Malam Aminu Kano: Ya Cika Shekara 38 Da Rasuwa (17/4/1983)

0
123

Malam Aminu Kano: Ya Cika Shekara 38 Da Rasuwa (17/4/1983) II

Ci gaba daga makon jiya

Ga kwafin wata wasika da Aminu Kano ya aikawa Sardauna lokacin yana raye

Wasika Da Aminu Kano Ya Aikawa Sir, Ahnadu Bello a Shekara ta 1958.

Zuwa ga Alhaji Ahmadu Sardaunan Sakkwato,
Ina mai farin ciki shaida maka cewa na sadu da wasikarka a ranar 1 ga wannan wata. Hakika, shirye-shiryen ka da suke cikin wannan takardar, babu shakka za su taimaki musulman kasar nan. Allah ya saka maka da mafificin alheri.

Kuma zan yi amfani da wannan dama wajen bayyana maka farin ciki na sport da irin karɓar da kake yi min, da kuma yadda ka nemi da in tuntube ka a kan duk wani batu da na ji zan iya yi a kan haka. Na tabbata wannan zai amfani abokanta kar mu, wadda muka kulla tun lokacin da ba daya daga cikin mu da ya san zai rike wani muƙami a gwamnati. Na yi alƙawarin ziyartarka a duk lokacin da nazo Kaduna komai kuwa irin yanayin aiyyukana

Shagulgulan ‘Yancin Kai: Manyan Al’amurra Fiye Da 60 Game Da Nijeriya

A cikin wasikarka na ga ka kawo wani batu da ya dade a raina, Wadda shi ne ‘yancin kai ga Arewacin Nijeriya da ma kasa baki daya, ka tuna da abin da na faɗa maka a cikin jirgin ruwa kan hanyarmu ta zuwa Landan na ce koda yaushe zan goyi bayan ka a kan maganar ‘yancin kai, ka kira ni a duk lokacin da ka bukace ni zan taimaka a duk wata hanya da zan iya. Amma Ina fatan za ka yi nazari a kan shawararin da zan bayar sannan ka kula da wa su tsiraru da za su yi kokarin biyan bukatun kansu da sunan yancin kai.

Ina fatan zaka sanar da ni a cikin lokaci duk lokacin da bukatar hakan za ta taso saboda yanayin tafiye-tafiye na.

Ina yi maka fatan kammala azumin watan Ramadan lafiya musamman a cikin wannan yanayi Na zafi. Allah ya shirya mana wannan kasa kuma ya daukaka ta.

Na ka. Aminu Kano.

TSAKANIN MALAM AMINU DA SARAKUNA DA TURAWAN MULKIN MALLAKA
Al’ummar yankin Arewa a kasarmu Nijeriya lokacin mulkin mallaka da bayan bada mulkin kai solar kasance a wani yanayi da Sarakunan Gargajiya da masu faɗa aji suka danne talaka da azabtar da shi tamkar bawa a wasu lokutan ma gara bawa kan irin kama karyar da ake yiwa talaka. Zamanin ya kasance cikin yanayi na danniya da kama karya da handama da babakere da nauyuka iri-iri na zalunci da aka dankara wa talakawa. Talakawa a lokacin na biyan kudin Haraji da Jangali da Nomau a gonakin masu mulki a kyauta. Wasu lokutan ma in masu mulkin lokacin suka kai rangadi a yankunan dake karkashin su akan tilasta wa magidanci ya bar gidansa da dukkan abunda ya mallaka harma da iyalansa domin saukar dasu da tawagarsu.

Malam Aminu Kano ya bayyana ne a tsakiyar lokacin da ake irin wannan zalunci da danne hakkin talaka. Yayi kira ga al’umma dasu bijire tare da kin amincewa da zalunci da kama karyan da akeyi masu tare da mutumta su kamar yan adam masu yanci da martaba. Kafuwar NEPU ke da wuya talakawa suka shiga Jam’iyyar babu kama hannun yaro wanda ya jawo tsoro da fargaba ga turawan mulkin mallaka da sarakunan gargajiya domin akidun NEPU na kira ne ga kawo karshen yadda suke tafiyar da mulkin su na son rai .

Talakawa a lokacin solar amsa kiran NEPU na samun yanci wanda hukumomi su kuma a lokacin suka dauki tsauraran matakai a kansu inda yayi sanadiyar daure tare da azabtar da magoya bayan NEPU. Wasu yan NEPU suka tafi gudun hijira wasu kuma a kama a sheka dasu barzahu. NEPU ƙarƙashin jagorancin Malam itace Jam’iyyar farko a tarihin kafuwar Nijeriya a kasa daya na yunkurin yanto talaka daga mulkin zaluncin fir’aunanci.

