Mace Ta Gari Jagora Ga Samuwar  Al’ummah  Ta Gari

0
66

Mace Ta Gari Jagora Ga Samuwar  Al’ummah  Ta Gari

Usman Umar Assakafiy,

Da sunan Allah…

Mace mutum ce da ubangiji ya samar mata da rayuwa irin wacce ta dace da tsarin yanayin halittarta, wacce ta kasance tasha bambam da rayuwar namiji, ƙkarfinta ba a surar halittarta yake ba kamar yadda namiji yake, ita ƙkarfinta a zuciya yake, saboda tayi tasiri a zuciyar  duk wanda jikinsa yake da karfi, da gaske ne maza suna da sirrin karya zuciyar mace da tattausan lafazinsu amma kuma ƙkarfafa mata zuciya ƙkokarin gyara mata kuskuren raunin da jikinta ya tasirantarwa ƙwawalwa, da haka ne zamu gina mace ta gari.

Wannan ɗdan rubutun nawa zai yi nazari ne a kan, yadda mace take a al’ummarmu da kuma yadda ya kamata ta zamo tagari dan a gina al’umma da ita, zamowar mace ta gari shine zai yaye mana halin da al’ummarmu take ciki, saboda tsayuwarta kawai nasara ce, jajircewarta galaba ce, wanda rauninta kuma rushewa ce, nuna halin ko in kula kuwa da take yi alamace ta nuna cewa bazamu kai ga nasara ba.

Muna da kyakykyawan rawar da zamu taka dan gina wannan al’ummar da ta durfafi rushewa ta hanyar sana’anta mace ta gari wacce zata zamo uwar al’umma a gobe, muna raye ko bama raye ba shi ne mai muhimmaci ba a wannan al’ummar idan har mun zurfafa tunani zamu iya jaran goben wannan al’ummar kuma zamu fara tane daga yau idan har mun yarda cewa al’ummarmu muke son rayawa.

MA’ANAR MACE TA GARI

Idan ina maganar mace ta gari a wannan rubutun nawa bana nufin macen da ta kama kanta ta yi aure ta mutu a ɗdaki ta na mai yi wa mijinta biyayya, duk da kuwa hakan ma abune ne mai kyau, amma macen da ta zamo ta gari abun alfaharin al’ummarta ko jama’arta, wacce ta sadaukar saboda ayi alfahari da ita a goben al’ummarta saboda sadaukarwa da tayi ita nake nufi.

Mace ta gari ita ce matar da ta yarda ita mutum ce wacce tayi imani da samar da sauyi ga Al’ummarta a yayin da jama’arta ta suka shirya shiga kwazazzabon halaka ba tare da solar ankara ba, wacce za ta sauke nauyin da yake kanta ba tare da ta yi la’akari da dole sai an fahimce ta ba.

Irin wannan matar tana da wuyan samu,amma idan muka similar ta zamu kai ga tudun- mun tsira kamar yadda Nana Bilkisu takai mutanen ta ga shiriya saboda zurfin tunaninta kamar yadda al’kur’ani ya bamu labari.

Ke ma za ki iya ki zamo kamar Sarauniya lakshimi jhansi (1885) na ƙkasar Indiya  ko kuma ki zamo irin dakarunta dan nemawa al’ummarki ƴ’yanci, kuma zaki yi nasara muddin ki ka jajirce kamar yadda ta jajirce.

Kowace mace uwa ce kuma ko wace uwa za ta iya zamowa mace ta gari jagorar al’umma.

YADDA AKE GANE MACE TA GARI

A irin al’ummarmu ko nace a irin yankin da muke rayuwa tasirin gargajiyanci da kuma ƙkarancin ilimin sanin halayyar ɗdan adam da na zamantakewa ta jawo idan aka ƙira jumlar mace ta gari abun da zai fara fadowa a ƙwawalwar mutum shi ne wata mata mai halaye kamar haka:

–  Ladabi da biyayya ga miji

Idan kuma maras aure ce:

Macen da bata kula maza.

Mace mai kamantuwa da siffan addini.

Mace mai kyawawan halaye, da faram-faram ga jama’a.

Amma duk da haka akwai wasu ma’aunai da za’a iya gane mace ta gari da dasu wadannan ma’aunan sune waɗannan abubuwa masu zuwa:

(1) Dogaro da kai:

Muddin mace ta zamo mai ƙkokarin dogaro da kan ta dan biyawa kanta bukatun yau da kullum to wannan matar ta hau matakin da za’ace mata mace ta gari.

(2) Damuwa da damuwar Al’umma:

Wannan ya yi ƙkarancin a cikin al’ummarmu kuma shi ne hakikanin mutumtaka, duk lokacin da ta ga jama’arta suna da rashin shuwagabanni na gari zata shirya dan nemo jagora na gari da hasashenta.

(three) Zurfin tunani:

An yaƙmatan mu na wannan al’ummar da sunan addini ta hanyar riya musu cewa su basu da tunani ko kuma suna da ƙkarancin ƙwawalwa ta tunani da hangen nesa, ta yadda duk hasashenta a gurin wasu rudaddu ne,amma kuma idan muka duba al’ummun da suka gabata da suka rayuwa ƙarshin jagorancin mace, sai mu ga ce wa sunayin nasara, mace mai zurfafa tunani akan al’amuran yau da kullum mace ta gari ce uwar al’umma.

(four) Bayar da gudumowa:

Mace ce ta gari take iya bayar da gudumowa dan ci gaban al’ummarta ta fuskacin sanya dukiya ko kuma bayar da sharwarwari ta hanyar bijiro da abubuwan da take ganin matsaloli ne da kuma hanyar da za’a magance ta.

(5) Mace Mai Tunanin Goben Al’umma:

Duk lokacin da mace bata Tunanin goben al’ummarta to zai yi wuya ta tsaya kyam dan yin nazari akan yadda za ta tsara tarbiyyar iyalinta saboda ‘ya’yanta su zamanto masu gyara kuskuren da magabatansu suka aikata.

Mace Ta Gari Ita Ce Jagora Ta Gari

Mace ta gari ce kawai take iya zamowa jagora ta gari ta hanyar haifo mutum da bashi tarbiyyar da zai zamowa al’umma fitila a lokacin da al’ummarsa ta shiga duhu.

Mace ce Allah ya bawa baiwar tasiri ga wanda ta haifa ko ta rena ta yadda zai kasance ne a farkon al’amarinsa kamar sabuwar randa wacce ba komai daya taɓa shiga cikinta ta yadda idan taso ta nemo tsaftaceccen ruwa ta adana a ciki ko kuma ta ɗauko gurɓatacce ta sanya a ciki, ba dole kowani mutum ya lura da abun da yake cikin randar ba kafun yayi amfani da ruwan ba, mafiya yawan jama’a sai sunyi amfani dashi za su iya fahimtar irin abun da suka sha ta fuskacin kyau ko muni.

Dan haka ƴ’yar uwata ki dage ki tanadi abu mai tsafta dan sanyawa a ƙwalwalwar yaro ko yarinya saboda gobenmu tayi kyau.

Zan sake mai maitawa a karo na ƙkarshe: “Idan muka samu mace ta gari a yau, Goben Al’ummarmu zatayi kyau”.

 

What's On Your Mind?