Manoman Nijeriya Za Su Yi Tsimin Naira Biliyan 9 Wajen Amfani Da Irin TELA Maize —IAR

0
75

Manoman Nijeriya Za Su Yi Tsimin Naira Biliyan 9 Wajen Amfani Da Irin TELA Maize —IAR

Cibiyar binciken aikin gona IAR da ke Jami’ar Ahmadu Bello Zaria ta bayyana cewa, sabon irin masara da cibiyar da kirkiro mai suna TELA Maize zai taimaka wajen tsimin fiye da Naira biliyan 9 a duk shekara da zaran manoma solar fara amfani da shi.
An dai samar da ‘TELA maize’ ne ta yadda za ta iya jure farmakin kwari da kuma fari, ma’ana za ta iya jure karancin ruwan sama.

Shugaban hukumar IAR, Farfesa, Mohammad Ishyaku, ya sanar da haka a yayin girbin masara a gonar gwaji da aka yi a Zaria, ya kuma ce, an kiyasata manoma za su yi tsimin fiye da Naira biliyan three daga kudaden sayen magunguna feshin kwari a Hecta 500 na filin noma yayin da kuma za a yi tsimin Naira biliyan 6 daga barnar da fari kan iya yi wa gonakin.

Cibiyar Riyadulsalihin Ta Ba Maruyu 2000 Tallafin Abincin Azumi Da Kayan Salla A Funtuwa

Shugaban cibiyar wanda ya samu wakilcin, mataimakinsa, Farfesa Bitrus Tarfa, ya kuma ce, IAR ce akan gaba wajen gudanar da bincike tare da kirkiro sabbin hanyoyin sauwaka wa manoma hanyoyin gudanar da harkokin noma a kasar nan.

Ya kuma kara da cewa, cibiyar ta samu gaggarumin nasarar wajen samar da auduga da ke iya jure farmakin kwari, musamman kwarin nan mai suna ‘Ballworm’ ana kuma samun karin yabanya na fiye da kashi 80, haka kuma cibiyar ta kirkiro da irin wake da aka sa wa suna SAMPEA 20T wanda shi ma yana jure farmakin kwari, ana kuma samun karin yabanya daga shuka irin.

A jawabinsa, Farfesa Abdukkahi Mustapha, shugaban hukuma ‘Nationwide Biotechnology Debelopment Company (NABDA)’ ya ce fasahar ‘Biotechnology’ ita ce babbar hanyar samar da cigaba mai dorewa tare da maganin dukkan matsalolin da albarkatun gona ke fuskanta a wannan zamanin.

Ya kuma tabbatar da cewa, NABDA za ta cigaba da aiki tare da IAR da kuma saura cibiyoyin binciken harkar gona don ta haka ne za a bayar da gudumwar da ya kamata ga tattalh arzikin kasar nan.

Da yake tsokaci a wurin, Farfesa Rabiu Adamu, shugaban kwamitin kula da bincike akan ‘TELA Maize’ ya ce, irin zai iya samar da fiye da kashi 80 in har aka kula da yadda aka shuka shi yadda ya kamata.

Ya kuma bayyana cewa, TELA Maize ta yi maganin abubuwa 2 da harkar masara ke fuskanta “Muna wannan gwajin ne a karo na three, mun fara a lokacin rani, mun kuma gudanar da na 2 a watan Yuni 2020 na three kuma a watan Nuwamba 2020 zuwa watan Afrilu 2021,” inji shi

What's On Your Mind?