Mallam Aminu Kano shi ya jagoranci dubban yan gwagwarmayan kwato yanci da wadanda muka sami labarinsu da waɗanda ma ba’a taɓa jin su ba muka sami yancin da muke morewa a yanzu. Wasu yan NEPU ma tsire su akayi har suka mutu kamar sannanen labarin Malam Audu Angale. Shi dai an tsire shine a bainar jama’a bisa zargin da akeyi masa na batanci ga Iyayen masu mulki ba tare da gurfanar dashi a gaban shari’a ba. Haka ma an daura daruruwan yan NEPU ba tare da yi musu shari’a ba in ma an kaisu gaban shari’a ba a ba su damar kare kansu kan tuhumar da akeyi masu.

Irin wannan zalunci da fin karfi shi yasa wasu yan NEPU in aka kai su gaban alkali sai suce su yan mishan ne domin kotunan basu da hurumin yiwa wanda ba Musulmi ba shari’a sai a kai su kotun nasara inda za’a sake su domin babu shaidun da zasu tabbatar da zargin da akeyi musu.

NASARORIN DA YA SAMU A RAYUWA

Wanne nasarori ya samu a gwagwarmayarsa? Allah ya kaddara masa haddar Al-Kur’ani Mai girma wadda duk inda zai gabatar da jawabi da wahala bai kawo Aya ya fassara da take da alaka da taron ba, haka Lallai Mallam ya sami gagarumar nasara a gwagwarmayarsa na kawo karshen zalunci. Gwagwarmayar Malam ta tilasta wa Sarakunan gargajiya su sake salon mulkin su tare da kawo karshen nomau kyauta a gonakin masu mulki a kyauta. Ya kuma kawo karshen Haraji da Jangali. Sannan tsayuwar dakan da Mallam yayi ya baiwa ya’yan talakawa damar samun ilimi zuwa kowanne mataki sannan da rike mukaman siyasa da gwamnati wanda a da ya takaita ne kawai ga gidajen mulki, Yau a Najeriya tun daga kan shugaban ƙasa har kan wadda yafi kowa kankantar mukami Ƴaƴan talakawa ne
A yau a ko’ina a Arewacin Nijeriya mutane na kokarin sanin tare da kare hakkokin su da kundin tsarin mulkin kasa ya basu. Suna kuma shiga cikin harkokin bunkasar dimokaradiyya domin cigaban kasar su. A yau akwai yancin faɗin ra’ayin ka da walwala wanda masu mulkin mulukiya suka hana al’ummar su a wancan zamanin .
WASU DAGA CIKIN MANYAN ABOKAN GWAGWARMAYAR SA.
1. Malam Sa’adu Zungur
2. Bello Ijumu
three. Musa Kaula
four. Baballiya Manaja
5. Alhaji Adamu Danjaji
6. Magaji Dambatta
7. Mudi Sipikin
eight. Malam Abba Mai kwaru
9. Malam Illah Ringim
10. Muhammad Danjani Hadejia
11. Malam Audu Angale
12. Alhaji Dauda Dangalan
13. Hajiya Asabe Reza
14. Hajiya Gambo Sawaba
15. Malam Lawal Dambazau

Mrs. Bola Ogunbon
17. Muhammadu Abubakar Rimi
18. Sule Lamido
19. Gambo Hawaja
20. Sabo Bakin Zuwo
21. Alhaji Ali Kaura
22. Yerima Ballah

Da sauran su da dama
An saka sunan Malam Aminu Kano a, Filin jirgin saman ƙasa da ƙasa dake Kano, Asibitin koyarwa na Kano, Aminu Kano collage of Islamic and Authorized research, Filin taro na Aminu Kano Triangle dake Jigawa, Titin Aminu Kano Method a Kano, Jigawa, Lagos, Bauchi, Kaduna Da Abuja da sauran abubuwa masu yawa.

Ya rasu ya bar mata daya, Aishatu. Wadda Allah ya yiwa rasuwa ranar /22/5/2017 da ‘yarsa ɗaya Maryam. Sannan ya bar gida daya da gona ɗaya. Allah ya jikan Mallam da iyayenmu, da dukkan al’ummar musulmi.

What's On Your Mind?