Majalisar Dokokin Kaduna Ta Kwabe Tsohon Shugabanta Daga Mazabarsa

0
83

Majalisar Dokokin Kaduna Ta Kwabe Tsohon Shugabanta Daga Mazabarsa

Daga Abubakar Abba,  Kaduna

Majalisar Dokokin jihar Kaduna ta kwabe tsohon shugaban majalisar Aminu Abdullahi Shagali da ke wakiltar Sabon Gari daga kujerarsa ta dan majalisa yayin da ta bayyana kujerar a matsayar wadda babu kowa a kanta.

Hakan na kunshe ne a cikin  sanarwar da shugaban ma’aikata na shugaban majalisar Haruna Jafaru Sambo ya sanya wa hannu.

Majalisar ta yanke wannan hukunci ne biyo bayan karya dokokin majalisar na kin zuwa zaman majalisar har tsawon Kwanaki dari da ashirin.

Bugu da kari, majalisar ta kuma kara fadada dakatar da wasu ‘yan majalisu guda hudu na tsawon shekara Guda, sakamakon kama su da laifin cin amanar majalisar.

Mutanen da majalisar ta dakatar solar hada da Mukhatar Isa Hazo da ke wakiltar Basawa da Salisu Isa da ke wakiltar Magajin Gari da Nuhu Goro da ke wakiltar Kagarko sai kuma Yusuf Liman da ke wakiltar Makera.

Majlisar ta dauki wannan matakin ne a wani karamin zama da mataimakin shugaban majalisar Rt. Hon. Dakta  Isaac Auta Zankai ya jagoranta a ranar Talatar nan.

What's On Your Mind?