Manoma 20,000 Za Su Amfana Bashin Noman Rani Na Masara Da Kungiyar MAGPAMAN Za Ta Samar A Jihar Katsina

0
139

Manoma 20,000 Za Su Amfana Bashin Noman Rani Na Masara Da Kungiyar MAGPAMAN Za Ta Samar A Jihar Katsina

Sama da manoma 20,000 za su amfana da bashin noman rani na Masara da kungiyar noman Masara da sarrafata MAGPAMAN ta kasa reshen jihar Katsina za ta  ba manoman jihar.

Wannan tabbacin ya fito ne daga bakin shugaban na jihar Katsina Injiniya Magaji Ibrahim Dantankari a lokacin da yake hira da manema labarai a ofishin kungiyar dake Funtuwa.

Alhaji Magaji Dantankari ya cigaba da cewar kungiyarsu ta yi nisa wajen karbar sunayen masu son kungiyar ta basu bashin noman rani ya cekungiyar su ta MAGPAMAN ta ciri tuta ba kamar sauran kungiyoyin ba domin kungiyarsu tana da ofis a kowacce karamar hukuma 34 a fadin jihar Katsina domin kusantar manoman kungiyar.

Shugaban kungiyar na jihar Alhaji Magaji wanda ake kira da Bileja ya cetuni aka ware wasu kudade domin biyan diyya ga manoman da suka samu ambaliyar ruwa a gonakin su na Masara ya cetuni suka fara karbar takardun koke ga manoman da suka sami ambaliyar ruwan amman dole akwai hanyoyin da kungiyar za ta  bi domin tabbatar da koken, idan suka kama wani mambansu da bada rahoton karya za’a hukuntasu ya cekamfanin inshora da bankin Eco Monetary establishment sune za su  tantance inda aka sami ambaliyar ruwan kuma yana kira ga manoma da suka amfana da shirin bashin noman masarar da zarar lokaci ya yi su daure su biya bashin domin photo voltaic san bashin aka basu ya ceza su  fara karbar kayan da zarar an fara aikin gona kuma abisa farashi mai kyau, Alhaji Magaji ya cea karshen watan 11 watau watan nuwamba zuwa farkon watan 12 disamba zuwa karshen shi za su  gama karbar kayan, duk manomin da ya kai farkon watan 1 watau janairu na shekarar mai zuwa laifi ne sosai kuma bankin da ya baya ya amince ya bada bashin bankin Eco Monetary establishment zai chaji manomin wasu kudi na musamman ganin manomin ya karya yarjejeniyar da akayi dashi tun farko.

Ambaliyar Ruwa Ta Kashe Mutum 54 A Kano

Injiniya Dantankari ya cebabu shakka daminar bana tayi albarka kuma tayi kyau domin zaa sami amfanin gona mai yawa musamman masara, don haka yana kira ga manoman dasu kara amfani da bashin noman rani, ya cetuni kungiyar su za ta  gina kananan wuraren samar da ruwa a lokacin noman rani a dukkan kananan hukumomi 34 dake fadin jihar.

Alhaji Magaji ya ce, kwanannan kungiyar za ta  fara rangadin kananan hukumoni don duba yadda za su  gudanar da kananan wuraren samar da ruwa don yin noman rani na masara a yankunasu, ya cedukkan manoman dasu kasamu matsalar ambaliyar ruwan za su  sami tabbacin makwaftan manoman cewar manomin daya nuna gonar a tabbatar tashi ce kuma dole za su  bi ta hanyar masu unguwanni don tabbatar da gaskiyar manomin don tabbatar da gaskiyar manomin idan ka sami akasi babu shakka za a ladabtar da wanda ya yi karya kuma zai biya dukkan kudaden da aka bashi bashin.

Dantankari ya godema shugaban kasa Alhaji Muhammadu Buhari da ministan aikin gona da babban bankin Najeriya da Eco Monetary establishment da shugaban kungiyar na kasa baki daya Dokta Edwin Uche da kuma mai gayya mai aiki gwamnan jihar Katsina Alhaji Aminu Bello Masari yadda ya taimaki kungiyoyin manoman jihar, sannan yana kira ga gwamnatin jihar Katsina da kwamishinan aikin gona kuma mataimakin gwamnan jihar Alhaji Mannir Yakubu da su kara taimakon al’umma don habaka noman rani a jihar baki daya.

Daga karshen injiniya Alhaji Magaji ya gode ma dukkan ma’aikatan kungiya na jihar da shuwagabannin kungiyar na kananan hukumomi 34 na fadin jihar sannan ya yi kira ga manoman jihar da su ba mara da kunya wajen biyan bashin kuma su kara amfana da wani bashin na noman rani, duk wanda ya biya bashin noman damina ya cika sharuddan sake karbar bashin noman rani wanda za’a fara badawa ba da dadewa ba.

What's On Your Mind?