Manchester City Ta Lashe Gasar Firimiyar Ingila

- Advertisement -

Manchester City Ta Lashe Gasar Firimiyar Ingila

Kungiyar kwallon kafa ta Manchester City ta lashe kofin Premier karo uku cikin shekara hudu bayan babbar abokiyar hamayyarta wato Manchester United ta sha kashi hannun Leicester City a ranar Talata.

Pep Guardiola ya lashe kofin ne da tazarar maki 10 kan Manchester United da ke matsayi na biyu ya yin da ya rage wasanni uku a kammala gasar firimiyar Ingila ta wannan kakar mai karewa.

Yanzu Guardiola mai shekara 50, ya lashe kofuna takwas tun zuwansa Manchester City a shekarar 2016 sannan tun a ranar Asabar ya kamata Manchester City ta lashe kofin amma ta sha kashi hannun Chelsea 2-1 a Etihad Stadium.

Amma yanzu, Leicester City ta kammala aikin inda ta doke Manchester United 2-1 a Outdated Trafford ranar Talata sannan kofi na biyu kenan da Manchester City ta lashe cikin mako biyu bayan ta doke Tottenham a kofin Carabao kuma yanzu tana harin lashe kofin zakarun Turai bayan ta kai wasan karshe inda za ta hadu da Chelsea.

- Advertisement -