Magoya Bayan Falasdinawa Na Shirin Gudanar Da Zanga-zanga A Faransa

- Advertisement -

Magoya Bayan Falasdinawa Na Shirin Gudanar Da Zanga-zanga A Faransa

Masu fafutuka solar kira zanga-zangar a gundumar Barbes da ke Arewacin Paris don nuna rashin amincewa da yadda Isra’ila ta yi amfani da karfi a Zirin Gaza don mayar da martani ga rokokin da kungiyar Hamas ta harba kan Yahudawan.

Ministan cikin gida Gerald Darmanin ya wallafa ta shafinsa na Twitter cewa “Ya bukaci shugaban ‘yan sanda na Paris da ya hana zanga-zangar na ranar Asabar mai nasaba da rikice-rikicen da ke wakana a Gabas ta Tsakiya.”

Ministan cikin gidan Faransa Gerald Darmanin ya yi kira ga shugaban ‘yan sanda da ya haramta zanga-zanga goyon bayan Falasdinawa

Ya kara da cewa “An ga mummunar hargitsi ga zaman lafiyar jama’a a shekarar 2014,” don haka, yana kira ga shugabannin ‘yan sanda da ke wasu wurare a Faransa su ma su kula da zanga-zangar.

A watan Yulin 2014 an gudanar da mummunar zanga-zanga da Faransa don yin Allah wadai da harin Isra’ila kan Zirin Gaza, bayan da suka yi fatali da haramcin da ‘yan sanda suka yi, lamarin da ya zama tarzoma tare da jikkata mutane da dama.

- Advertisement -