Majalisar Dokokin Bauchi Ta Gargadi ’Yan Kwangila Bisa Aikata Ha’inci

0
138

Majalisar Dokoki ta jihar Bauchi ta yi gargadi da kakkausar murya wa ‘yan kwangila da ke gudanar da aiyukan gine-gine da gyare-gyaren ajujuwan karatu na ‘yan makaranta karkashin kulawar hukumar bayar da ilimi bai-daya ta jihar Bauchi (SUBEB) da su guji yin ha’inci cikin ayyukan da aka ba su.

Shugaban Kwamiti na Majalisar Kan Lamuran Ilimi, Honarabul Babayo Muhammad Akuyam shine ya yi wannan gargadi lokacin da kwamitin sa ya kai ziyarar gani da ido kan aiyukan hukumar ilimi bai-daya na shekarun 2017/2018 a kananan hukumomin Gamawa, Warji da Ningi.

Majalisar Dokokin Bauchi Ta Gargadi ’Yan Kwangila Bisa Aikata Ha’inci

Ya lura da cewar, akwai ha’inci a cikin wasu aiyukan makarantu da ‘yan kwangila suke gudanarwa a wannan lokaci, yana mai yin tir da amfani da kayayyakin aiyuka marasa ingaci, ma’aikata marasa kwarewa, da rashin bin tsarin gyara ko gini da aka zayyana, sune ummul-aba’isin rashin ingancin aiyuka da ‘yan kwangilar ke gudanar wa.

Honorabul Babayo Akuyam don haka ya roki ‘yan kwangilan da su gudanar da aiyukan nasu da sanin ya kamata, hadi da gujewa yin ha’inci domin su al’ummomin da ake yiwa wadannan aiyuka su ci moriyar aiyukan yadda ya kamata, tare da inganta rayuwar su.

Shugaban kwamitin na majalisa, sai ya baiwa ‘yan kwangilar tabbacin cewar, gwamnati a shirye take domin jin korafe-korafen su da zummar magance su, hadi da samun nasarar su.

Akuyam ya bayyana cewar, ziyarar ta gani da ido ta zama wajibi, biyo bayan rahotanni da ake samu kan yadda ‘yan kwangilar suke yiwa aiyukan rikon sakainar kashi, hadi da rashin la’akari da makudan kudade da gwamnatin jihar ke kashewa kan wadannan aiyuka domin inganta lamuran malamai da dalibai a makarantu.

Dogaro: NDE Na Bai Wa Mata Da Matasa 300 Horo A Bauchi

Dan majalisa Babayo Akuyam sai ya bukaci ‘yan kwangilan da su rika yin waiwaye bisa yarjejjeniyoyi da aka cimma tare da su kafi fara wadannan aikace-aikace na gina sabbin ajujuwa da kuma gyare-gyaren su, da nufin kwalliya ta biya kudin sabulu.

Ya jaddada bukatar a rika bibiyar aiyukan ‘yan kwangila, tare da tantace ire-iren aiyukan su a kowane bigire na kwangilolin, kafin a baiwa dan-kwangila umarnin cigaba zuwa wani bigire na aikin da ya ke gudanarwa.

Shugaban kwamitin na majalisa ya lura cewar, a mafi yawancin makarantu da suka ziyar ta, gine-ginen da aka gudanar ba su da inganci, rufin gine-gine suna yoyon ruwan sama, katangu da wasu rufin dakunan karatu photo voltaic tabarbarce, lamuran dake wanzar da kalubale wa rayuwar matasa.

Honarabul Babayo Akuyam daga karshe ya shawarci ma’aikatan hukumar bayar da ilimin bai-daya da su tantance ajujuwan karatun dalibai kafin fara amfani da su.

What's On Your Mind?