Majalisar koli ta Shari’ar Musulunci ta jinjinawa gwamna El-Rufa’i

0
32

Majalisar koli ta Shari’ar Musulunci a Najeriya ta jinjinawa gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa’i bisa rusa otel din da aka shirya banbadewa zindir makon da ya gabata.

Majalisar ta ce ire-iren wadannan laifukan ke gadarwa al’ummar Najeriya fushin Allah.

Hakazalika ta yabawa gwamnatin jihar bisa damke wadanda suka shirya bikin.

Majalisar koli ta Shari'ar Musulunci ta jinjinawa gwamna El-Rufa'i

A jawabin da shugaban majalisar na jihar Kaduna, AbdurRahman Hassan, ya saki, ya ce ire-iren wadannan taron shaidancin ke haifar zuba da jini da ake yi ta hanyar garkuwa da mutane, fashi da makami.

“Ko shakka babu, ire-iren wadannan abubuwa ya gadar mana fushin Allah (SWT) da muke fuskanta yanzu,” wani sashen jawabin yace.

An yi jana’izar Iyan Zazzau, Alh Bashar Aminu, a Zariya

“Lalacewar tarbiyyanmu ke haifar da zub da jinin da akeyi ta hanyar garkuwa da mutane, fashi da makami da sauran laifuka.”

“Yayinda muke yabawa gwamnatin jihar Kaduna kan wannan abun alkhairin da tayi, muna kira da gwamnatin ta zuba ido kan sauran wuraren da ake ire-iren wadannan abubuwa a jihar, irinsu Ajagunle, dake Maiduguri Street, karamar hukumar Kaduna ta Arewa, inda akwai gidajen tsiraici.”

A bangare guda, hukumar yan sandan jihar Kaduna a ranar Alhamis ta bayyana wadanda suka shirya taron banbadewa zindir da aka shirya a shirya kwanakin baya.

Kwamishanan yan sandan jihar, CP Umar Muri, ya bayyana cewa an damke matasan a ranar 27 ga Disamba, 2020, bayan solar yanke shawaran gudanar da casun mai take “Casun lalaci a Kaduna” a wani otel da karamar hukumar Kaduna ta kudu.

Wadanda aka damke sune: Abraham Alber, mammalakin otel din, Umar Rufa’i da Suleiman Lemona, Every day Belief ta ruwaito.

What's On Your Mind?