Mahangar Mata Kan “Miji Nagari”

0
75

Mahangar Mata Kan “Miji Nagari”

Masana a bangarorin zamantakewa solar tattauna batun aure a matsayin muhimmin jigo a rayuwar dan Adam, sannan kuma ya ake kulla shi bisa yarjejeniya mai cike da fahimtar juna a manufar kasancewa waje daya wanda ta hanyar sa ne halittu ke hayayyafa kuma ta yadu kana ta wanzu a bayan kasa, kana kuma ta hanyar sa ce ake tantance halatattun mazauna a bayan kasa, haka kuma aure shi ne hanyar dakile husuma da tabbatar da hakki kan abokan zamantakewa a rayuwar auratayya.

 

Bugu da kari kuma, idan an kebanci batun aure a zamantakewar dan Adam, shi ne babban jigon rayuwa wanda dukan al’ummar duniya ta yi tarayya wajen kasantuwar sa ba tare da sabani ba; wanda dukan bangarorin addinai, da wadanda ba su da addini- face kawai bambancin al’adu, tunani da hanyoyin gudanar dashi ke da sabani nan da can.

 

Aure a mahangar Mululunci, a karkashin faffadan bayani dangane da kima da muhimmanci, a hannu guda kuma solar bayyana matakan gudanar da shi, tun daga matakin farko zuwa karshe. Wanda ko shakka babu duk ma’auratan da su ka bi godaben da addini ya shata, ba su ba da-na-sanin haduwar su (mutu ka raba), sabanin wadanda su ka kaucewa tafarkin tare da kama hanyar shaidan da son rai; a nan fa takima da jidali su ke.

 

Zancen daya ne- dukan mazhabobin addinin Musulunci solar yi baki-guda kan muhimmanci tare da cimma matsaya kan shika-shikan sa na asali face yan bambance-bambancen da ba a rasa ba wajen yi masa tubka ko warwara idan ta baci. Yayin da kowace kabila a duniyar nan a haka ta ginu a kai, face bambancin al’adu da yanayin zamantakewa.

 

A zubi da tsarin da musulunci ya yi wa turbar aure babu wasa ko shakka a ciki tsagwaron hikimomi ne, tausayi ne, soyayya ce, kauna ce, arzikin duniya da lahira ne. Kaicho, rashin sani ya fi dare duhu kana kuma rashin sani ya jawo kaza ta kwana a kan damin hatsi, musamman halin da duniyar mu a wannan zamani ta tsinci kanta, wanda duk da kasancewar aure babban ginshiki kuma jigo a rayuwa, amma an shigar da bakin abubuwa maras tushe a ciki.

 

A wani kaulin, Annabin Rahama (s), dangane da kasancewar aure babban ginshiki kuma jigo rayuwa, ya ce: rayuwar duniya dadi ne dan kankani, kuma mafificisa shi ne samun mace tagari (ko miji nagari). Wanda a takaice wannan ya nuna irin muhimmancin samun abokiyar zama (ko abokin zama) nagari tsakanin ma’aurata, tare da bayar da tabbacin babu wani dadi da nutsuwar da ya kai shi a rayuwar dan Adam. Sannan kuma rashin samun abokin zama nagari babban cikas ne a rayuwar yau da kullum ga dan Adam, wanda tasirinsa ya isa a kalle shi da kima.

 

Sai dai kash, duniyar maaurata a halin yanzu tana cike da rudani, al’amarin da ya kara jefa tsarin rayuwar dan Adam mafi muhimmanci a cikin garari, hana ruwa gudu a yanayin zamantakewar aure, sannan abin fargaba shi ne irin yadda abin ke ci gaba da tabarbarewa maimakon shawo kan matsalar. Har wala yau, duk irin jawabai da tunatarwar da malamai da masana ke yi dangane da hatsarin da ake ciki, wanda yake ci gaba da shafar al’umma da jawo koma baya a yanayin zamantakewa.

 

Akwai matsaloli daban-daban da suka dabaibayi tasarin zamantakewar auratayyar al’ummar mu a yau, musamman a yankin arewacin Nijeriya, wanda mafi muni shi ne irin yadda ake yi wa tsarin aure shigar sauri, kutse da hawan kawara. Haka zalika kuma, akwai alaka tsakanin halin da tsarin auratayya da zamantakewarsa ke ciki da yadda yake gudana a zahirance, hadi da kallon da mafi yawan mutane ke yi masa.

 

A hannu guda kuma, duk da hakan za ka tarar kowane mutum idan ya tashi aure ya dage sai ‘mace ta gari’ ko miji nagari zata aura, a tunanin sa shi ne nan ne mafita take a tsarin rayuwa. Amma inda gizon ke saka shi ne: anya mun san “mace tagari ko miji nagari”? Sannan ko shakka babu, kalmar nan yar gajera ce amma kuma doguwa ainun idan an zurfafa binciken waye hakikanin “nagari”! Saboda lalle sanin amsar wannan tambayar sai anyi jibin goshi da shan wahalar gano hakikanin wannan al’amari.

 

Kowa burinsa shi ne samun mace tagari ko miji nagari, kuma hakan yana da munasaba da yakinin da kowane mutum ya yi a kan cewa ita ce hanya kwaya guda wadda zata kai mutum gaci a zamantakewar rayuwar yau da kullum. Sai dai inda gizon ke saka shi ne, anya a shirye muke kuma shin abu ne mai sauki mu wajen gano ko su waye “nagari”, kuma shin muma nagarin ne wanda ya sa har muke shaukin su?

 

Ko shakka babu, duk mutum mai hankali yana da burin samun mace tagari, ita ma babu wata mace mai hankali wadda ba burinta samun miji nagari ba. Sai dai inda gizon ke saka shi ne zai yuwu mu iya gane nagari kuma mu amince dashi a wannan tunani namu da kwakwalwar mu wadda ta cika da son rai da neman abin duniya ido a rufe? Anya miji nagari ba mai abin hannu da shuni mafi yawan yan mata ke ikirari ba, ko matasanmu?

 

A bayanan masana a wannan fannin, solar yi faffadan bayani dangane da “mata tagari” ko “Miji nagari”, wanda a hakikanin gaskiya, gano hakikanin nagari jan aiki ne tsakanin matasanmu a yau, saboda yadda son rai da rungumar abin duniya kai tsaye. Wanda hakan ya na iya kasancewa hijabi kuma katanga wajen sanin abubuwa masu muhimmanci irin wannan, mai cike da tasiri kuma jigo a tsarin zamantakewar rayuwar dan Adam.

What's On Your Mind?