Mako daya da bude Masallacin Harama, mutane 24,000 sun yi ibadar Umarah

0
121
  • Kusan mako daya yanzu da bada iznin cigaba da Umrah, babu wanda ya kamu da Korona

  • An tanadarwa tsofaffi da marasa karfi hanyoyi a musamman domin nasu ibadar

  • Saudiya ta samu sauki sabbin masu kamuwa da Korona yayinda masu waraka na kara yawa

Akalla mutane 24,000 sun yi ibadar Umarah tun lokacin da aka bude Mallacin Harama dake Makkah ranar Lahadi, 4 ga watan Oktoba, 2020 kuma babu wanda ya kamu da cutar Korona.

Ofishin kula da lamuran Masallatan harama biyu a ranar Laraba ta ce an samar da ka’idoji domin kare maniyyata da kuma hana yaduwar cutar COVID-19.

Mako daya da bude Masallacin Harama, mutane 24,000 sun yi ibadar Umarah

“Matakan kariyan da muka shirya domin Umarah lokacin Korona sun hada da tsaftace muhalli, hana cakuduwan jama’a da kuma wayar da kan mutane, ” Kakakin ofishin, Hani Haidar.

“Mun shirya cibiyoyin kebance duk wanda aka gani da wasu alamun cutar.”

“Amma babu labarin wanda ya kamu da COVID-19 ko daya har yanzu.”

An kashe dan sanda daya a yayin da zanga-zangar neman rushe SARS ta rikide zuwa rikici a wasu jihohi 3

Domin tabbatar da cewa ana baiwa juna tazara, ofishin ta shirya hanya ta musamman ga masu manyan shekaru da kuma masu nakasa saboda su gudanar da Umrah cikin kwanciyan hankali.

Haidar yace ma’aikata 4000 aka tanada domin tsaftace Masallacin Ka’aba akalla sau 10 a rana.

Hakazalika an tanadi litan sinadarin tsaftace muhalli saman da lita 1,8000 domin wanke bayan gida sau shida a rana.

Bugu da kari, ana goge na’urar bada sanyi watau AC akalla sau tara a rana.

A wani labarin daban, Wata kotu a kasar Yemen ta zartar da hukuncin kisa a kan wasu mutum 10 ciki har da Shugaba Donald Trump, Sarki Salman Bin Abdulaziz Al-Saud, da Yarima Mohammed Bin Salman Bin Abdulaziz Al-Saud saboda aikata laifukan yaki.

An zartar da hukuncin ne a wani Kotu na musamman na masu manyan laifuka a Saada akan harin hadin gwiwa da aka kai wa wata motar bas cike da kananan yara a mazabar Majz.

What's On Your Mind?