Mahaifiyar Sarkin Kano Ta Rasu!

0
109

Mahaifiyar Sarkin Kano Ta Rasu!

Kwaryar birnin Kano ta shiga dimuwa sakamakon bayyanar labarin mutuwar  mai dakin marigayi Sarkin Kano, Alhaji Ado Bayero, wadda kuma itace mahaifiyar sarakkuna biyu masu ci a halin yanzu a masauratar Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero Sarkin Kano da Alhaji Nasiru Ado Bayero Sarkin Bichi.

Marigayiyar Hajiyar Maryam Ado Bayero ta rasu da safiyar Asabar a wani Asibiti dake kasa Masar, marigayiyar  tayi fama da rashin lafiya wanda hakan yasa aka kwantar da ita a wani asibiti dake Cairo ta Kasar Masar makonnin da suka  gabata.

Innalillahi wa inna ilaihi Raji’un!!! Allah Yayiwa Mahaifiyar Sheikh Kabiru Haruna Gombe Rasuwa

Maryam Ado Bayero ‘ya ce ga Sarki Illori da ke jihar Kwara, Sulu Gambaru, mai dakin marigayi Sarkin Kano Alhaji Ado Bayero kuma mahaifiyar sarakuna biyu masu ci a ahalin yanzu a masarautar Kano Alhaji Aminu Ado Bayero da kuma AhajiNasiru Ado Bayero.

Marigayiya Hajiya Maryam mai babban dakin Kano da Bichi, ‘yar Sarkin  illori Zuilkarnani Gambari, dan Sarkin Illori Shu’aibu Bawa, dan Sarkin Illori Zubairu, Dan Sarkin Illori Abdussalami, Dan Sarkin Illori Salihi Alimi (Bafulatani) mai tutar Shehu Usman Danfodiyo. Haka zalika ya yace ga Sarkin illori  na yanzu, kuma Kanwa ga mahaifiyar matar Sarkin illori na yanzu.

What's On Your Mind?