Majalisar Wakilan Nijeriya Ta Bukaci Buhari Ya Ayyana Dokar Ta Baci Akan Sha’anin Tsaro

0
122

Majalisar Wakilan Nijeriya Ta Bukaci Buhari Ya Ayyana Dokar Ta Baci Akan Sha’anin Tsaro

Yanayin tabarbarewar tsaro a dukkan sassan Nijeriya ya sa majalisar wakilan kasar ta bukaci shugaba Muhammadu Buhari da ya ayyana dokar ta baci akan sha’anin tsaro a kasar.

Daga cikin matsayar da aka cimma a zaman zauren majalisar wakilan na ranar jiya Talata, majalisar ta yi kiran da a dauki karin ma’aikata da jami’ai a hukumomin tsaron kasar, ta yadda za su sami isassun ma’aikata da zai ba su damar shawo kan kalubalen tsaro.

‘Yan majalisar solar kuma ce za su gayyaci mai bai wa shugaban kasa shawara a sha’anin tsaro, da manyan hafsoshin tsaro, da ma dukkan shugabannin hukumomin tsaro na kayan sarki, domin su yi bayani akan halin da kasa take ciki akan sha’anin tsaro.

Haka kuma majalisar ta umarci dukkan kwamitocinta na sha’anin tsaro, da su gaggauta soma cikakken bincike akan dukkan kayan aiki da makamai na rundunar soji da sauran hukumomin tsaro, su kuma gabatar da rahoton binciken na su a cikin makwanni four.

Majalisar ta kuma yi kira ga bangaren shari’a da ya gaggauta yanke hukunci ga wadanda ake tuhuma da laifukan ta da kayar baya, ta’addanci da sauran manyan laufuka, wadanda ke zaman jiran hukunci.

Bugu da kari, majalisar wakilan ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ta tabbatar da bai wa kananan hukumomi ‘yancin cin gashin kan su, ta yadda za su sami damar biyan bukatun jama’arsu a yankunan karkara.

Majalisar dokokin ta yi Allah wadai da hare-haren da ake kai wa hukumomi da jami’an tsaro a fadin kasar, inda kuma ta jajantawa iyalai da ‘yan uwan dukkan wadanda matsalar tsaro ta rutsa da su, kana kuma ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ta tallafa musu.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ‘yan Nijeriya ke ci gaba da zaman dar-dar tare da fargaba, sanadiyyar kara yawaitar kalubalen tsaro a fadin kasar.

A ranar Litinin da ta gabata ne Gwamnan Jihar Neja Sani Bello, ya yi koken cewa kungiyar Boko Haram ta kafa tutocinta a wasu sassan jihar, yayin da al’ummar garuruwa fiye da 50 solar yi kaura daga gidajensu.

Rahotanni solar bayyana adadin wadanda suka mutu daga cikin daliban jami’ar Greenfield ta Kaduna da aka sace cewa ya karu zuwa biyar bayan da ‘yan bindigar da suka sace su suka dada kashe wasu biyu.

A wannan ranar ce kuma wasu mahara da ake zargin ‘yan kungiyar fafutukar kafa kasar Biafra ce suka kai farmaki a Awkuzu da ke Yankin Karamar Hukumar mulki ta Oyi a Jihar Anambra, inda suka kashe mutane akalla 12.

A jihar Ribers ma ‘yan bindiga solar kai hari suka kashe kimanin sojoji shida a yankin Omelema da ke yankin Karamar Hukumar mulkin ta Abua/Odual.

Haka kuma wasu ‘yan bindiga da ba’a san ko su waye ba solar kai hari a jami’ar koyon aikin gona ta tarayya a Makurdi ta Jihar Benue inda suka yi awon gaba da dalibai uku.

A jiya ne dai shugaba Muhammadu Buhari, ya nemi kasar Amurka da ta kawo wa Nijeriya dauki, duba da yadda matsalar tsaro ke kokarin kassara kasar. A can baya dai majalisar Wakilai ta yi yunkurin gayyatar shugaba Buhari domin ya bayyana a zauren majalisar ya kuma yi bayanin yadda ake ciki a sha’anin yaki da matsalar tsaro.

Da farko ya amince zai amsa gayyatar majalisar, amma daga baya ya sauya shawarar cewa ba zai bayyana a gaban majalisar ba a wannan lokacin, saboda wasu dalilai na siyasa.

A gefe guda kuma, Shugaban Muhammadu Buhari ya gana gana da Sakataren Harkokin Wajen Amurka Antony Blinken, inda suka tattauna kan batutuwan da suka hada da karfafa dangantakar kasashen biyu da kuma batun tsaro.

Wannan ganawa na wakana ne, a daidai lokacin da Nijeriya ke fuskantar kalubalen tsaro daga kungiyoyin ISWAP da Boko Haram yayin da matsalar garkuwa da mutane don neman kudin fansa ta zama ruwan dare.

Wannan kuwa na zuwa ne albarkacin wani rangadi na farko ta na’urar sadarwar bidiyo da sakataren na harkokin wajen Amurka zai soma a yau, a kasashen Nijeriya da Kenya na nahiyar Afirka.

Worth ya ce a lokacin ziyarar ta na’ura, Antony Blinkin zai yi taro da shugaba Muhammadu Buhari, da kuma Ministan Harkokin Wajen Nijeriyar Geoffrey Onyeama, domin sake karfafa matsayin dangantakar diflomasiyya tsakanin Amurka da Nijeriya, wadda kuma ke da matukar muhimmanci ga dukan kasashen biyu.

Karin bayani akan: Antony BlinkinBiafra, Boko Haram, Shugaba Muhammadu BuhariNigeria, da Najeriya.

To sai dai ‘yan Nijeriya da dama na fatan wannan ganawar za ta yi tasiri a sha’anin yaki da matsalar tsaro, da yanzu haka take kara habaka a dukkan sassan kasar.

Rahotanni na baya-bayan nan na nuni da cewa yanzu haka kungiyar Boko Haram ta karbe ikon a wata karamar hukumar mulki a yankin Arewa maso Gabas, da kananan hukumomin mulkin Kaure da Shiroro a Jihar Naija da ke Arewa maso yammacin Najeriya.

Haka kuma ‘yan bindiga a wasu sassan Arewa maso Yamma na ci gaba da kai hare-hare inda suka ta da garuruwa da dama, kazalika da uwa-uba, satar mutane domin karbar kudin fansa. A yankin kudancin kasar nan ma kungiyar nan mai fafutukar kafa kasar Biafra, ta sabunta kai hare-hare biyo bayan kashe kwamandanta a karshen mako, inda a baya-bayan nan ma suka kai farmaki a wani gidan Fulani, suka yi wa mutane 19 kisan gilla a jihar Anambra.

What's On Your Mind?