Mafi Yawan Kamfanonin Ma’adanai Ba Sa Bin Ka’idar Aiki A Nijeriya – Adamu Nasko

0
88

Mafi Yawan Kamfanonin Ma’adanai Ba Sa Bin Ka’idar Aiki A Nijeriya – Adamu Nasko

An yi kira ga gwamnatin tarayya da ta tabbatar ta tankwasa keyar kamfanonin da ta ke baiwa lasisin amincewa da hakar ma’adinai a Nijeriya domin mafi yawan kamfanonin ba sa cika ka’idar da aka tsara sau da kafa.

Kwamred Musa Adamu Nasko, shugaban kungiyar leburori masu aikin hakar ma’adinai reshen jihar Neja ne ya yi kiran lokacin da yake zantawa da manema labarai a Minna.

Nasko ya cigaba da cewar zargin da ake yiwa masu hakar ma’adinai akan hannu a cikin ta’addanci da ke faruwa a arewacin kasar nan ba gaskiya ba ne, domin duk wani dan ma’adani da wahala ka equivalent shi batagari, wanda zai zage ya shiga rami sama da gaba goma dan nema halalinsa a ce zai dauki bindiga ya tare hanya ko kuma ya kora mutanen gari wannan ba adalci ba ne.

Ba su iya rike makamai ba abinda suka sani shi ne rike shebur, diga da gwangiri su hako dukiyar da Allah ya boye a cikin kasa dan su rufawa kan su asiri.

Ayyukan More Rayuwar Sin Sun Taimakawa Tattalin Arzikin Duniya

Duk wanda ka ji yana kiran leburan ma’adinai da cewar yana aiki ba bisa ka’ida ba a jihar nan to bai san ka’idar aikin ba ne, saboda ita kan ta gwamnatin tarayya ta daina anfani da wannan kalmar, domin a halin yanzu an fitar da wani sabon tsarin da gwamnatin za ta anfane su, su ma su anfana da gwamnatin. Yanzu an umurce mu da kowani mutum goma suna iya kafa kungiya da cikakkun bayanan su ta yadda gwamnatin za ta ita ba su gudunmawa, yanzu haka a jihar Neja muna da kungiyoyi sama da dari biyar da ke da rajista karkashin kungiyar nan kuma muna ba su shawarwarin hanyar da za a inganta sana’ar ba mu taba yin aiki ba tare da amincewar hukumar da ke alhakin kula da hako ma’adinai ba dan muna daga cikin kungiyar kwadago ta kasa.

Babban matsalar da ake samu shi ne akwai tsarin da gwamnatin tarayya ya kamata ta daidaita, wato gwamnatin jiha da kananan hukumomi su shigo cikin harkar, amma a tsarin da ake tafiya yanzu gwamnatocin jahohi da kananan hukumomi ba sa cikin tsarin ko kadan, gwamnatin tarayya ce kadai ke kan tsarin.

Gwamnatin tarayya ce ke baiwa mutum damar hakar ma’adinai, zai shiga jiha ya fada karamar hukuma bai san kowa ba a kauyen da zai je ba yayi ikirarin cewar wurin nan na shi ne. Ka ga zai wuya a samu zaman lafiya, akwai CDA da ya kamata duk wani mai takarda ya cika, amma kamfanonin da ake turowa daga Abuja su zo ba sa cika wadannan ka’idodin, saboda haka duk wanda zai ce leburan ma’adinai yana aiki ba bisa ka’iba to ya nemi ya kore su dan yayi babakere akai, photo voltaic ki yarda shi yasa ake yi masu lakabi da wannan kalmar.

Mun fadawa mambobin mu cewar duk wanda Allah yasa ya gano inda ke da ma’adani to ya sanar da mu zamu hukumar da abin ya shafa dan yin bincike kafin fara gina wajen. Shi yasa mu ke kokarin daidaita al’umma da masu wajen da kuma ma’aikatan ma’adanan.

A ka’idar aikin idan a gona ne, za a zauna da mai gonar in har bai yarda ayi ba to ba damar a yi din. Dokar kasar ta bada wannan damar, domin bai kamata kamfani ko kungiya ta fara hakar waje ba sai an samu amincewar mazauna wajen a rubuce kafin ta baiwa kamfani dama. Amma halin mu na ‘yan Nijeriya yayi nisa domin mutum zai zauna a daki ya cike takardar nan ba tare da sanin masu hakki ba yazo yana ikirarin waje a karshe sai a rika batawa jama’a suna. Su kuma hukumomin da ke da hakkin ba da takardar amincewa ba tare bincike ba sai su ba su takarda kai tsaye wanda a karshe sai ya zama fitina.

Ina kira da babban murya ga gwamnatin tarayya da ta tabbatar ta janyo gwamnatin jahohi da na kananan hukumomi a cikin lamarin dan samun daidaito. Haka su kan su ‘yayan kungiyar mu a duk inda suke su tabbatar photo voltaic yi rajista da kungiya kuma su zama masu bin doka. Muna kara jaddada masu cewar idan photo voltaic wajen aiki kuma ba su da karfin fuskantar wajen su sanar da mu za mu bi hanyar da ta dace dan samu daidaito da masu wajen da masu gari dan yin aikin nan cikin kwanciyar hankali.

What's On Your Mind?