Manchester City Ta Fara Jin Kamshin Zuwa Wasan Karshe

0
131

Manchester City Ta Fara Jin Kamshin Zuwa Wasan Karshe

Kungiyar kwallon kafa ta Manchester City ta fara jin kamshin zuwa wasan karshe na gasar cin kofin zakarun turai na bana bayan nasarar knowledge samu akan zakarun kasar Faransa, Paris Saint German a ranar Laraba.

Paris St Germain ta yi rashin nasara a hannun kungiyar kwallon kafa ta Manchester City da ci 2-1 a wasan farko zagaye na biyu a Champions League da suka fafata a kasar Faransa kuma kungiyar PSG ce ta far cin kwallo ta hannun dan wasanta na baya, Markuinhos kuma minti 15 da fara wasan.

Dan wasan ya zama na uku a tarihin gasar Champions League da ya ci kwallo a kuarter finals da karawar daf da karshe a kakar wasa biyu a jere a gasar kamar yadda alkaluma suka nuna a jiya.

Wadanda suka yi wannan bajintar a baya solar hada da dan wasan Jubentus Cristiano Ronado a kakar wasa 2011 zuwa 2012 da 2012 zuwa 2013 da kuma 2013 zuwa 2014, sai Antoine Griezmann da ya yi a shekarar 2015 zuw 2016 da kuma kakar wasa ta 2016 zuwa 2017.

Manchester City ta farke ta hannun dan wasan tsakiya Kebin de Bruyne da kuma Riyad Mahrez da kowanne ya ci daga bugun tazara wanda hakan ya bawa kungiyar ta kasar Ingila damar zuwa wasa na biyu da kwarin gwiwa.

Dan wasa Kebin de Bruyne ya zama dan wasa na hudu da ya ci PSG a haduwa uku a jere a Champions League, bayan Lionel Messi da Marcus Rashford da kuma Neymar a lokacin yana Barcelona.

Shi kuwa Riyad Mahrez ya yi sanadin cin kwallo 20 a wasa 26 a Champions League, bayan da ya ci takwas sannan ya bayar da 12 aka zura a raga a tarihin san a buga kofin zakarun turai gaba daya.

PSG ta karasa wasan da ‘yan kwallo 10 a cikin fili, bayan da ka bai wa dan wasan tsakiya, Idrissa Gueye jan kati saura minti 13 a tashi daga fafatawar bayan an similar shi da yin keta a gumurzun.

Gueye shi ne dan wasa na biyu da aka kora karo biyu a kakar zakarun turai na Champions League guda, bayan Albaro Arbeloa na Actual Madrid a kakar wasa ta shekarar 2012 zuwa 13 knowledge gabata.

Bugu da kari wannan shi ne wasa na hudu da suka buga a tsakaninsu a gasar ta zakarun Turai, inda Manchester City ta yi nasara a biyu da canjaras biyu kenan duk da cewa ba’a buga wasa na biyu ba.

Tarihin Haduwar Kungiyoyin

Manchester City ta ziyarci kungiyar kwallon kafa ta Paris St Germain domin buga wasan farko na daf da karshe a Champions League da su kara a Faransa sannan wannan shi ne wasa na uku da suka fafata a gasar Zakarun Turai, inda Manchester City ta yi nasara a karawa daya da canjaras biyu.

Karon farko kenan da Guardiola ya kai wasan daf da karshe a Champions League tun bayan da ya koma horar da kwallon kafa a Etihad a shekarar 2016 sannan zai kuma fuskanci kalubale a wajen PSG wadda ta kai wasan karshe a bara, wadda ta fitar da Barcelona da kuma Bayern Munich mai rike da kofi a bana.

Manchester City ta yi rashin nasara a wasa biyu daga biyar baya da ta fafata bayan nan a dukkan karawa da ta yi, wato jumulla cikin wasanni 33 ta yi rashin nasara a uku ne gaba daya a gasar.

PSG ta lashe wasanni 19 daga 25 da ta fafata a dukkan karawa da canjaras biyar aka doke ta wasa daya, inda ta ci kwallo 59 aka zura mata 21 a raga a wasannin sannan suma Pochettino da Guardiola solar fuskanci juna sau 18, inda kocin PSG ya yi nasara sau uku, shi kuwa na Manchester City ya lashe 10 da canjaras biyar.

Kyalian Mbappe ya ci kwallo 19 a wasanni 14 baya a PSG har da cin uku rigis da bibiyu sau bakwai da bajintar zura biyu a ragar Metz a Ligue 1 ranar Asabar sannan Manchester City ta yi nasara a wasanni 11 daga 16 baya da ta yi a gasar Zakarun Turai da rashin nasara biyu da canjaras uku.

Wasan karshe da aka ci Manchester City a waje shi ne wanda Shakhtar Donetsk ta yi nasara da ci 2-1 a Champions League a kakar wasa ta shekarar wasa ta shekarar 2017 zuwa 2018 knowledge gabata.

Karawar da aka yi tsakanin PSG da Manchester City:

2020/2021

Paris St Germain 1-2 Manchester City ranar Laraba 28 ga watan Afirilun 2021

2015/2016

Champions League Talata 12 ga watan Afirilun 2016

Man City 1 – zero Paris St-Germain.

Champions League Laraba 6 ga watan Afirilun 2016

Paris St-Germain. 2 – 2 Manchester City

2008/2009

UEFA CUP Laraba three ga watan Disambar 2008

Manchester City zero – zero Paris St-Germain.

Wadanda suka yi alkalanci fafatawar

Alkalin wasa: Felid Brych (Jamus)

Mataimakan akalin wasa: Mark Borsch da kuma Stefan Lupp (Jamus)

Mai kula da BAR: Marco Fritz (Jamus)

Mataimakin mai kula da BAR: Bastian Dankert (Jamus)

Alkali mai jiran ko-ta-kwana: Daniel Siebert (Jamus)

Jerin ‘yan wasan PSG da za su fuskanci Manchester City:

BAKKER Mitchel

DAGBA Colin

DIALLO Abdou

DI MARIA Angel

DRADLER Julian

FLORENZI Alessandro

GUEYE Idrissa

HERRERA Ander

ICARDI Mauro

KEAN Moise

KEHRER Thilo

KIMPEMBE Presnel

KURZAWA Laybin

MARKUINHOS

MBAPPÉ Kylian

NABAS Keylor

NEYMAR JR

PAREDES Leandro

PEREIRA Danilo

RAFINHA

RANDRIAMAMY Mathyas

RICO Sergio

SAIDANI Yanis

SARABIA Pablo

BERRATTI Marco

Wadan da ke yin jinya :

BERNAT Juan

FRANCHI Denis

GHARBI Ismael

KAMARA Abdoulaye

LETELLIER Aledandre

MICHUT Edouard

NAGERA Kenny

PEMBÉLÉ Timothée

SIMONS Xavi

 

What's On Your Mind?