Mako biyu da yin aurenta amarya ta fara korafi, ta ce mijinta yana aikenta barkatai

0
143

Mako biyu da yin aurenta amarya ta fara korafi, ta ce mijinta yana aikenta barkatai

Shahararriyar matashiyar nan ta kasar Ghana, Abena Moet, ta haddasa cece kuce recreation da ra’ayinta a kan aure bayan shafe kusan makonni uku a gidan miji.

A cikin bidiyon barkwancin da ke yawo a shafukan sada zumunta, Abena Moet ta nuna cewa daga abin da ta gani, da zaran kin yi aure a matsayinki na mace, toh kawai mijinki zai ta aikenki ne yadda ransa ke so.

An gano ta a bidiyon tana kallon kafaɗarta don tabbatar da cewa sabon mijin nata ba ya jin abunda take fadi a bidiyon nata.

Kalli bidiyon a kasa:

Maryam Malika Ta bayyana Matsayin Aurenta a Yayin cike Form din zama cikakkiyar Jaruma a Kannywood

Abena Moet ta yi aure a wani kasaitaccen biki da ya bazu a yanar gizo a ranar 27 ga waran Maris, 2021.

A wani labarin kuma, rundunar yan sanda reshen jihar Enugu ta kama wata mata yar shekara 29, Nnenna Egwuagu, da zargin kashe ɗan kishiyarta dan shekara uku, Knowledge Egwuagu.

Lamarin ya faru ne a garin Umulumgbe dake ƙaramar hukumar Idi, jihar Enugu ranar 9 ga watan Afrilu kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Rahotanni solar bayyana cewa matar da ake zargin ta baiwa yaron wani abu dake ɗauke da guba, kuma hakan ya yi sanadiyyar mutuwarsa.

What's On Your Mind?