Majalisar Wakilai Ta Bukaci Buhari Ya Sa Dokar Ta-baci A NIjeriya

0
108

Majalisar Wakilai Ta Bukaci Buhari Ya Sa Dokar Ta-baci A NIjeriya

Daga Yusuf Shu’aibu,

Majalisar wakilai ta tarayya ta bukaci gwamnatin tarayya ta ayyana dokar ta-baci a kan tsaro tare da kara yawan sojoji da ‘yan sanda, sakamakon tabarbarewa tsaro a ‘yan kwanakin nan a yankunan kasar nan. An yi asarar rayukan jama`a a sassan kasar da dama ga kuma fargabar da ake yi cewa mayakan Boko Haram solar kwace iko a wasu yankunan Jihar Neja har solar kafa tutocinsu. Shawarar majalisar wakilai ta tarayya ga shugaban kasa Muhammadu Buhari na ayyana dokar ta-baci a harkar tsaro ta kasar, ya biyo bayan da mayakan Boko Haram suka kwace wasu yankuna 42 a Jihar Neja. Wannan na cikin kudurori 12 da ‘yan majalisar suka zartar bayan awowi sama da uku suna tafka muhawara.

‘Yan majalisar dokoki solar nuna damuwa sport da yadda tsaro ke kara tabarbarewa a kasar nan musamman ma kisan da ‘yan bindiga suke yi wa jamaa ciki har da jamian tsaro. Bukatar majalisar ta ayyana dokar ta-baci a kan harkar tsaro na zuwa ne yayin da ita kuma majalisar dattawa ta yanke shawarar gayyatar hafsoshin tsaron domin su yi musu bayyani. Gwamnatin Buhari dai ta amsa cewa tana fuskantar matsaloli na tsaro kamar yadda mataimakin shugaban kasar, Farfesa Yemi Osinbajo ya fada a ranar Litinin cikin wata sanarwa, amma ya ce gwamnati za ta iya magance su.

Sai dai masana dai na ganin akwai gazawar shugabanci da suka jefa Nijeriya cikin wannan yanayi. Ana ganin abubuwan da ke faru a Nijeriya na tattare da hatsari ga makomar kasar mai bambanci jama’a da kabila da addini.

Majalisar ta yi wannan kira ne ga shugaban kasa a dai-dai lokacin da ake kara samun matsalolin tsaro, wanda ko a makon da ta gabata an kashe mutane da dama a Nijeriya. Haka kuma, ‘yan bindiga masu da Boko Haram na ci gaba da kai hare-hare tare da satar mutane domin biyan kudin fansa.

Jihar Zamfara na cikin wuraren da ‘yan bindiga suka kasha fiye da mutum hamsin a makon jiya. ‘Yan bindiga solar sace dalibai da dama a Jihar Kaduna. A kwanan nan gwamnatin Neja ta ce Boko Haram ta kwace wasu yankunan jihar tare da kafa tuta. Mayakan Boko Haram da na ISWAP solar tsaurara kai hare-hare inda suka suke fitowa suka yi ikirarin kai hari a garin Geidam na Jihar Yobe wanda har yanzu ba a tantance yawan mutanen da aka kashe ba. ‘Yan bindiga kuma solar kashe jami’an tsaro a Jihar Ribas a harin da ake zargin ‘yan IPOB ne suka kai. Jami’an tsaron kasar nan na ta kokarin shawo kan karuwar hare-haren ‘yan bindiga da ‘yan bindiga masu satar mutane domin amsar kudin fansa da kuma wadanda ake zargin ‘yan a ware.

Halin da Nijeriya ke ciki ta sanya gamayyar kungiyoyin fararen-hula na Arewacin kasar, wato Coalition of Northern Teams ta shawarci matasa cewa suna da gagarumar rawar da za su taka wajen shawo kan kalubalen da kasar ke fuskanta ta fannin tsaro. Gamayyar kungiyoyr wcce ta ji takaicin kisan da ‘yan bindiga suka yi a sassan Nijeriya cikin kwanakin nan, ta yi zargin cewa babu abin da shugabannin siyasa za su tsinana, saboda batun zabe ne ke kan gabansu ba tsaron rayukan ‘yan kasa ba.

What's On Your Mind?