Mai Horas Da ‘Yan Wasan Wikki FC Ta Bauchi Ya Yi Murabus

- Advertisement -

Mai Horas Da ‘Yan Wasan Wikki FC Ta Bauchi Ya Yi Murabus

Daga Khalid Idris Doya, Bauchi

kasa da kwanaki uku da suka gabata bayan shan kashi da ta yi daga kungiyoyin wasannin kwallon kafa na jihohin Katsina da Nasarawa, mai horas da ‘yan wasan kwallon kafa na kungiyar Wikki FC ta Bauchi, Malam Usman Abd’allah ya ajiye aikinsa.

Ita dai kungiyar ta kwallon kafa ta Wikki Vacationer Soccer Membership, Bauchi ta sha kashi ne a hannun kungiyar kwallon kafa ta Katsina United da ci biyar da daya (5-1) a garin Katsina da kuma ban kashin 2-1 daga kungiyar kwallo ta Nasarawa soccer membership a wasan su a garin Bauchi.
Dangane da wannan kisan mummuke ne da aka yi wa kwallon kafa ta Wikki, kungiyar masu rubuta labaran wasanni ta kasa reshen Jihar Bauchi (SWAN) ranar sati da ta gabata ta bayyana rashin jin dadin ta dangane da wannan lamari mai ban takaici da kungiyar ta Wikki take yi a cikin zangon wassannin kwararru na kasa da ake cigaba da fafatawa.

kungiyar ta SWAN sai ta yi kira wa gwamnatin Jihar Bauchi da ta hamzarta kafa wani kwamiti da zai gano matsalolin dake addabar kungiyar kwallo ta Wikki a fagen wasannin kwararru na kasa domin yi wa tufkan hanci warwara.

SWAN ta kuma yi kira ga hukumar kwallo ta Wikki da ‘yan wasannin ta da su tashi daga barci domin dawo wa kungiyar ta Wikki darajar ta a fagen wasanni.
Mai horas da ‘yan wasan kwallon kafa ta Wikki dai a jiya Talata ne ya gabatar da takardar sa ta ajiye aiki wa kungiyar kwallo kafa ta Wikki.

A cikin takardar tasa ta ajiye aikin horaswa, Usman Abd’allah yana mai cewar, “Tare da ladabi da hamdala na damar da aka bani nayin aiki da wannan kungiyar kwallo ta Wikki, ina mai bakin cikin gabatar da takardata ta ajiye aikin horas da ‘yan wasan ku, tare da yin fatar alheri wa kungiyar ta wikki a dukkan lamuran ta a nan gaba”.

An dai jima ana korafin rashin tabuka abun a zo a gani daga kulob din Wikki inda ake daura alhakin matsalolin ga masu horas da ‘yan wasan da kuma masu gudanar da lamuran ‘yan wasanta.

- Advertisement -