Mabiyan Addini A Jihar Xinjiang Na Gamsuwa Da Yanayin Rayuwarsu A Cikin Watan Ramadhan

0
74

Mabiyan Addini A Jihar Xinjiang Na Gamsuwa Da Yanayin Rayuwarsu A Cikin Watan Ramadhan

Daga CRI Hausa

Wani mazaunin yankin Kizilsu Kirghiz na jihar Xinjiang, Pazla Sidikaji, ya bayyana gamsuwa sport da yanayin rayuwarsu da yadda suke gudanar da harkokin da suka shafi addini a cikin watan azumin Ramadhan.

Pazla Sidikaji, mataimakin mai karantar da Alkur’ani a masallacin kauyen Iksak dake birnin Atush na yankin Kizilsu Kirghiz ya bayyana hakan ne jiya a birnin Urumqi, yayin wani taron tattaunawa ta musammam ta kafar bidiyo da ofishin jakadancin kasar Sin da ke kasar New Zealand da gwamnatin jihar Xinjiang suka gudanar.

A cewarsa, an shiga watan Azumi a ranar 13 ga watan Afrilu. Kuma yin azumi ko rashin yi, ya dogara ne da ra’ayin mutum, yana mai cewa babu wanda ke tsoma baki cikin batun. Ya ce musulmai da dama a kauyensu na yin azumi. Kuma a yayin watan Azumi, gwamnati ta kan shirya likitocin da suke bada jinya a masallatai, kana a kan samar da shayi da burodi da ‘ya’yan itatuwa da sauran abinci a lokacin shan ruwa, yana mai bayyana gamsuwa sosai da yanayin rayuwarsu. (Zainab)

What's On Your Mind?