwa Kaduna.

A watan Yuni na shekarar 2016 ne kasar nan ta fada cikin komadar tattalin arziki.

A watan Oktoba na shekarar 2016, gwamnatin tarayya ta iya fanso yara ‘yan matan makarantar Chibok su 21 daga hannun ‘yan kungiyar Boko Haram kafin daga bisani a sake sakin wasu 82 a watan Mayun 2017.

Jirgin Helikwaftan da Mataimakin shugaban kasa Farfesa Osinbajo yake a cikinsa ya yi wani dan karamin hatsari a Jihar Kogi.

A shekarar 2019 ne kuma aka gudanar da babban zaben shugaban kasa a tsakanin ranakun 23 ga watan Fabrairu zuwa 16 ga watan Maris na shekarar 2019 wanda ya kai shugaba Buhari sake lashe zaben a wa’adi na biyu.

A ranar 5 ga watan Disamba ne na shekarar ta 2019  ce wata kotu ta sami tsohon Gwamnan Jihar Abiya, Orji kalu da laifin almunbazaranci da dukiyar al’umma a inda ta daure shi a gidan yari.

A ranar 21 ga watan Agusta, na shekarar ta 2019 kuma shugaban kasa muhammadu Buhari ya yi umurni da kulle kan iyakokin kasar nan domin kare tattalin arzikin kasa daga tabarbarewa.

Bikin cikar Nijeriya shekara 60 da samun ‘yancin kai dai zai ci gaba da gudana har na tsawon shekara guda kamar yadda gwamnatin tarayya ta shelanta.

What's On Your Mind?