Maganar Gaskiya ! Shin Da Gaske Sheikh Abubakar Giro Argungu Ya Rasuwa?

0
42

A yau ne ko yanzu nan wasu kafafenen sada zumunta ke yawo da wata karya da cewa Allah yayiwa Sheikh Abubakar giro Argungu Rasuwa..

Maganar Gaskiya ! Shin Da Gaske Sheikh Abubakar Giro Argungu Ya Rasuwa?

Cigaban Yadda Wata Mata Tanayiwa Yar Aikinta Tsarki Da Ruwan Barkono Har Ta Rasa Ranta

Ga kada daga cikin shafukan da sunka watsa wannan labari da babu tushe.

Wanda alhamdulillahi wannan karya ce kamar yadda yana nan da ransa bai mutu ba shi lokacin mutuwar kowa yana wajen Allah saboda haka a daina yada karya.

Majiyarmu Hausaloaded ta samu sahihin labarin daga shafin jibwis na kasa idan sunka wallafa a shafinsu.

“Sheikh Abubakar Giro Argungu yana nan Bai Mutu Ba

Wani makiyin Allah ya bada sanarwan cewa Sheikh Abubakar Giro Argungu ya rasu, Wannan magana ta daga hankalin al’umma a fadin duniya, sannan mun kai karar wanda ya fara ruwaito wannan labari wajen Allah.

Sheikh Abubakar Giro Argungu yana Kasar Misrah neman magani, kuma ba’a Asibiti yake kwance ba, a gida yake zaune domin rashin lafiyar bai kai a kwantar dashi a Asibiti ba, ko yanzu munyi magana da shi ta wayar tarho, kuma har solar fara shirya-shiryen dawowa gida Naijeriya.

Dan haka ayi watsi da maganar mutuwar da ake ta yadawa.

Allah ya karawa Sheikh Giro lafiya, ya dawo mana da shi gida lafiya.

Ibrahim Baba Suleiman
DG Jibwis Media & Publicity
[email protected]
17-Jumada Akheer-1442
30-January-2021″

What's On Your Mind?