Mahaifin Marubuci Habibu Hudu Darazo Ya Kwanta Dama

- Advertisement -

Mahaifin Marubuci Habibu Hudu Darazo Ya Kwanta Dama

Marubuci Habibu Hudu Darazo fitaccen marubuci ne da sunansa ya yi shuhura a duniyar rubutu da marubuta. Ya taba rike shugabancin kungiyar marubuta ta ‘Hausa Authors Discussion board’ Ya wallafa littattafai da dama da suka hada da: Zafin Nema, Makauniyar Shari’a, Nisan Kwana, dan Makaho, da dai sauransu.

Marubuci Habibu Hudu Darazo, ya rasa mahaifinsa ne Alhaji Hudu Ahmad Darazo a daren ranar Alhamis da ta gabata a sakamakon hadarin mota da ya rutsa da shi, wato 29/04/2021 wanda ya yi daidai da 17, Ramadhan, 1442. Kuma aka yi jana’izarsa a washe gari ranar Juma’a da protected, inda aka sallace shi a fadar Maimartaba Sarkin Kanya Darazo L/G dake jahar Bauchi.

Marigayi Alhaji Hudu Ahmad, ya rasu yana da shekaru Saba’in Da Shidda (76) a duniya, ya bar ‘ya’ya Goma Sha Daya (11) Bakwai (7) maza, Hudu (four) mata, da kuma jikoki guda Arba’in Da Shida (46). Daga cikin ‘ya’yan nasa akwai: Sale Hudu Ahmad wanda ke aiki a hukumar ‘yan sanda ta Najeriya (Nigerian Police Drive), da Mustapha Hudu Ahmad jami’i a rundunar sojojin Najeriya (Nigerian Military Drive), da kuma Shamsu Hudu Ahmad mashahurin dan kwallon kafa.

Marubuci Nazir Adam Salih, wanda babban aboki ne ga Habibu Hudu Darazo, a sakon ta’aziyya da ya wallafa a shafinsa na fb ya ambaci marigayi Alhaji Hudu Ahmad da cewa: “Mutum mai kirki da barkwanci, wanda bai dauki duniya a bakin komai ba. A tsawon shekaru kusan Talatin da muka yi tare da Habibu muna rubutu, mahaifinsa ya taimaka mana matuka wajen iya kimsa barkwanci a cikin labaran nishadi. Idan ka zauna da shi, ba za ka so ku rabu da shi ba. Muna barar addu’a Allah Ya ji kan sa da rahma Ameen.”

- Advertisement -