Maganin Gargajiya Kwantar Da Maleriya Ya Ke Ba Maganin Ta Ba- Bincike

0
86

Maganin Gargajiya Kwantar Da Maleriya Ya Ke Ba Maganin Ta Ba- Bincike

Daga Idris Aliyu Daudawa,

Dakta Oluwagbemiga Aina, wani babban jami’i ne a cibiyar bincike kan al’amuran da suka shafi magunguna na kasa (NIMR), ya bayyana cewa al’amarin da ya shafi shan maganin gargajiya don maganin zazzabin maleriya, yana kwantar da kwayar cutar ce kawai na zuwa wani lokaci ne, amma ba yana maganin ita cutar bane gaba daya.

 

Aina wanda shugaba ne a sashen al’amarin da ya shafi bincike kan kimiyyar tsirrai da kuma abinci, wadda ke karkashin cibiyar ta NIMR.

Ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da manema labarai Ranar Cutar Maleriya ta Duniya wadda ake yi, a ranar 25 ga Afrilu na kowacce shekara.

Manema labarai solar ba da rahoton cewa ana bikin Ranar Maleriya Ta Duniya ne a ranar 25 ga Afrilun kowacce shekara, don wayar da kan mutane da kuma nuna kokarin da kasashen duniya ke yi na ganin an gano bakin zaren, kan zazzabin cizon sauro ko kuma  maleriya da kuma murnar nasarorin da aka samu.

Ya kara da bayyana cewa“Abin sha’awa, ni ne Shugaban cibiyar bincike ta fannin nazarin magungunan gargajiya, a karkashin cibiyar NIMR.

“Mutane da yawa suna zuwa da ikirarin magunguna inda suke cewa solar samo maganin maleriya, amma a zahiri har yanzu ba mu ga wani maganin da yake da tasiri kan cutar ba, kamar magungunan na zamani.

“Har yanzu ana ci gaba da yin binciken, sai dai kuma muna neman wani mai bincike kan magungunan gargajiyar da za’a e ya samu nasara, har kuma an gano kayayyakin na gargajiya da za su yi wani tasiri.

 

“Abin da maganin gargajiya ya ke yi shi ne maganar gaskiya ita ce yana dan dakushe wani ci gaban da cutar ke yi ba ya kashe su kwayoyin cutar ba, sai bayan wani lokaci kwayar cutar za ta sake tashi tangaran,” kamar yadda ya bayyana.

 

Dangane da ko cutar Korona na iya shafar kokarin da ake yi kan cutar maleriya a Nijeriya, kwararren ya ce ita kwayar cutar wadda ke saurin yaduwa ba wani abin a zo a gani da za ta iya yi, kan cutar ta zazzabin cizon sauro ba.

 

Ya kuma kara jadadada cewa “Ba ya tsammanin ita cutar ta Korona za ta iya kawo wani cikas a kokarin da ake yi, kan cutar ta maleriya, musamman ma da ya yi la’akari da binciken da suka yi a cibiyar shekarar da ta gabata.

 

“Mun gano cewa daga cikin wadanda aka tabbatar da solar kamu da cutar Korona, kashi daya ne kawai daga cikinsu su ke dauke da cutar zazzabin na maleriya,” a yadda ya bayyana.

Dangane kuma da shi maganin ko allurar rigakafin ta cutar zazzabin cizon sauro, babban jami’in ya ce ana bukatar fiye da kashi 50 na maganin allurar a duniya baki daya, kafin ya wadaci kowa har ya yi amfani kamar yadda kowa zai amfana.

 

Bugu da kari ya yi kira ga ‘yan Nijeriya da su tsaftace muhallinsu, su kuma mata masu juna biyu da kananan yara ya dace su rika bin dokokin da aka san za su samar da wata waraka dauwamammiya da za ta a kalla rage kamuwa da shi zazzabin.

Shi ma Dakta Taiwo Adekunle, Shugaban sashen hatsari da kulawar gaggawa, na babbar asibitin Alimosho, ya bayar da shawara ga ‘yan Nijeriya da cewa su guji yin amfani da maganin da su kan su ne kawai, su ke tsammanin zai taimaka masu su samu sauki daga zazzabin na maleriya da yake damun su.

Kamar yadda ya yi karin bayani mai amfani ya ce “A tsarin asibiti, ba mu bayar da maganin zazzabin maleriya, ba tare da yin gwaji ba, domin kuwa akwai wasu cututttuka da suke da alamu irin na cutar maleriya.

”Lokacin da mutane suka fara suka fara yin tunanin cewar idan solar sha shi wancan maganin zai yi masu maganin zazzabin na maleriya ba tare da an ce musu su saya ba, ko lokacin da ya dace a yi amfani da shi, wannan maganin ba zai yi aiki ba kamar yadda mutum ya ke so, daga nan kuma za a fara samun ana shan magani amma baya yin aiki domin bai warkar da cutar ba, har ma abin ya kasance kamar wani wasan yara.

” Duk da yake dai ba za mu iya yin watsi da al’amarin maganin gargajiya ba wajen warkar da wasu cututtuka ba, dommin abin bai tsaya bane kan shi zazzabin cizon sauro, amma har yanzu da akwai jan aiki gabanmu”.

Daga karshe hanya mafita ita ce, akwai bukatar a rika tsaftace muhalli, domin hakan zai hana shi sauro yaduwa, sai kuma amfani da gidan sauro lokacin kwanciya, ga kuma amfani da maganin da ake fesa wa saboda kashe sauron, yin hakan ma zai taimaka musamman ga mata masu Juna biyu da kuma kananan yara.

 

What's On Your Mind?