Manchester United Ta Fara Jin Kamshin Kofin Europa League

0
65

Manchester United Ta Fara Jin Kamshin Kofin Europa League

Kungiyar kwallon kafa ta Manchester United ta yi nasarar caskara kungiyar Roma da ci 6-2 a wasan zagayen farko na daf da karshe a gasar cin kofin Europa League da suka fafata ranar Alhamis a filin wasa na Previous Trafford.

Manchester United ce ta fara cin kwallo ta hannun dan wasanta na tsakiya, Bruno Fernandes, a minti na tara da fara wasan, sai dai Roma ta farke ta hannun Lorenzo Pellegrini a bugun fenareti sannan saura minti 11 su yi hutu ne Roma ta kara ta biyu ta hannun Edin Dzeko.

Minti biyu da komawa zagaye na biyu ne Edison Cabani ya farke kwallo, sannan ya kara ta biyu a ragar Roma sannan United ta kara cin ta hudu ta hannun dan wasa Bruno Fernandes a bugun daga kai sai mai tsaron raga, kuma ta biyu da shima ya zura a raga a fafatawar.

Tun bayan zuwansa kungiyar, Bruno Fernandes ya zama dan wasan Manchester United na uku da ya ci fenariti 20 ko fiye da hakan, bayan Ruud ban Nistelroy mai 28 da Wayne Rooney mai 27 a raga.

Saura minti 15 a tashi daga wasan dan wasa Paul Pogba ya kara kwallo ta biyar a raga, sannan daga baya aka sako dan wasa Mason Greenwood, wanda yayi canjin Marcus Rashford, ya ci kwallo ta shida.

A ranar Alhamis 6 ga watan Mayu za a buga wasa na biyu, inda Manchester United za ta ziyarci Roma a gasar ta Europa League a wasan da za’a fafata a babban filin wasa na Olympic dake birnin Rome na kasar Italiya.

What's On Your Mind?