Mace-macen da aka yi a Kannywood cikin 2020

0
26

SHEKARAR 2020 shekara ce wadda a cikin ta mutuwa ta yi ragargaza a ko’ina a faɗin duniya, musamman saboda cutar korona (COVID-19). A Nijeriya, ba a taɓa samun yawan mace-macen manyan mutane ba kamar a bana.

A masana’antar finafinai ta Kannywood ma, ‘yan fim guda biyar ne su ka mutu, sannan ga iyayen wasu da su ma su ka kwanta dama, duk sakamakon rashin lafiya daban-daban. Ga sanannun mace-macen da su ka shafi ‘yan fim kai-tsaye mujallar Fim ta lissafo maku su daki-daki:

*Alhamis, 6 ga Fabrairu:Allah ya ɗauki ran Hajiya Maryam Yusuf, mahaifiyar fitacciyar jaruma Halima Yusuf Atete, a wani asibiti da ke Abuja bayan doguwar jinya da ta yi fama da ita.

*Litinin, 2 ga Maris:Mahaifin fitaccen mawaƙi kuma jarumi Umar M. Shareef, Abdul M. Shareef da Mustapha M. Shareef ya rasu. Alhaji Muhammad Shareef ya rasu ne a Asibitin Sultan da ke Rigasa, Kaduna. Shekarun sa 75 a duniya.

*Asabar, 14 ga Maris:Allah ya ɗauki ran fitacciyar jaruma Ladi Muhammad, wadda aka fi sani da Ladi-Mutu-Ka Raba.

*Talata, 21 ga Afrilu:Mahaifin fitacciyar jaruma Sadiya Muhammad (Gyale), ya rasu. Alhaji Muhammad ya rasu a gidan sa da ke unguwar Sagagi, Ƙofar Na’isa, a cikin garin Kano.

*Litinin, 27 ga Afrilu:Allah ya yi wa mahaifin masanin harkokin Kannywood kuma Mataimakin Shugaba (VC) na Buɗaɗɗiyar Jami’ar Nijeriya (Nationwide Open College of Nigeria, NOUN) rasuwa. Dakta Muhammadu Uba Adamu (Kantoma) ya rasu ne a Asibitin Nassawa, a Kano. Shekarun sa 85.

Mace-macen da aka yi a Kannywood cikin 2020

*Alhamis, 30 ga Afrilu:Mahaifin fitacciyar jaruma Hajara Isah Jalingo ya rasu a ‘Federal Medical Centre’ da ke Jalingo, Jihar Taraba. Shekarun Malam Isah Tidwa Jalingo 67 a duniya.

*Alhamis, 30 ga Afrilu:Allah ya yi wa fitaccen jarumi Ubale Ibrahim (Wanke-Wanke) rasuwa, a gidan sa da ke unguwar Rangaza da ke Ƙaramar Hukumar Ungogo a cikin garin Kano. Shekarun sa 50.

sama daga hagu: mahaifin Hajara Isah Jalingo da na su Umar M. Shareef da na Ali Nuhu. A ƙasa daga hagu: mahaifin Safiya Musa da mahaifiyar Halima Atete da ta Nasiru Auwal (Horo)

*Laraba, 13 ga Mayu:Allah ya ɗauki ran shahararren ɗan wasan Hausa Alhaji Daudu Galadanchi. Ɗan shekara 86 a duniya, ya rasu ne a gidan sa da ke unguwar Galadanchi a cikin Birnin Kano. Ya bar mace ɗaya da ɗan sa ɗaya.

Yanzu Yanzu: Allah ya yi wa ƙanin Sarkin Daura rasuwa

*Lahadi, 24 ga Mayu:Allah ya yi wa mahaifin fitaccen jarumi Nura Hussaini rasuwa.

*Litinin, 8 ga Mayu:Mahaifin fitaccen jarumi Ali Nuhu, ya rasu a Gombe sakamakon rashin lafiya da ya yi. Shekarun Mista Nuhu Poloma 79 a duniya.

*Asabar, 12 ga Yuli:Allah ya yi wa jaruma Asma’u Adam rasuwa. Ta rasu a Asibitin Nassarawa sakamakon rashin lafiya.

*Asabar, 22 ga Agusta:Mahaifiyar jarumin barkwanci Nasiru Auwal (Horo Ɗan Mama) ta rasu a garin Gumel, Jihar Jigawa. Shekarun Hajiya Ladi Auwal 65 a duniya.

*Juma’a, 28 ga Agusta:Allah ya yi wa fitacciyar jaruma Fadila Muhammad (Ummi Lollipop), rasuwa. A cikin motar mahaifin ta ta rasu a lokacin da ake kan hanyar kai ta asibiti. Ta rasu ta na da shekara ta 27 a duniya.

*Allah ya ɗauki ran mahaifin tsohuwar jaruma Safiya Musa rasuwa a Asibitin Sojoji da ke cikin 1 Division a Kawo, Kaduna. Shekarun Alhaji Musa Makka kimanin 98.fimmagazine ce na ruwaito.

Allah ya jiƙan Musulmi, amin.

What's On Your Mind?